← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 95

Sashe 59

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

```HALEESA```
_Haleesa_ tana cikin kitchen sai ta ji ana sallama, da sauri ta fito ga mamakinta sai taci K'aro da Mus'ab zaune akan 1 sitter da murmushi tak'arasa shiga parlourn _sannu da zuwa Mus'ab_
''Yauwa Haleesa ya gida duk da naji gidan tsit yak'arasa magana yana 'yar dariya.
Haleesa ta yi murmushi ta koma kitchen tadauko masa kwalin fruitta mai sanyi had'e da glass cup ta tsiyaya ta mik'a masa tanemi kujerar da ke facing d'inshi ta zauna ta sada kai k'asa saboda tana mai jin kunyar abunda yafaru jiya.
''Mus'ab ya d'an yi slipping juice d'in ya ajiye cup bisa stool ya yi gyaran murya, yace Haleesa dama zuwa na yi na baki hankuri akan abunda yafaru shi kanshi lamid'o ya yi Nadama abunda ya yi miki kawai yana jin kunyar yadda zai yi facing d'inki yabaki hankuri amma yace nace da ke ki yi hankuri Sharrin shed'an ne.
"Haleesa ta yi murmushi domin tasan abunda Mus'ab yafad'a ba gaskiya bane Habeeb Lamido ne zai ce a bata hankuri ae ba yau ya sa6a cin mata zarafi Wanda yafi wannan ya yi mata bai ce a bata hankuri ba sai wannan.
''Idanunta suka ciko da hawaye bata damu da ta goge su ba, tace ba zan 6oye maka ba Mus'ab a da ina da ra'ayi zama da yaya Habeeb koda ace zai dinga yanka naman jikina sai yagajin don kanshi ya saleme ni, amma a yanzu nayi nadamar aurenshi ba don komai sai don ya kasance mashayi ni kan bara iya rayuwa da mashayin giya tak'arasa magana cikin shasshek'a kuka.
''Mus'ab ya zaro idanu a rikice yace giya fa ki ka ce Haleesa"?
''Kwarai Mus'ab abokinka mashayi ne Sam babu tsoron Allah a tare da shi a cikin gidanan yake shan abarsa ya yi tatul.
"Da mugun mamaki Mus'ab yake kallon Haleesa daga bisani yace to ke Haleesa menene shedarki Lamido yana shan giya"?
Ni kuwa nakeda sheda mu je part d'inshi ka ganewa idanunka Haleesa tashige gaba Mus'ab yana biye da ita saboda iya zamanshi da Habeeb yasan ko cigarette ba yasha asalima ya tsanin duk wani abu da yake saka maye.
''Haleesa ta turo k'ofa suka shiga cikin parloun ta nunawa Mus'ab glassblower da ke d'auke da jerin white wine kala-kala Mus'ab ya yi ajiyar zuciya ya bud'e glassblower yaciro bottle gudu ya mik'awa Haleesa da sauri ta ja baya tana wani zare idon Mus'ab ya kyalkyale da dariya yace ki k'ar6a mana so nake ki karanta rubutu da ke jikin bottle d'in a sanyaye Haleesa ta k'ar6a ta karanta juice ne da aka sarafa da fruits sannan kuma an rubuta non alcoholic Haleesa tasauke ajiyar zuciya wani sanyi ya ziyarce zuciyata ta runtse idanu daga bisani ta ware su cikin jin kunya tace gaskiya na yarda da maganar yaya Habeeb da yake cewa ni villager ce amma kuma Mus'ab karka ga k'auyancin na saboda ban tashi a gidan da ake shan irin wad'annan abubuwan ba.
Mus'ab ya yi murmushi yace ki kyalle Lamido shima bak'auye ne sannan kuma ba ke kadai ki ke kallon wannan juice a matsayin giya mutane da dama Wanda ba su San juice bane a haka suke kallonsa.
''Haleesa ta yi dariya tajuya Mus'ab ya Mara mata baya suka koma parlournta, yacigaba da bata hank'uri saida ya tabbata da ta hank'ura sannan ya yi mata sallama.
_5:00pm_
Haleesa tana zaune a parlournta Imaan ta isheta da rigima a dole sai sunyi wasan 'yar 6oya Haleesa ta yatsine fuska ta ajiye phone d'inta bisa hannun kujera ta rik'on hannun Imaan suka nufi compound daga idan suke zuwa main gate akwai tazara sosai Haleesa taciro d'an kwalin kanta gashinta yasauka a gadon bayanta, tace da Imaan zo nan babyn aunty na daure miki idanunki
''Imaan tadaka tsalle cikin shagwa6a tace Allah aunty ke ce first ni kuma second Haleesa ta yi dariya tace kai....ka ji min yarinya da wayyo tana magana tana daure fuskarta idanunta na rufe tace 1.....2....3.... Start tasoma lallu6en Imaan tana jin dariyar Imaan amma takasa kamata, haka tacigaba da lullube.
''Bala yaddano hancin mota cikin compound Habeeb na owners corner a zaune tun kafin su k'arasa parking space ya hango Haleesa da Imaan suna wasa yaja tsoki a zuciyarshi yace k'aramar kawai Bala yana dariya ya bud'ewa Habeeb k'ofa yafito
"Boss yau amarya ta tuna da k'urciya wasan 'yar 6oya sukeyi yak'ara sa magana yana wani Sosa kai.
Harara Habeeb ya watsa masa yace kadauko briefcase ka shigar min da shi ciki Yajuya yanufi cikin gida.
"Babyn aunty where are you I'm tight zan bud'e idanuna in bara ki bari na kama ki ba Imaan ta kyalkyale da dariya tace _yeee.... Aunty if you're can catch me_
Da sauri Haleesa tanufi idan takejin sautin muryarta dai-dai Habeeb yakawo da sauri Imaan ta boye bayanshi garin lallube Haleesa ta yi tuntube za ta fad'i da sauri Habeeb yatare ta tafad'o kan k'irjinshi..........

Jeeddah Aliyu🌹

[22/11 4:05 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*

