← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 95

Sashe 65

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jeeddah Aliyu🌹

[29/11 6:21 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*

```81```

~~suna had'a ido tasake masa murmushi Wanda ya haddasawa Habeeb mutuwar jiki ya ja iska, had'e da cizo lips d'inshi na k'asa Ya tsare ta da idanu kamar tsohon maye.
"Haleesa tak'arasa kusa da shi tana magana had'e da 'yar dariya yaya Habeeb na manta ba ka sha maganinka ba.
Tsaki ya ja Cike da takaici Yace dama shine dalilin da yasa ki ka shigo min room a wannan lokacin"?
Eh mana tafad'a had'e da dauko ledar magani ta zauna a gefen gado.
"Ranshi a 6ace ya mik'e zaune yafisge ledar daga hannunta ya jefar ya rik'e hannayenta duka biyu can! K'asan mak'oshi yace ke! Wannan magani da za ki bani bashida amfani a tare da ni bara iya warkarda cutar da nake d'auke da ita saboda haka ko kin bani bara sha ba yak'arasa magana yana kallon cikin idonta.
Haleesa tarausayar da kai had'e da marairaice murya tace ba don kace na yi maka shishshigi ba da nace wane irin cuta ne yake damunka"?
''Har Habeeb ya bud'e baki da sunan ya zaiyano mata buk'atarsa sai kawai wani 6angare na zuciyarsa ya kwa6e shi _haba Habeeb kai fa jarumin namiji ne Wanda ba ya sauya magana ko ka manta da irin furucin da ka yi akanta ne"?_ _kana furta mata abunda ka ke da buk'ata za ta d'auka kamar kana sonta ne alhali kai ba sonta ka ke yi ba karka sake ta fahimce halin da ka ke ciki domin girmanka zai zu6e a wurinta_
"Habeeb ya dawo daga duniyar tunani ya sauke ajiyar zuciya ya tsayar da idanunshi akan fuskar Haleesa, wance tun lokacin da ya afka tunani ta kafenshi da ido jikinsa a sanyaye yasake mata hannu ya juya mata baya.
''Haleesa ta yi shiru tana kallon bayansa tsawon lokacin ta dauka a haka daga bisani cikin sanyin murya ta kira sunansa, _yaya Habeeb_
A fusace ya mik'e zaune ya galla Mata harara _look I don't want any disturb now so leave my room_
Haleesa ta kad'a kai batayi mamakin jin wad'annan kalamai daga bakin Habeeb ta mik'e tsanm! Sum-sum tafice Batare da ta furta uffan ba
yayinda Habeeb yabita da kallo ya ja iska yafesar yana tsotsan bakinshi, ya koma ya kwanta da yarufe ido Haleesa yake gani yakasa bacci sai fama juyi yake akan bed bacci ya k'auracewa idonsa, ji yake yi kamar ya mik'e ya je room d'inta ko k'amshin jikinta yashak'a ya tabbata zai same sauki abunda yake ji a game da ita a haka bacci ya sud'ad'o ya sace shi batare da ya nemawa kansa mafita ba.
''Ta6angare Haleesa kuma ita ma hakan ce tafaru da ita da ta rufe idanu Habeeb Lamido take gani, yayinda wani bak'on al-amari yake ziyartar jininta da kyar tasamu baccin yadauke ta.
**********************
_WASHE GARI_
_10:15am_
Haleesa na tsaye a dining area tana jejjera breakfast akan dining table, tana kamallawa tanufi part d'in Habeeb.
"Kwance ta tararda shi akan _3 seater_ idanunshi a rufe jin sallamarta yasa ya bud'e idanu kallo d'aya ya yi mata yadauke kai _ina kwana yaya Habeeb ya lafiyar jiki"?_
"Lafiya! Ya amsa ya a dak'ile.
Breakfast na jiranka tafad'a cikin murmushi
Tabe baki ya yi a tsarina sai 11:00 o'clock nake taking breakfast yak'arasa magana had'e da lumshe idanu.
"Haleesa ta yatsine fuska tanemi kujerar da ke facing d'inshi ta zauna, ta rafka tagumi.
''Ke! Ya kira sunanta a nitse da sauri Haleesa ta dube shi, still idanunshi a rufe ke! Zo nan yak'arasa magana had'e da yafito ta da hannu jiki a sanyaye Haleesa ta mik'e tanufi wurinshi.
''Ganin idanunshi a lumshe yasa tace yaya Habeeb gani
Na ganki mana ko angaya miki ni makaho ne da za ki ce min ga ki yana magana ne had'e da bud'e ido d'aya
"Um.....Haleesa tafad'a tana turo baki ya gyara kwanciyarshi cikin isa da tak'ama yace tausa za ki yi min ina fatar kin iya"?
A tsorace ta waro ido umh......umh....a wane waje zan tausa ma"?
