← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 95

Sashe 4

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

malam Usman mai kifi da malam Audu mai kifi su biyu kacal iyayye su suka haifa mahaifin su malam balarabe bashida wata Sana'a da tawuce sayarda kifi, kuma har ya mutu sana'arsa kenan, shiyasa 'ya'yasa Usman da Audu suka gadin wannan sana'ar tasa tasayarda kifi.
Tun suna cikin ganiyar kurciya mahaifiyarsu ta rasu, mahaifinsu malam balarabe yacigaba da kula da su yasanya su makaranta allo saboda a lokacin ba kowa yake saka 'ya'yasa makarantar boko Usman yanada shekara 15 Audu kuma yana 13 Allah ya yiwa malam balarabe rasuwa, tun daga lokacin suka fara fuskantar 'kunci rayuwa babu mai taimaka musu da ko lomar tuwo domin rankatakar zuri'a su talakawa ne talauci yayi musu kanta yahana su rawar gaban hantsi.
Tun daga lokacin Usman da Audu suka duk'ufa da neman na Kansu, ta hanyar maye gurbi sana'ar mahaifinsu, a haka suke rayuwa, lokacin da suka kai muzalin aure kowane su ya yakin filin daga cikin ru6abe gidan da suka gada daga wurin mahaifinsu dama gidan d'akin d'aya ne da shi, da kyar kowane su iya gina d'aki d'aya shima na jar k'asa.
Malam Usman ya aure wata bafulatana da ke kai musu nono a kasuwa, mai suna Fatima yayin da malam Audu ya aure 'yar 'kanin mahaifinshi mai suna mairo, a haka suke rayuwa cikin rufin asiri mairo da fatima sun had'e Kansu suna zaman lafiya.
Bayan shekara d'aya da aurensu fatima ce tafara haihuwa inda ta haifo d'anta ranar suna aka rad'a masa suna salman ranar da akayi suna salman a dare ranar mairo ita ma tasami d'a namiji ranar suna na zagayowa aka sa masa Suna Habeeb.
Lokacin da salman da Habeeb suka isa shiga makaranta aka yasanya su makarantar allo da ta boko suna da shekara 3 a duniya mairo da Fatima suka K'ara haihuwa inda mairo ta haifi d'a namiji mai suna Hashim fatima kuma ta haifi 'ya mace juwairiyya.
Sai ya zamana kusan a lokacin d'aya suke haihuwa a wannan karo ma mairo ce tafara haihuwa 'ya mace aka rad'a mata suna Zainab, bayan wata d'aya da haihuwa Zainab fatima ta haifi Haleesa tun daga ranar da Haleesa ta zo duniya Habeeb yad'auki duk wata soyayarshi yad'aura akanta.
Da yadawo daga _school_ zai d'auketa yadinga yi mata wasa duk tsabar so da Habeeb yake yiwa _ball_ a dalilin reno Haleesa yawatsar da zuwa _training_ da sukeyi da yamma a lokacin da Haleesa ta isa yaye Habeeb ne yaye ta saboda a d'akinsu da ke zaure take kwana akwai wata rana da dare da ta falka tana, kuka salman da ke kwance bisa gadonsa yana bacci kukanta ne ya tayarda, shi cikin zafin rai da k'unar zuciyar yace Habeeb katashi ka mayarda yarinya nan wurin Ammi kana matsayin namiji ina kai ina yaye
