← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 95

Sashe 89

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Habeeb da ke kishingid'e a parlournshi, yana dafe da waya a kunnenshi jin Haleesa ta yi shiru ba ta yi magana ba yasa ya ajiye zafin kanshi a gefe, yace _Leesa na yi fushi a maimakon ki kira ni ki bani hak'uri sai ki ka nuna mini halin ko in kula koh"?_
"Huh.... Yaya Habeeb kenan to ni wane laifi na yi maka da zan baka hak'uri"?
Dai-dai lokacin da Hannah tak'araso gate d'in gidan ta yi horn saida suka d'auki tsawon _3 minutes_ kafin gate ya bud'e su shiga yayinda Haleesa ke cigaba da waya da Habeeb.
"Parking Hannah ta yi Haleesa ta bud'e k'ofa tacire wayar daga kunnenta ta yi k'asa da murya yadda Habeeb bai zai ji abunda takeso fad'a ba what's time za ki dawo dauka na"?
Batare da Hannah ta yi magana ba tad'aga mata yatsunta uku.
_3 o'clock"?_ Haleesa tafad'a.
Hannah ta gyad'a mata kai Haleesa tajuya tanufi cikin gida yayinda Hannah ta ja mota.
"Direct part d'in Habeeb ta wuce tana mai cigaba da waya da shi a hankali ta turo k'ofa cikin Sa'a k'ofar ya bud'e ta hango Habeeb kishigid'e da waya a kunnenshi ta katse kiran miyarda phone d'inta cikin purse cikin sand'a tashiga parlourn ta bayan kujeri ta bi ta la6a6o ta rufewa Habeeb fuska.
"A tsorace Habeeb yashiga kacaniya cire hannayenta daga fuskarshi finciko ta ya yi da k'arfi tafad'o bisa kujera razananen ihu tasaki had'e da kai mishi duka da purse d'in hannunta haba! Yaya Habeeb karya ni za ka yi ne"? Irin wannan fincikowa da ka yi min Allah saura kiris na yi targad'e.
"Fuskarshi d'auke da shu'umin murmushi yajuyo yana facing nata hannayenta yarik'o yacire purse daga hannunta ya jefa bisa kujera da ke kusa da shi ya ja iska yana mata kallon k'asan ido mekika zo yi wurina bayan ni kin haramta min zuwa wurinki"?
"Au! Haka ma za ka fad'a ae ni a tunani ba wannan tambaya yakamata ka yi mun ba tak'arasa magana had'e da fizge hannayenta tasoma k'ok'arin tashi da k'arfi ya mayarda ita zaune ya aza kanshi bisa cinyoyinta yace na yi matuk'ar mamakin ganinki Leesa domin wannan kiran da nayi miki na bankwana ne har na k'udiri anniyar gobe da zaran andaura auren Hannah zan koma Lagos daga can na haura Canada ba za ki k'ara ganina ba har sai kin nemi ni da kanki.
"Haleesa ta tabe baki da kuwa kayiwa kanka domin ba neman naka zan yi ba.
"Nasan za ki iya Leesa saboda ba damuwa ki ka yi da ni ba shiyasa a koda yaushe nake godewa Allah da yakare ni daga matan banza yak'arasa magana kamar zai yi kuka.
''Tausayinshi yakama Haleesa ita kanta tasan Habeeb yana cikin maza masu k'arancin sha'awa mata basa gabanshi shi dai barshi da neman k'udi a hankali take Shafa sumar kanshi muryarta asanyaye tace ka yi hak'uri my handsome Don nasan kana jin zafina amma yakamata ka yi min adalci ka tuna irin d'an banzan wulaqancin da dinga yi min har fa ce......da sauri yatoshe mata baki karki dawo da hannun agogo baya Leesa abunda yawuce bai kamata ki tadinga dawowa da shi ba kisani a yanzu inasonki tamkar numfashina KE D'AYA CE a zuciyata daga kanki na rufe ba wata.
"Murmushi ta yi cike da jin dad'in kalamanshi mai hira mai dad'i suka shiga yi daga bisani salon hirar ya canza cak d'auke ta yanufi bedroom d'inshi da ita tabbas Haleesa ta yarda ita d'aya ce a zuciyar Habeeb Lamido domin yanda yadinga zuba mata, zazzafan kalamai abun ba kama hannun yaro bayan komai ya wakana Haleesa na tsaye a gaban mirror tana busar da gashinta da hand dryer Habeeb yafito daga bathroom yak'araso daf ita ya kar6i hand dryer d'in yacigaba da busar mata da gashin Leesa kin ga yanda ki ka dawo 'yar lukuta musanman nan wurin yak'ara cikowa yana magana had'e da Shafa k'irjinta da hannunshi d'aya yana wani lumshe ido.
"Ta cikin mirror ta zabga mishi harara ae kai abun a cikin jininka yake duk mace da ta aurenka sai ta zama katuwa sai dai bana fatar na kai girman wannan matar tak'arasa magana tana yatsina.
"Dariya Habeeb ya yi had'e da kashe hand dryer ya ajiye ta a gefen mirror yajuyo da Haleesa suna facing junansu ashe bani kadai nake kishi da matace ba ke ma kina yi.
"Ture shi ta yi tanufi wajen wardrobe ta bud'e taciro black colour Long sleeve d'inshi ta kwashe inner wears d'inta tanufi bathroom tasanya kayan tafito Habeeb yana tsaye daga shi sai white vest da boxer ya yi crossing hands nashi a k'irji kallon mai cike da so da k'auna yake mata ni kuwa Leesa in tambaye ki mana"?
"Gira ta d'aga mishi had'e Yeap!
Yasauke hannanye shi yarik'o hannunta suka nufi k'ofar fita daf kunnenta yarad'a mata yaushe za ki fara saka kaya a gabana"?
"Ignoring nashi ta yi kamar bata ji abunda yafad'a ba suka yadda zango a parlour Habeeb ya kwanta akan 3 seater yajanyo ta jikinshi a wannan karo idan na tambaye ki kada ki yi ignoring nawa.
Turo baki tayi indan kuma tambayar naka ba mai buk'atar amsa bane to kasani ba lalle bane kasame amsa ba.
Ya ja iska had'e da dage gira ko yana buk'ata ko ba ya buk'ata dole ki nemo amsa Yaushe za ki dawo gareni"?
"Huh....dama wannan ne tambayar naka"?
Amsa yakamata ki ba ni firstly kafin ki yi naki tambaya.
"Haleesa ta yi murmushi tace idan an k'are bikin Hannah ka je ka ga mom na amince zan dawo gareka........

