← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 95

Sashe 55

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

~~A hankali ya ja towel yarufe mata k'irji wani irin kasala mai had'e da tsintsa shawa'a suka lullu6e shi, ya zauna a gefen k'afafuta ya dafe kanshi da hannaye shi yad'ago ya sace kallonta she is still unconscious yadauke fuskarshi ya lumshe idanu image d'in abunda yafaru yafara yi masa shawagi surar jikin Haleesa yake gani da sauri ya bud'e idanu ya ware su akan fuskarta, d'an k'aramin bakinta mai d'auke da pink lips ya k'urawa ido jin yake kamar ya sumbace ta a wannan karon kasa d'auke idanunshi ya yi akanta tsawon lokacin yadauka yana kallon kyakyawar surar jikinta sai kawai ya tsince kanshi da zance zuci _ashe haka yarinya nan take"?_
Ya sauke ajiyar zuciya _she is very beautiful_
Saida shekaru ta sun yi k'ank'anta a tsarina banaso mace mai k'anana shekaru nafiso mace mai shekaru da yawa tun daga kan marigayiya salma nagano amfani auren mace take da shekaru ita ce tasan yadda ake tarairaya miji sa6ani wannan da batasan komai ba sai tsoro da kuka wannan yaya Habeeb d'in ya riga ya sagarta ta gashi yatafi ya barni da lalura ya ja tsoki da ace ina son yarinya nan da zan juri na rene ta har ta kai shekaru da nakeso matata ta kasance da su, ya shafi lallausar saje shi ya mik'e da kyar kamar Wanda yasha kayan maye yashiga kitchen ya bud'e fridge yadauko robar ruwa yadawo parlour har yanzu idanunta na rufe.
"Ya balle murfi ruwan ya zuba a hannunshi ya tsuguna dai-dai fuskarta ya Shafa mata tasauke katuwar ajiyar zuciya saidai bata bud'e idanunta ba.
Tsabar iskanci irin na Habeeb Lamido saida ya dube saitin k'irjinta inda towel bai ida rufewa ba ya tsiyaya mata ruwa, Zubur Haleesa ta yi ta mik'e zaune a firgici ta furta _wayyo yaya Habeeb ka jefar da maciji nan kada ya cije ka_
"Gani yadda ta yi magana Habeeb yagano har yanzu bata dawo a hayyacita ba ke"! Yadaka mata tsawa
A tsorace ta dube shi sai fama zare ido take yi
Ya muturk'e fuska Macijin roba ne zai cije ni yak'ara sa magana yana yatsina.
Haleesa tak'ara zaro idanu a rikice ta furta maciji roba kuma"?
''Kwarai kuwa maciji roba ne tsabar rashin hankalinki ne yasa ki ka kasa gane na roba ne yak'ara sa magana yana mata kallon banza.
"Cikin tsanani mamaki Wanda yakasa boyuwa akan fuskarta tace macijin roba to me yakawo macijin roba a room d'ina"?
''Tabe baki yayi kamar bara bata amsa ba sai da ya ja iska yace tsaraba da Imaan tace na siyo mata a Canada ne.
Ran Haleesa ya yi mugun b'aci har takasa boyewa cikin tafarfasa zuciya tace _haba yaya Habeeb yanzu ka Lula uwar duniya har Canada karasa abunda za ka yiwa 'yarka tsaraba da shi sai macijin roba wannan wace irin d'abi'a ce"?_
"Habeeb Lamido ya yi sororo yasaki baki da hanci yana kallonta tsanani mamaki da kuma k'arfin halinta su ka hana shi furta uffan sai faman kallonta yake.
''Ganin yadda ya tsareta da mayyu idanunshi yasa ta kalli jikinta ta zaro ido da sauri tasaka hannayeta takare k'irjinta.
Abunda ya yi masifar k'ular da shi ya galla mata harara Me ye kuma na wani kare k'irji"?
Abunda ki ka sake a fili sai ni ne na taimaka na rufe miki shine don tsabar iskanci za ki wani kare zai fi miki sauki ki bar shi a haka domin ba burge ni zai yi ba yak'arasa magana yana yatsina.
"Kunya ta lullube Haleesa ko kwakwara motsi takasa wannan yaba Habeeb Lamido dama yacigaba da gasa mata maganganu masu zafi da k'ona zuciya da ki ke zance narasa abunda zan yiwa Imaan tsaraba da shi sai macijin roba da shi naga dama yi mata tsaraba, tun da nat fahimce kina tsoron maciji sai nasa an nemo mini masu rai k'ato kg zan yi a gidanan na zuba su da na kamaki kina mini kukan mutuwar saurayinki a gida sai nasaka ki a ciki sun cinye ki In yaso ki bi saurayinki da ya koya miki soyayya lahira sai Ku cigaba daga inda ku ka tsaya.