Wani mugun kallo Habeeb ya watsa masa, yacigaba da jijiga Haleesa da kyar yasamu ta koma bacci ya rungume ta tsanm a k'irjinshi yana shafar suma kanta a hankali,
Wai ba magana nakeyi da kai ba Habeeb"? salman yafad'a cikin d'acin rai
Don kana magana da ni akace da kai dole sai na tanka ma"?
Ba zai yu ba duk dare kukan Haleesa yahanani baccin in kai za ka iya ni ba zan iya ba wannan ae d'aukar alhaki ne.
Mtsss...Habeeb yaja tsoki yayi kwanciyarshi yabar salman yanata faman fad'a shi kadai.
A dalilin Haleesa salman da Habeeb suka raba d'aki tun da Haleesa tayi wayo batasan kowa ba sai Habeeb, ko rashin ji takeyi da Ammi tace sai na fadawa yaya Habeeb yanzu zata fara kuka tace Ammi nadaina kuma karki fad'awa yaya Habeeb yace bayaso na.
Wata rana mal Usman da d'an uwansa mal Audu suna zaune a k'ofar gida suna fira Habeeb yafito d'auke da Haleesa, Habeeb ya rusuna ya gaida su mal Usman ya tsare shi da kallon tuhuma daga bisani yace Habeebu me kake jira ne da har yanzu ba fita shagon koyon d'iki ba"?
Habeeb ya Sosa kai alama rashin gaskiya yace wallahi baffa yau rigimar Haleesa ce ta motsa sai faman kuka takeyi shine nayi, zamana saboda ko naje _tailoring raining centre_ d'in ba abunda zan fahimta.
Baffa ya girgiza kai yace haba Habeebu miyasa za ka za6i kadinga wasa da damarka"?
Karka sake kace za ka dogara da karatun boko, a matsayinka na d'an talaka zaka k'are karatun ne kanemi aikin yi karasa domin a wannan zamani aikin gwamnati na 'ya'ya masu da shi ne ba na 'ya'ya talakawa ba, kadage kanemi Sana'a hannu kadogara da kanka.
Habeeb yace insha Allah baffa zan kiyaye baffa yace masha Allah tashi ka mayarda ita wurin Fatima
Habeeb ya sada kai k'asa cikin raunaniya murya yace Dan Allah baffa in Haleesa ta girma za ka bani ita na aura"?
Baffa ya kalle d'an uwansa mal Audu sukayi dariya, daga bisani baffa yace Habeebu ae Haleesa taka ce matuk'ar ina Raye Haleesa bata wani miji sai kai cikin tsanani farin ciki marar misaltuwa Habeeb yasoma zubawa baffa godiya Yayinda baffa da baba Audu, suke masa dariya tun daga ranar Habeeb yak'ara ririta soyayyar Haleesa tsanani so da shak'uwa ya shiga tsakaninsu.
Da Haleesa tayi laifi hukunci d'aya Habeeb yakeyi mata shine yace Haleesa banasonki ranar tadinga ihu da birgima kenan, har yaran unguwa suka ganota da sun ganta a k'ofar gida sai su fara tsokanarta ta hanyar cewa Haleesa yaya Habeeb baya sonki, kawai sai ta daka tsalle tayi fad'uwar 'yan bori tana taratsi kuka in kuma tsautsayi yagita salman yaganta ya dank'e hannu 'yar banza ya ta duka shi kuma ranar sai sun kwashe 'yan kallon da Habeeb tun lokacin da Haleesa ta mallaki hankalin kanta, ta fahimce tsantsa son da Habeeb yake mata, ita ma tana sonshi tamkar ranta ta kuma fifita shi akan kowane d'a namiji.
[24/08 7:32 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love❣_