```77```

~~A hankali ta bi jikinta da kallo gaba d'aya zo6o yabata mata kaya a harzuk'e tad'ago idanunta Wanda suka canza colour zuwa red, kallo d'aya za ka yi mata ka hango b'acin ranta yadda ta tsare Habeeb Lamido da ido za ka yi tsanmani za ta zanga masa mari ne.
"Kallo mai cike da zazzafar tsana Habeeb yake watsawa Haleesa cikin tafarfasa zuciya yadaka mata tsawa cikin angry voice ya furta _How dare you ni za ki wulaqanta in front of my friends"?_
''Kafin Haleesa ta ba shi amsa Mus'ab ya taso yashiga tsakaninsu ranshi a b'ace yace _what's wrong with you Lamido akan wane dalilin za ka yi mata wannan d'ayen wulaqancin matarka ce fa"?_
''Kallon banza Habeeb ya watsa masa so what's don tana matata shi zai bata dama tacin min zarafi a gabanku"?
Haleesa ta yi karaf tace ancin zarafin naka yaya Habeeb ka yi duk abunda za ka iya ae ba tsoronka nakeji ba, tana k'arasa magana ta yi shigewarta bedroom tabar Habeeb Lamido sake da baki sai faman huci yake yi bai ta6a tunanin Haleesa za ta iya maida martanin abunda yake mata.
"Mus'ab ya ja tsoki ya dube khaleel yace tashi mu tafi khaleel a zahirin gaskiya nayi danasanin zuwanmu gidanan da bamu zo ba Lamido da bara ka, same damar wulaqanta 'yar mutane ina mamaki wannan miskilancin da girman kan naka Lamido ka gyara halayyarka ko za ka jin dad'i rayuwa.
''Khaleel ya kar6e zance ta hanyar cewa wannan abun da kayi Lamido kasanin ba burgewa bane, wulaqanta mace ba abu bane mai kyau muna jiye maka ranar Nadama.
''Yana k'arasa magana yarik'o hannun Mus'ab mu tafi kawai Mus'ab kana kallon irin kallon banzar da yake mana.
''Habeeb ya ja tsaki yace sai me don kuntafi dama can! Ban gaiyyace Ku ba ra'ayin kanku ne yakawo gidanan don kuntafi bara jin zafi ba asalima zuwanku wulaqancin ya janyo min tunda nake da yarinya nan banta6a magana ta mayar mun da amsa ba sai zuwanku banzaye kawai.
''Mus'ab ya galla masa harara yace ae Kaine banza Wanda baisan darajar matarshi ba wallahi Lamido in na cigaba da tsayuwa a gabanka haushinka da nakeji zai iya haddasa min hawan jini.
''Habeeb ya ja tsoki had'e da ficewa daga parlourn yabar Mus'ab da khaleel tsaye suna mamaki wannan halayen nashi daga bisani suka kama gabansu.
***********************
Kuka Haleesa taci kamar ranta zai fita tabbas Habeeb Lamido yade6o da zafi daga yau bara k'ara d'aga masa k'afa saidai ya yanka ni a gidanan.
Chapter 59 · 0% Book details