← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 95

Sashe 12

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

```LAGOS```
Yau kwana Haleesa biyu a garin Lagos duk da tun zuwa ta ko k'ofar gida bata lek'a ba amma yanayi gari yayi mata dad'i ta tsince kanta cikin farin ciki Wanda rabonta da shiga irinshi tun yaya Habeeb yana raye.
Haleesa tafito daga d'akin da aka ware mata tanufi _kitchen_ tana taya aunty juwairiyya aiki.
Aunty juwairiyya kinada _visitor's_ ne
naga tun safe kike ta faman girke-girke"?
Mahaifiyar maigida masa'ud daga Abuja za ta zo Lagos duk lokacin da ta zo Lagos sai na girka mata abinci kala-kala na kai mata saboda tana matuk'ar jin dad'i girki na.
_"Humm aunty juwairiyya tana jin dad'i girki ki ko dai kuna neman gidin zama Haleesa tak'arasa magana cikin dariya_
Juwairiyya ta kyalkyale da dariya daga bisani tace kai Haleesa kin shiga uku ko ma gidin zama muke nema ae muna da gaskiya zamani nan dole sai ana had'awa da hakan musanmman shugaban _company_ nasu akwai zafin rai tsiya Sam bayason wasa da aiki Haleesa tayi murmushin had'e da cewa ae shima yanada gaskiya.
Bayan sun kamalla girkin kowane su yasha _make up_ musanmman Haleesa da takeji jin kanta kamar sabuwa rayuwa za tayi a Lagos shiyasa lokacin da juwairiyya tace ba za ta bita ba sai tayi kwalliya batare da tace koma ba ta ca6a adonta cikin 'karamar atamfa _super Holland_ dark green da touch's din yellow tayafa _veil yellow colour_ ita kanta da ta dube mirror saida ta yabawa kanta.
Tana fitowa suka shiga mota masa'ud yaja mota suka d'auki hanyar _Victoria island_ masa'ud yafara tsokanar Haleesa ta hanyar cewa wannan irin kyau Haleesa ko d'an Lagos za ki samo mana"?
Haleesa ta turo baki had'e da cewa Allah ya kiyaye me zanyi da bayarbe"?
Masa'ud ya kyalkyale da dariya yace wayagaya miki yarbawa ne kadai a Lagos"?
Ni dai banaso Haleesa tafad'a kamar za tayi kuka
Masau'd yace to wa kike so"?
Haleesa ta galla masa harara tace kai!
Masa'ud da juwairiyya suka kyalkyale da dariya daga bisani masa'ud yace ni kan na juwairiyya ne kiyi 'ko'kari ki nemo naki ko kuma mu ba da sadakarki.
Haleesa kamar za tayi kuka tace Ni yaya Habeeb kadai nakeso tun da narasa shi saidai in mutu banyi aure ba ko kuma Ku bada sadaka ta.