_am sick really need ur prayer's😪_

Jeeddah Aliyu🌹

[9:10PM, 23/12/2016] Hafsat Yau Abdullahi: [22/12 6:33 pm] aliyujeeddah: 💝```NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa shehu Aliyu🌹

*®NWA*

*°°°°In Dedication°°°*
*Shehu Aliyu Family's*

*98*

_°°°°Hurray up today it's your birthday Autar Hajiya in my heart I make wishes for you to have peace & successful life_ °°°Happy birthday once again my Auta°°°°

~~Habeeb yasaki ihun farin cikin had'e da k'ara k'amk'ameta kamar zai shigar da ita k'irjinshi Sai zuba mata ruwan peck yake yi akan fuskarta zuwa, wuyanta muah...muah..I love you Leesa.... I really so much love you Leesa....wannan rana ta kasance d'aya daga cikin rananku da ba zan ta6a mantawa da su a rayuwana, Haleesa ta yi murmushi had'e da cewa d'an sausauta wannan matsar da ka yi min kada garin murna ni kuma kafasa mun k'irji.
"Karan hancinta ya ja ya sausauta rungumar da ya yi mata yashiga shafa cikinta yana lumsashe idanu Leesa...yakira sunanta
"Uhm.....tafad'a
Yaushe za ki bani baby"?
''Tabe baki ta yi ka nemo Wanda za yi min ciki ne"?
Mitsineta ya yi tasaki ihu washh....tafad'a had'e da Shafa fatar cikinta kai fa yaya Habeeb mugu ne sai ka yi ta yi wa mutum mugunta.
''Dole yasa nake miki mugunta Leesa kunnen k'ashi ne da ke nace da ke banaso abunda yawuce kina dawo min da shi sai naga kamar ba kiyafemin ba.
"Amma kuma abunda ka fad'a ne nake maimaitawa tak'arasa magana tana murgud'a baki.
"Shine nace da ke banaso don haka kidaina in baso ki ke mu yi fad'a ba.
Shikenan nadaina tacusa hancinta cikin k'irjinshi tana shinshinar k'amshin perfume d'inshi.
"D'ago kanta ya yi yana kallon cikin idonta yana dariya meye haka Leesa"?
"Allah yaya Habeeb k'amshin perfume d'inka yana mun dad'i har banaso nadaina shak'arsa.
''Habeeb ya kyalkyale da dariya yana shafar sumar kanta Lessa rigima ta yaya Habeeb Haleesa ta yi dariya wane yaya Habeeb ka ke nufi"?
"Harara ya galla mata baya ni kina da wani yaya Habeeb ne"?
"Peck ta yi mishi a kumatu kai d'aya ne baya kai ba Wani.
Dad'i ya lullu6e Habeeb cikin tsokana yace ae na yi zaton za ki kira sunan wannan mutume
"Rausayar da kai ta yi Wannan mutume ya zama past a yanzu Kaine presently, saboda haka kadaina zancenshi saidai in addu'a za ka dinga yi masa wannan ba zan hanaka ba.
"D'an bazawarin murmushi Habeeb ya yi, turo baki Haleesa ta yi ko ba za ka iya masa addu'a ba"?
Ni na isa nace ba zan masa addu'a ba yafad'a yana k'ok'arin cireta daga jikinshi Haleesa ta mik'e da kanta daga jikinshi ya yi mik'a ya dubi Haleesa yace Leesa yunwa nakeji fa
"Ta mik'e tsaye da sauri tace ka bani _15 minutes_ na dafa maka abunda za ka ci"?
Shima ya mik'e tsaye mu je na rakaki ta wuce gaba ya Mara mata baya.

_20 minutes later_
Chapter 89 · 0% Book details