← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 95

Sashe 72

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

~~Gaba d'aya Habeeb yafita hayyacinsa sai yakai karshen bango yadawo farko bango yana yarfe hannaye kamar Wanda ruwan zafi suka k'ona.
"A d'age Mus'ab yake kallonshi yana murmushi mugunta sai kawai ya d'auke fuskarshi yaciro phone d'inshi gaban aljihun rigarsa ya kira Hannah yana zuba mata kalaman soyayya, yayi kamar bai fahincin halin da Habeeb yake ciki ba.
"Habeeb yarasa idan zai sa kansa jin yake yi kamar duniya ta juya masa baya me yasa leesa za ta yi min haka"?
Me yasa saida ta bari zuciyata tayi niyar fallasa mata sirrin da ke cikinta za ta gujeni domin nasan saboda ni leesa ta koma Abuja yau.
Da sauri yadauko phone d'inshi ya yi dialling number ta ga mamakinsa wayar na ringing ba'a d'aga ba da yacigaba da kira sai ya ji wayar a rufe ya ja iska da k'arfi jikinsa yadauki rawa kamar mai jin sanyi.
Cikin tafarfasa zuciya ya maka wayar a bango ta tararatsi sai kace wayar ce tayi masa laifi.
"Why leesa tell me why do this to me"?
Yak'arasa magana cikin shouting had'e da dukan desk, yasoma watsi da files d'in da ke zube akan desk da sauri Mus'ab ya katse wayar da yake yi da Hannah.
Yanufi wajen Habeeb yarik'onshi da k'arfi kanka d'aya kuwa Lamido"?
Ko kasha kwaya ne ko angaya maka soyayya hauka ne"?
"Habeeb ya ja iska had'e da ya mutsa gashin kanshi manyan idanu nan, nashi suka k'ara firfitowa basu da banbancin da na magge da sauri Mus'ab yadauke idanunshi da barin kallonshi, yace kai ni daina kallona da wad'annan masifafin idanun naka masu firgita mutum gaba d'aya kafara tsorata ni.
matsalarka kenan Lamido komai da zafi ka ke daukarsa zo ka zauna mu yi magana zan nemo maka solution yanzu nan.
''Da kyar Habeeb ya amince ya zauna sai huci yake, kamar Wanda ya yi wrestling Mus'ab ya bud'e fridge yadauko coke na gwagwani ya balle, ya mik'awa Habeeb da k'arfi yafizge gwagwani daga hannun Mus'ab yakafa kai saida ya shanye coke d'in tass....Ya matse gwagwanin cikin tafin hannunshi.
"Mus'ab ya girgiza kai yace ni ina mamaki wannan fushi na menene"?
"Akan wane dalilin leesa za ta koma abuja without my permission"? kasan irin zafi da quna da zuciyata take mun a lokacin da ka ke sanarda ni leesa, ta koma abuja shin ko kasan saura kiris heart attack ya kamani"?
"Mus'ab kacuce ni me yasa ka zuba min desire tablet a drink na kusance leesa da k'arfi"? gashinan a garin wannan iskanci naka ka janyo min leesa ta yi fushi da ni.
Mus'ab ya ja tsaki yace to ae ni taimaka maka nayi na nema maka hanyar da za ka kawarda sha'awarka akanta, to yanzu kuma menene abun damuwa just forget about her my friend mu cigaba da tsara yadda contract d'in nan zai tashi karka manta kai ka ke cewa money is everything, so za ka iya magance wannan matsala da ke tsakaninka da leesa da k'udi yak'arasa magana yana dariyar shak'iyanci.
"mugun kallo Habeeb ya watsawa Mus'ab karka fad'a min maganar banza Mus'ab duk ba wannan shishshigin naka bane yajanyo leesa tayi fushi infact ina ruwanka da sha'awarta da nakeyi ko kai ne ka biyan mun sadakin aurenta"?
"Omg! Wai kai Lamido wane irin masifafen mutum ne huh!"? Abunda ka keso ne nayi maka kai fa kace baka sonta sha'awarta ka keyi to don tayi fushi da kai shine me"?
''Habeeb kamar zai fashe da kuka yace Mus'ab "I'm in love with her wallahi Mus'ab ina sonta inason leesa tankar numfashina.
Mus'ab ya yi ajiyar zuciya yace d'an iska kawai da kana sonta uban waye yace kadinga wulaqantata"? Yanzu kuma it's her turn abun ya juyo kanka, ba lallai bane leesa ta amince da soyayyarka ba.
"Da mugun mamaki Habeeb yake kallon Mus'ab daga bisani ya ja tsaki, ina tsanmani Mus'ab ka manta da waye Habeeb Lamido shiyasa har ka ke tunani leesa bara ta amince da soyayyata ba.
Tabe baki Mus'ab ya yi shikenan Lamido in kana gani kamar wannan zafin kan naka zai sa leesa ta amince da kai ga filin ga mai doki, tun kafin tafiya tayi nisa kafara sauke fushinka akan phone zuwa gaba leesa tana 6ata maka rai wuta za ka cillawa company nan.
"Harara Habeeb ya galla masa ya ja tsaki ya kwashe sauran phone's dinshi da ke zube akan desk yanufi k'ofar fita, Mus'ab ya kyalkyale da dariya yace d'an rainin wayyo, yadauka masa briefcase d'inshi wance garin watsi da files ya had'a da ita ya Mara masa baya yana dariya a k'ofar fita ya had'u da Bala yace Bala please ka saka a gyarawa Lamido office dinshi kasame mu a parking space.