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```9```

A kwana atashi asarar mai rai ga shi har Habeeb da salman sun kamalla karatun sakandire _{secondary school}_ a lokacin Haleesa da zainab suna aji biyu a _primary school_ jawairiyya kuma tana aji uku a sakandire, zuwa wannan lokacin sun kware da d'ikin tela, hakan yasa iyayyesu suka zauna suka yanke shawara bud'e musu shago, d'an tanadin da suka jima sunayi suka fito da shi, suka nemo haya shago, a cikin unguwar tasu aka zuba musu telolin.

Habeeb da salman na zaune a tsakiyar gida sai faman shawara suna da za su sakawa shago nasu sukeyi, duk suna da salman yakawo Habeeb yace baiyi masa ba, cikin bacin rai salman yace nagaji Habeeb na fahimice cewa so kake yi ka haddasa mini ciwon kai don haka na baka za6i, Habeeb yayi murmushi had'e da cewa dad'i na da kai salman saurin fushi girgiza kai salman yayi daga bisani, yace banaso damuwa shiysa na baka za6i kafin Habeeb yabashi amsa ya ji 'yar siriiyar muryar Haleesa tayi sallama, sun dawo daga _school_ ita da zainab yad'ago yana kallonta fuskarshi d'auke da murmushi Haleesa na kyala ido taga Habeeb tadaka tsalle had'e da jefarda _school bag_ d'inta ta kwasa da gudu ta nufi wurin Habeeb da sauri ya mik'e tsaye ya ware mata hannaye shi tafad'a jikinsa ya k'ank'ameta yace _oh my baby I miss you so much_ ya sumbace kuma tun ta ina fatar _babylove_ tayi karatu sosai"?
Turo d'an karamin bakinta tayi cikin shagwaba tace nayi karatu sosai yaya Habeeb har da _sweet_ auntymu tabani tasake shi tajuya tad'auko _school bag_ d'inta da ta jefar ta zuge _zip_ tafito da _sweet d'in splash_ ta6are leda tafito da _sweet_ ta jefa baki ta gutsirawa Habeeb yunwa ta duk ya lullube, sweet tasakawa Habeeb a baki da sauri salman ya kauda fuskarsa yana wani yatsina fuska, Habeeb yad'aga ta sama suna kyalkyale dariya, daga bisani yadireta, yaja karan hancinta yace zo mu je _babylove_ ki cire _uniform_ da kanshi yasauya mata kaya, sai faman zazzaga masa surutu takeyi shi kuma yana kwasan dariya, salman ya gallawa Habeeb harara had'e da cewa _look malam karka maida ni soko irinka tun d'azu ina jiranka sai yawo da hankali kake min_
Murmushi Habeeb yasaki yace _sorry in-law kasan duk lokacin da naga babylove mantawa nakeyi da komai_
Mtsss...salman yaja tsoki yace wannan kuma matsalarka ce ni ba abunda yahad'ani da wannan shirme naka, don haka ka ajiye shi a gefe mu yi abunda yake gaban mu.

Hannu Haleesa, Habeeb yarik'o yace _babylove fad'a min sunan da kike so asakawa shagonmu?_
Kallon amma kai shashasha ne salman yake watsawa Habeeb, yayin da Haleesa ta wangale baki tana dariya daga bisani tace ```Ni da yaya Habeeb ```
Habeeb ya tintsire da dariya Haleesa na taya shi, cikin tafarfasa zuciya salman yaja dogon tsoki, ya mik'e had'e da ficewa daga gidan domin yana tunani Habeeb ya zauce.
Salman bai tabbatar da Habeeb ya zauce ba sai a washe gari da yaci karo da k'aton _symbol_ a kafe a gefen shagon su an rubuta ```NI DA YAYA HABEEB TAILORING CENTER ``` salman ya yi tsaye had'e da tsurawa sunan ido kawai yasaki murmushi yak'ara sa shiga shagon batare da kalle Habeeb ba yanufi wurin tela sa yayinda Habeeb yayi tsuru-tsuru da ido daga bisani ya mik'e yanufi wurin salman yadafa kafad'arsa ya marairaice murya yace kayi hank'uri salman nasan suna da na sanyawa shagon nan baiyi maka dad'i ba amma Dan Allah kayi hank'ur karka yi fushi da ni.
Salman yasaki murmushi yarik'o hannu Habeeb, yace daina bani hank'uri Habeeb duk abunda kake so nima ina sonshi saidai son da kake nunawa Haleesa yayi yawa da za ka d'auki shawara na da nace karage ko da d'an k'ank'ani ne.
Habeeb ya6ata fuska daga bisani yace son Haleesa _Allah ne yad'ora min bani na d'orawa kaina ba_
Salman ya girgiza kai batare da yace komai ba domin yasan har abada Habeeb ba zai ta6a d'aukar shawara sa.
Sannu-sannu shagon su Habeeb yadinga han6aka suna samu _customers_ sosai gani yadda suke samu kud'i yasa suka yanke shawara neman _admission_ a _polytechnic_ cikin yarda Allah suka samu adadafe suka, kamalla _diploma_ sun sha gwagwarmaya neman aiki amma basu samu ba dole suka hank'ura suka cigaba da d'ikin su na tela, watakila nan Allah yanufi abincin su yake.

```DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S ```
Chapter 4 · 0% Book details