Masa'ud da juwairiyya sai dariya suke mata har suka shiga had'adiyar unguwar nan ta masu kudin Lagos _Victoria island_ tafiya mai nisan gaske sukayi daga bisani suka nufi wani had'ad'e gida _gate_ d'in gidan kadai abin kallo ne _horn_ masa'ud yadanna bayan kamar _5 minutes_ gate d'in ya bude yadanna hancin motarsa yana shiga _securities_ suka taso saida sukayi _checking_ d'in motar masa'ud daga bisani suka barsu shiga gate na biyu saida bai kai tsaruwa na farko ba Haleesa sai zarar ido take tacigaba da kallon inda masa'ud yadosa wani karamin _parkin space_ yanufa yayi parking cikin zuciya Haleesa tace wannan shine na ba'ki a hankali ta mayarda idanu ta wurin k'aton _parking space_ mai d'auke da tsalatsala motoci lullube cikin _tenfold_ Haleesa bata sha kallo ba saida suka shiga cikin _main parlour_ gidan wata munmuna mata suka fara cikin karo da ita tana sanye da _black colour mini skeet da farar Riga gashi kanta lullube da attachment da sauri ta nufo waje su ta kar6i warmer d'in hannu masa'ud tanufi cikin wani karamin parlour yayinda su Haleesa suka Mara mata baya_
Kujera ta nuna musu masa'ud ne kadai ya zauna Haleesa da juwairiyya sukayi tsaye suna jiran matar tadawo ta kar6i Warmer's d'in hannu su........
[28/08 9:55 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```29```

Bayan matar mai kirar katti tazo ta kar6i Warmer's d'in sannan su Haleesa suka zauna bayan tadawo tace da su madam na zuwa tajuya ta koma inda tafito, a hankali madam Heendu take taka matakala bene fuskarta tadauke da murmushin da ke baiyanar da farin cikinta nagani bak'inta{visitor's} 'kamshin turare ta yadaki hanci Haleesa da sauri tad'aga kai ta dube ta kyakyawar fara mace kamar kata6a fatarta jini yafito kamanu matar kadai ya Haleesa ta kalla tagano cewa balarabiya ce tana sanye da tsadadiyar _combination shahada da material d'inki Senegal wuyanta yasha gold kirar Dubai_
Tana k'arasa shigowa _parlour_ masa'ud da juwairiyya suka mik'e tsaye gani Haleesa tak'i mik'ewa tsaye yasa juwairiyya ta galla mata harara dole Haleesa ta tashi tsaye madam Heendu ta rungume juwairiyya ta sunbace kumatu ta hagu da dama tajuya wurin Haleesa ta rungumo ta ta sunbace ta kamar yadda ta yiwa juwairiyya a zuciya Haleesa tace kutt yau kuma ga wata sabuwa bidi'a cikin girmamawa masa'ud da juwairiyya suka kwashe gaisuwa dole Haleesa tayi yadda ta ga sunyi daga bisani madam Hindu ta zauna sannan suma suka zauna a zuciyar Haleesa tace kai jama'a duniya ina za ki damu _kudin bala'i ne ita wannan ba matar President ba ba kuma matar governor ba amma don tsabar girmamawa sai ta zauna mutane suke zaunawa_ ta dube Haleesa tana murmuahin ras-ras gaban Haleesa yafadi domin tayi mata kama da wata halitta da ta6a gani kafin ta lala6o inda ta ta6a gani mai irin kamanu madam Hindu sai ta ji sautin murya madam Hindu tana cewa juwairiyya amma wannan sister ki ne" koh"?
Juwairiyya tace eh madam Hindu tace saidai tafi ki kyau 'yan mata ya sunan ki Haleesa ta hadiye yawu da kyar tace......

```DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S ```

Jeddah Aliyu🌹
[29/08 8:09 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [29/08 12:13 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```30```

"Sunana Haleesa, _madam Hindu_ tace sunanki mai dad'i har yaso yafi na Juwairiyya dad'i tak'arasa magana cikin dariya Juwairiyya tayi murmushin tace _Allah mommy nima sunana yana dad'i_
Nima bance sunanki bai dad'i ba Juwairiyya amma na Haleesa yafi dad'i saidai matsala Haleesa bata magana.
Juwairiyya da masa'ud suka kyalkyale da dariya, Janet ta shigo hannuta rike da _tray_ da kwalaye _juice a sama had'e da glass cups ta ajiye bisa stool ta tsiyayawa su juwairiyya Haleesa ta kar6i cup d'in_ tana jujuya shi yayinda suka cigaba da firar su Haleesa kanta na sunkuye tana saurare firar tasu, tsawon _2 hour's_ suka share suna fira daga bisani masa'ud ya mik'e tsaye yace madam bara mu barki ki huta sai gobe insha Allah zan shigo mu yi magana akan wance _Issue_
_alright_ masa'ud ba matsala sai ka zo Amma Haleesa nan za Ku barta ta tayani fira ko bara ki zauna ba Haleesa"?
Madam Hindu tak'asara magana had'e da duba fuskar Haleesa a tsorace Haleesa tad'ago tana kallon madam Hindu karaf Juwairiyya tace za ta zauna mana, Haleesa ta sada kai k'asa jin takeyi kamar tafasa ihu akan wane dalilin aunty Juwairiyya za ta yanke wannan hukunci akaita, gani yadda Haleesa tayi shiru yasa madam Hindu tace anyya Juwairiyya Haleesa za ta zauna kuwa saboda naga ta sada kai k'asa"?
Da sauri Haleesa tad'ago murya ta na rawa tace zan zauna _Mommy_
Juwairiyya tasaki ajiyar zuciya saboda tasan halin Haleesa sarai za ta iya cewa ba za ta zauna ba, madam Hindu tana dariya tace shikenan juwairiyya Haleesa ta 'kwace miki fada a wurina, a wannan karon masa'ud ne yabata amsa ta hanyar cewa madam in dai Haleesa ce ba ki kama kowa ba saboda za ki yini guda cur da ita batare da kin ji muryar ta.
Madam Hindu tayi murmushi mai sauti tace "wai haka ne Haleesa"?
Girgiza kai Haleesa tayi madam Hindu tayi dariya had'e da cewa masa'ud Haleesa ta karyata zance ka don haka ja matarka Ku tafi gaba d'aya su suka kyalkyale da dariya daga bisani madam Hindu tace ina zuwa ta haura bene{upstairs} Da sauri Haleesa ta dube juwairiyya da masa'ud da alamar fad'uwar gaba a tattare da ita cikin sar'kewa halshe tace aunty Juwairiyya kuna nufi a gidanan za Ku barni"?
Kafin su bata amsa su ka ji tak'on takalmi madam Hindu hannuta ri'ke da katuwa Leda fara ta mik'awa Juwairiyya, yayinda juwairiyya ta du'ka tayi godiya Haleesa na kallonsu suka fice daga falon.
Cikin zuciyar Haleesa tace wannan wane irin d'aye hukunci ne"? ni bansan wannan matar ba kuma mutane nan sun tafi sun barni tare da Ita in muguwa ce fa"?
A tsorace Haleesa tad'ago tana duba madam Hindu da ke zaune a two Star hankalinta na wajen tv Haleesa taji wani matsananci faduwar gaba, saurtin murya madam Hindu ce tadawo da Haleesa daga natsuwarta sakamako kwadawa Janet kira da tayi da cikin tafiyar sauri Janet ta'karaso d'auke da _Warmers d'in abinci da Juwairiyya ta zo da shi ta ajiye tayi saving madam tasauko k'asa ta zauna bisa center carpet_
Ta dube Haleesa tace Haleesa zo mu ci abinci cikin sanyi murya Haleesa tace na koshi mommy"
"Madam Hindu tayi murmushi tace ina matuk'ar jin dad'i abincin Juwairiyya ta iya girki sosai ina fatar kema kin iya domin kwarewa da iya girki shine mace"?
Haleesa tayi murmushi had'e da cewa nima ina d'an k'ok'artawa
To ki k'ara bada himma domin iya girki yakansa mace tasami babban matsayi a zuciyar mijinta kinga ni nan lokacin da maigidana yana raye muna da _chef_ kuma kwarare ne sosai a fagge sarafa abinci amma Sam bana bari sa ya girkawa maigidana abinci ni nake girka masa da kaina, wasu lokuta a wurin _chef_ d'in nake koyo wasu girke-girke.
Har madam Hindu ta dasa aya a zanceta Haleesa tana kallonta daga bisani Haleesa tayi murmushi had'e da cewa _Allah yajikansa ya gafarta masa_
Ameen madam Hindu tafad'a had'e da ture _plate_ d'in gabanta
A zuciyar Haleesa tace ikon Allah matar nan nada saukin kai kalli yadda take bani labari abunda bai shafeni ba haka madam Hindu tacigaba da Jan Haleesa da fira sai ga Haleesa tasaki jikinta har da su tintsira dariya.......
[29/08 5:30 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```31```

```DARE```
Chapter 12 · 0% Book details