''Jikin Haleesa yadauki rawa ta hadiye yawu masu masifar d'aci tsoro mai cike da fargaba ya yi nasara lullu6e ta hawaye suka wanke mata fuska cikin sark'ewar harafi tace dan Allah yaya Habeeb Ka yi hank'uri karka kawo maciji a gidanan wallahi ina masifar tsoronshi ka ji tausayina yaya Habeeb.
''Harara Habeeb ya watsa mata dallah''! tashi ki sako kayan kirki ki zo ki gyara mini room d'ina wannan magiya da ki ke yi ba shi zai sa na fasa abunda na yi niyya.
"Shiru Haleesa ta yi takasa tashi
"Ina magana kin yi ignoring d'ina yana d'aya daga cikin dalili da zai sa na kawo miki maciji a gidanan.
Ba bu shiri Haleesa ta mik'e garin sauri towel d'in jikinta ya zame da sauri tadafe shi tajuya da gudu tashige bedroom d'inta.
Habeeb ya lumshe ido yana shafar sumar kanshi a hankali tsawon _3 minutes_ yadauka a haka daga bisani ya mik'e yanufi part d'inshi.
"Haleesa na karasawa d'akinta tafad'a bisa bed ta yi ruf da ciki shikenan yaya Habeeb yagama gane mini k'irji mugu kawai da sauri ta mik'e kada yaji ta shiru yashigo yak'ara ganinta haka ta bud'e wardrobe tafito da fitted gown na atamfa tasaka ta yi light makeup ta bi lungu da sak'o na jikinta da perfumes masu sanyi k'amshi direct part d'in yaya Habeeb tanufa tun zuwanta Abuja bata ta6a shiga part d'inshi wannan shine karo na farko da k'arfarta ta taka zuwa part d'in.
Tana zuwa last stairs ta yi tsaye tana tunani yadda za'a yi ta had'a ido da shi saboda kunya takeji yaganta half nacked
"Tsawon _5 minutes_ ta d'auka a tsaye tana shawara da zuciyata ganin tsayuwa bara fisheta ba ta turo k'ofar glass tashiga parlour sanyi Ac da k'amshi air freshener yadak'i hancinta ta lumshe idanu, cikin muryarta mai sanyi ta yi sallama yana zaune a 3 sitter hannunshi rik'e da handle cup yana slipping d'in White wine ya amsa mata a dak'ile karaf idanunta suka sauka bisa bottle d'in white wine da ke ajiye bisa stool saura kiris numfashinta yadauke a tunani Haleesa giya ne saboda bata ta6a sani akwai juice mai irin bottle d'in giya _dama yaya Habeeb mashiyi ne"? haba biri ya yi kama da mutum wannan iskanci da yake shek'awa ashe aikin chaji ne shiyasa kullum idanunshi a lumshe yana magana yana Jan iska kamar Wanda yaci yaji"?_
Cikin abunda bai fi _30 second's Haleesa ta yi jerowa kanta wad'annan tambayoyi_
"Habeeb Lamido yad'ago ya dube Haleesa idanunshi a lumshe _yace ke me ki ke jira ne kin wani tsare ni da ido sai kace kin ci karo da marigayi saurayinki_
Yana k'arasa magana ya yi slipping juice
"Haleesa tak'ara tsorata musanmman da ta hango glassblower jere da white wine kala-kala tak'ara gigicewa a zuciyata tace ashe bansaniba gidan giya nake zaune ashe madam Hindu tasan d'anta mashayi ne shine ta yi ruwa tayi tsaki tayi sanadin da na aure shi ta fake da tausayina takeji
Wallahi ta cuce ni shikenan ta kassara min rayuwa.
Ke! Wai me ki ke jira ne"? ni fa na tsani kallo
Hawaye da Haleesa take boyewa suka gangaro akan fuskarta ta kwasa da gudu tafice daga parlour tana kuka kamar ranta zai fita.
"Tsanani haushi ya turnuk'e Habeeb muddin yarinya nan bata daina yi mini kukan mutuwa saurayinta a gida sai na yi mata wulaqanci mai Sosa zuciya yak'ara sa magana had'e da Jan tsoki ya mik'e a zafafe yanufi part d'inta cikin zafin rai ya murd'a handle ya ji k'ofar a rufe.
Da k'arfi yafara knocking Haleesa da ke kwance akan bed tana rera kuka ta mik'e zaune a firgici ta gallawa k'ofa harara kamar tana ganin Habeeb duk knocking d'in da yake yi ta yi banza da shi.
Habeeb yak'ara harzuk'a ya yi k'udiri in kama Haleesa sai ya yi mata abunda bata ta6a tsanmani ba cike da haushinta yajuya part d'inshi.
Chapter 55 · 0% Book details