← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 95

Sashe 17

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Habeeb gudunta yakeyi tsawon sati ta d'aya da tarewa a gidanshi amma bata saka shi a idanu ta ba, gani wannan ba zai zame mata mafita, a wani dare takasa ta tsare Habeeb na shigowa cikin sand'a kamar barawo yashige da'kinshi tana la6e tana kallonshi, saida ta tabbatar da yashiga bedroom d'inshi ta Mara masa baya tana shiga yana fitowa daga wanka kallon-kallon suke yiwa junansu tsanani kunya tarufe Habeeb wai shine ya aure auntyshi salma tsawon lokacin suka dauka a tsaye daga bisani salma takawo karshen shiru ta hanyar furta zo zauna Habeeb mu yi magana Habeeb ya langwa6e kai yace aunty sal...
Dakata Habeeb! Karka k'ara kirana da suna aunty tuni na tashi daga wannan matsayin a yanzu Kaine gaba da ni.
Habeeb yak'arasa ya zauna a gefen bed ita ma ta zauna kusa da shi, tafara magana cikin rauni murya Habeeb wannan tsari da kafito da shi zaman mu ba zai yi armashi saboda ka aure ni ne don kana ji tausayina to bai kamata kana guduna.
Habeeb yayi k'asa da murya yace aunty salma kunyarki nakeji salma tarik'o hannunshi tace Habeeb ka ajiye zance kunya a gefen domin yanzu babu kunya a tsakaninmu tunda igiyar aure tashiga tsakani mu, a dare ranan Habeeb ya nunawa salma cewa shi d'in ba 'karamin yaro bane kamar yadda take kallonshi, ya sanyata farin ciki da bata ta6a mafalki samu a rayuwarta tun daga lokacin salma take ririta shi tana bashi girma a matsayin shi na mijinta tana matuk'ar son Habeeb tamkar numfashinta duk lokacin da Habeeb yake a gari bai yi tafiya ba salma na manne da shi tana nuna masa salon so, sannu a hankali son salma yasami muhalli a zuciyar Habeeb yabata babban matsayi a zuciyarshi yadda salma take ririta Habeeb da shagwa6a shi yasa tayi nassara mallake shi saboda akwai son girma Sam bayaso reni, yana matuk'ar son rayuwar Hutu gaba d'aya tsarin rayuwarshi ta turawa ce in har yana gida bayaso salma tayi nisa da shi hatta da baccin a k'irjin salma yakeyi ana cikin haka tasamu ciki Habeeb tamkar zai yi hauka don farin ciki har cikin salma yashiga wata tara bata fasa farantawa Habeeb ba ga girman ciki ga girman jiki amma a haka salma take zage dantsi ta taraiyi Habeeb, wata rana na zaune a downstairs parlour yana duba wasu file's salma tanufi wurinshi jin tak'o tafiyarta yasa Habeeb yad'ago suna had'a ido yasake mata murmushi, ita ma ta mayar masa da martani garin taka stairs k'afarta ta zame ta dinga mulmula akan stairs har ta sauko k'asa Habeeb ya watsarda file's d'in hannushi da gudu yanufi wurinta, tuni jini ya ballewa salma Habeeb ya dinga girgiza ta saidai ko motsi batayi duk iya 'ko'kari Habeeb yadauki salma ya k'asa saboda tayi mishi nauyi da gudu yanufi _main gate_ ya nemo taimako bala driver suka saka salma a mota sai hospital, yayinda salma keta faman bleeding nan take doctor's suka yanke shawara yi mata cs saboda kada baby da yake cikinta mutu Habeeb ya yi sign aka shiga _operation theatre_ da ita likitoci sukayi nasara Ciro mata baby girl mai Kama da ita sak saidai sun k'asa tsayarda bleeding d'in takeyi har salma tafarfado jini na zubar mata, cikin yanayi na jigata tace a kira mata gani yanayi da take ciki yasa likitoci suka amince Habeeb ya shiga d'akin salma na gani shi tarik'o shi da kyar take iya magana tace.......
[04/09 1:53 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```41```