"Cike da mamaki Bala yace maigida Mus'ab lafiya kuwa saboda naga boss yafita cikin mugun fushi yanzu nan ya wanke sister Lora da mahaukacin mari.
"Mus'ab ya zaro ido muryarsa na rawa yace Lamido ya mari sister Lora to me tayi mishi da ya mare ta"?
Bala ya karkace kai yafara kwararowa Mus'ab sharhi dai-dai babbar k'ofar fita ya zo wuce wa yaci karo da Sister Lora by mistake ta goge hannunshi shine fa ware yatsunsa akan kumatunta, ina tsanmani sai taje hospital saboda ta maru ba kad'an ba.
'Mus'ab ya yi dariya yace to BBC shige ka aiwatarda da aikin da nasaka ka.
********************
_ABUJA_
duk kiran da Habeeb yake yi wa Haleesa tana sane tak'i picking da taga ya matsa da kira sai tayi switch off d'in wayarta tanaso tagano har yanzu Habeeb Lamido yana nan akan bakarshi na cewa sha'awarta yake yi ba sonta yake ba ko kuma yanzu yafara sonta ne.
"Don kawai ta musgunawa zuciyarsa yasa ta matsawa Hannah tanemo mu su ticket suka dawo Abuja yau a maimakon sai gobe za su dawo.
Saida dare yayi Haleesa ta zo kwanciya tarena kanta saboda kasa bacci sai juyi take, ta mik'e a sa6ule tanufi part d'in Habeeb, ta kwanta akan katafare Bed d'inshi, can! Idanunta suka hasko Mata d'an k'aramin frame mai d'auke da pic d'in Habeeb da salma akan bedside kishi taji yakamata da k'arfi tafizgo frame d'in ta jefa shi jikin bango ya tararatsi.
"Kawai sai tasa kuka tana magana ita kadai kamar, mai ta6in hankali me yasa ba za ka soni ba yaya Habeeb"?
Ni ina sonka koda baka sona kuma zan cigaba da sonka har zuwa karshen rayuwata.
"A da na dauka daga kan margayi yaya Habeeb bara k'ara son wani D'a namiji ashe abun ba haka bane da kyar tasamu bacci yadauke ta.

```HABEEB```

Asuban fari Habeeb ya tashi yana gama sallah yacigaba da trying number Haleesa, still wayar a kashe yadafe kai zuciyarshi na soya yaja tsaki yafi a kirga.
"Haushin Haleesa yakama shi yafara zance zuci har ni leesa za ta wulaqanta in kirata tak'i picking daga k'arshe ta rufe wayarta don kawai ta fahimce na kamo da sonta sai na nuna mata cewa mace bata yi mun wulaqancin.

_10:00am_
A hankali Habeeb yake taka staircase sanye yake da black colour suit, hannaye shi na zube cikin aljihu wandonshi fuskar nan tashi a murtuk'e.
''Ya hango Mus'ab da Bala zaune akan dining table suna breakfast kallo d'aya yayi musu yadauke fuska.
Mus'ab yace Lamido ka zo ka yi breakfast harara Habeeb ya galla masa, tsawon zamanka da ni kata6a gani nayi breakfast a irin wannan lokacin"?
Uhm.....Mus'ab yafad'a had'e da tabe baki yacigaba da cin abincinsa.
A yatsine Habeeb ya dube Bala yace Bala ka yi sauri ka gama ka kaini airport.
"Cikin Tsananin mamaki Mus'ab ya ajiye fork d'in hannunshi me za ka je yi a airport Lamido"?
"Abuja zan tafi yafad'a kaitsaye yanufi 1 seater ya zauna yayi crossing legs, da alama yau 'yan rashin mutuncin sun motsa.
Mus'ab ya mik'e had'e da ture kujera yanufi wajen Habeeb me ka ke shiri aikatawa Lamido"?
"Habeeb ya ja iska can! K'asan mak'oshi yace bara iya jure rashinta ba Mus'ab koda ba zan ganta ba atlast ko muryata ce naji na tabbata jin muryarta kadai zai sa nasami kwanciyar hankali yak'arasa magana kamar zai yi kuka.
"Mus'ab ya zauna bisa hannun kujera da Habeeb yake kai yadafa kafad'arsa bai kamata akan wannan abun kad'aga hankalinka ba leesa matarka ce kamata ya yi ka lalla6ata Ku gyara zaman aurenku ka jinginar da wannan zafin kan naka domin yana d'aya daga cikin abunda yake hanaka jin dad'i rayuwa.
"Katuna manzon Allah{s,a,w} yahane mu da fushi don haka Lamido ka yi wa kanka fad'a karage fushi domin ba abunda fushi yake haifarwa face danasani.
"Karka manta daga kai har leesa kun aure junanku ne batare da kuna son juna ba Haleesa akwai Wanda takeso mutuwa ce ta raba su kaga kenan mafi mahimmancin kafara cusa mata soyayarka ka goge kiyayyarka daga zuciyarta domin ka cutarda ita ba kad'an ba.
"Habeeb yayi ajiyar zuciya yace shiyasa nakeso tafiya abuja yau d'inan na sanarda ita irin son da nake mata.
''Lamido bai kamata ka tafi abuja yau ba kamata gobe ne tafiyar mu Japan"? Kuma wannan tafiya dole sai da tare kai ka yi hak'uri har Allah yadawo da mu lafiya zuwa wannan lokacin leesa ta huce Mus'ab yacigaba da rarrashin Habeeb had'e da yi masa dad'in baki har yayi nasara hanashi tafiya.
***********************
_3 day's later_
Chapter 72 · 0% Book details