Habeeb kayafe min yadda nakeji jikin nan nawa bana tunani zan tashi, da sauri Habeeb yarufe mata baki yana girgiza, yace za ki tashi salma in kika tafi wa zai kula miki da ni da babynmu"?
Allah zai kula da Ku Habeeb dama chan shi yake kula da dukani halittu sa.
Habeeb share hawaye da suka zubo masa yace "please salma stay with me don't leave us we really need you me & my baby
Habeeb inaji rad'ad'i da zafin ciwo kayi min addu'a da sauri Habeeb yadinga karanto addu'a yana tofa mata tayi murmushi k'arfin hali tace Habeeb me na Haifa"?
Baby girl mai kama da ke kinaso ki gannta salma tadaga kai bara naje na kawo miki ita kinji salma naa"?
Ya sunbace goshi had'e da lips nata yafice yayinda salma tabishi da kallo, idanuta na tsiyaya hawaye, Habeeb yana karasowa rik'e da baby ya ga an turo salma lullube da farin kyale bayan fitar shi Allah ya kar6i ran salma Habeeb yayi matuk'ar tsorata saura kiris ya jefarda baby da sauri wata nurse ta kar6i baby gawar salma yanufa yadinga girgiza ta saida likitoci{doctor's} suka rik'e Habeeb kuka yakeyi kamar k'arami yaro, daga bisani aka wuce da gawar salma gida akayi mata sutura kamar yadda addini musulunci ya tanarda, ranarda sadaka bakwai aka rad'awa baby sunan salma Habeeb yana kiranta da iman kasancewar madam Hindu bata lokacin kula da baby iman dole Habeeb yabarta hannu Hajiya khareema ita kuma ta bud'e babi tatsar Habeeb da kuma cusa masa Maryam ita ala dole so take Maryam ta maye gurbin salma, a haka rayuwa iman tacigaba da kasancewa a k'arkashin kulawa Hajiya khareema har salma tayi shekara biyar da rasuwa Habeeb bai k'ara tunani yin aure ba farko haduwar shi da Haleesa ya je gani iman yatararda 'yar aiki Hajiya khareema tafi da iman unguwarsu shine yabiyota har driven shi ya watsawa Haleesa ruwan kwatami a karo na biyu ma yaje gani iman still Hajiya khareema tace tana gidansu lami mai aikinta shine haduwar shi ta biyu da Haleesa haduwar shi ta uku da Haleesa nan ma yaje ganin iman akace tabi lami gidansu ashe tsakani unguwar su lami mai aikin Hajiya kareema da Unguwar su Haleesa ba nisa kusan unguwa d'aya ce titi ne kawai yaraba su.

```cigaban labari ```
Madam Hindu tasauke ajiyar zuciya tashafi sumar kan Habeeb, zuciyarta cike da tausayi d'a nata Ko yaushe mafalkinta zai cika nagani Habeeb yak'ara aure"?
A hankali ya bud'e kwayar idonshi yarik'o hannu madam Hindu cikin sanyayar muryar shi mai matuk'ar dad'i yace mom tunani me kike yi"?
Madam Hindu tayi murmushi tace no thing son Habeeb ya mik'e zaune yace mom banaso ko kad'an naganki ciki damuwa please karki d'auki damuwar crazy girl kisaka a ranki'
Murmushi madam Hindu tayi daga bisani tace wacece crazy girl"?
Yana yatsina fuska yanuna bedroom d'in mommy da yatsashi yace wance take ciki madam Hindu ta girgiza kai tace _stop calling her crazy infact she is your sister_
She is not yafada had'e da mik'ewa tsaya yayi mik'a yace mom zan shiga ciki nayi wanka madam Hindu tayi murmushi had'e daga masa kai yayinda Habeeb yahaura stairs d'in zai sada shi da room d'inshi madam Hindu ta bishi da kallo daga bisani ta mik'e tanufi bedroom d'inta wurin Haleesa.......

```DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S ```

Jeeddah Aliyu🌹
[05/09 9:57 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [05/09 4:07 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```43```

Zaune take ta rakka d'a uban tagumi sallamar Madam Hindu ce tadawo da ita natsuwarta, da sauri tanufi wurinta, sannu Haleesa kintashi ya jikin naki"?
Murmushi Haleesa tayi tace I'm okay mom ba abunda yake min ciwo
"Alhamdulillah hankalina ya yi matuk'ar tashi Haleesa da naganki cikin wannan hali har naji a raina lallai ya Zame mini dole na tambaye ki waye yaya Habeeb"?
Tuni idanu Haleesa sun ciko da kwala ta sada kai k'asa cike da tausayi madam Hindu tarik'o hannuta karki kiyi kuka Haleesa in har wannan tambaya nawa zai haifar miki da tashi hankali to kiyi han'kuri karki fad'a kinji"?
Haleesa ta share hawaye had'e da majina tad'ago jajaye idanuta cikin sark'ewar halshe, tafara bawa madam Hindu labarin rayuwarta da yaya Habeeb tana dasa aya ta rushe da kuka mai matuk'ar sautin gaske, madam Hindu ta rungume ta tana sharar hawaye domin ita kanta labari Haleesa ya matukar bata tausayi, cikin tausasa halshe tafara rarrashin Haleesa ta hanyar furta mata kalamai masu dad'i Haleesa ta share hawayeta tace mommy narasa yaya Habeeb yatafi yabarni da soyayyarshi a zuciya a kullum tunani nakeyi anyya zan samu Wanda zai so ni kamar yaya Habeeb"?
Za ki samu Haleesa in har kika saka hank'uri da tawakalli Allah zai kawo miki wanda yafi yaya Habeeb Murmushi kawai Haleesa tayi domin tasan abunda madam Hindu take fad'a ba zai ta6a kasancewa gaskiya ta lafe a jikin mommy tana sauke ajiyar zuciya.

```3:00pm```
Chapter 17 · 0% Book details