"Bayanshi yanuna mata hannunta na rawa tafara yi masa tausa da ta daura hannunta a bayanshi sai ta d'auke da sauri kamar wance take ta6a electric shock.
''Ran Habeeb ya yi matuk'ar 6aci lallai yarinya nan ta renani kalli yadda take ta6ani kamar tana ta6a kashi da k'arfi ya rik'ota yajuyo da ita ta gabanshi ya mik'e zaune ke! Wannan wane irin tausa ne ki ke min abun Sam ba armashi"?
"Haleesa ta turo baki cikin murya shagwa6a Wanda ita kanta batasan, lokacin da ta yi ba tace ni ban iya mai armashi ba sai kanemo Wanda ya iya ya yi maka.
Habeeb ya ja iska kamar yaci yaji yana ya motsa sumar kanshi yace amma kafin ki yi min sai na tambayeki kin iya me ki ka ce"?
''Oh! tafad'a tana murgud'a baki shiru ya yi yana kallonta
Ganin yadda ya tsareta da ido yasa tace yaya Habeeb yaji ka ci ne naga kana Jan iska"?
"Oh! Shima yafad'a yana murgud'a baki
Haleesa ta kyalkyale da dariya Allah yaya Habeeb wannan murgud'a bakin yayi maka kyau kamar karuwa k'auye
"Da k'arfi ya matse mata hannuta tasaki ihu saboda ba k'aramin zafin taji ba yak'ara fisgo ta tafad'a bisa jikinsa fusk'okinsu na daf da juna yanda kowanesu yana jin bugawar numfashin d'an uwansa can! K'asan mak'oshi yace ke! Ni za ki kira da karuwa"?
No;no yaya Habeeb ni ba da kai nake ba"
"K'arya ki ke yi da ni ki ke haka ko jiya ki ka kirani da suna barawo yau kuma da sanyi safiya kin kirani da suna karuwa ko karuwa ma ta k'auye don kin rainani koh"?
"I'm sorry yaya Habeeb sa6ul da baka na yi amma bara k'ara ba tak'arasa magana cikin shagwa6a.
Janye ta ya yi daga jikinsa ya mayarda ita bisa kujera a hankali yake matsa mata jikinta, very slowly yace kin ga yaddda ake tausa mai armashi oya tashi ki yi mun da kyar Haleesa ta mik'e tsaye yayinda Habeeb ya koma ya kwanta, ba yadda Haleesa ta iya dole tadinga tausa masa jikinsa kamar yadda ya yi mata.
''Tsawon lokacin ta dauka tana masa tausa a tunaninta ya yi bacci, sakamako shirun da ya yi da kuma yadda yake sauke numfashin a hankali take sand'a da suna ta tsire karaf yarik'e mata hannun.
''Idanushi a lumshe yace ina za ki tafi ne bayan ban sallame ki ba"?
''Allah yaya Habeeb nagaji gaba d'aya hannaye na sun yi zafi
Ya mik'e zaune yana mata kallon k'asan ido ya ja iska yace kin amince na biyo ki bashi anjima za ki k'arasa mun"?
"Gyad'a kai ta yi
Ki bud'e baki ki yi min magana kinsan na tsani wannan gyad'a kan naki"?
Murmushi Haleesa ta yi tace toh....na ji amma sake mun hannu kuma katashi mu tafi ka yi breakfast har _11:15am_ ta yi tana ne had'e da nuna masa wall clock.
"Habeeb ya lumshe idanu a zuciyarsa yace in kina tare da ni Sam bana jin yunwa a baiyana kuma sai yace mu je Allah yasa ba jagwalgwale aka yi min ba.
''Wai yaya Habeeb bara ka daina zance jagwalgwale nan ba koh"? Allah zan shiga strike.
Habeeb ya ja tsaki mintsine mata fatar hannu mace bata yi min strike, ballantana ke da bakya cikin tsarina yana gama magana yasaki hannunta yafice daga falon.
Haleesa ta bi shi da harara a zuciyarta tace qarya ne wallahi, saidai in ba ka shigo hannuna ba d'an rainin wayo.
********************
```DARE```
_8:30pm_
Haleesa tana zaune a gaban dressing mirror tana fesa perfume fuskarta tasha simple make up, ta mik'e tsaye tak'arewa kanta kallo daga bisani tanufi wardrobe ta bud'e ta yi tsaye tana k'arewa kayan da ke ciki kallo.
"Ta Ciro tummy skirt sky blue colour had'e da top purple colour tana kamalla saka kayan ta zari d'an siriri veil ta yi rolling tanufi part d'in Habeeb ta tura k'ofar falon tashiga baya cikin falon sai kawai ta nemi kujera ta hakince, ta kama buga game a wayarta.
''K'amshin intense men da tashak'a ya bata tabbacin Habeeb yashigo falon tad'ago dara-dara idanunta tasauke su akansa yana sanye da T-shirt blue colour da white colour crazy Jeans sumar kanshi tasha gyara sai kyali take k'asumba da ta cika masa fuska ta d'an kawowa ainihin kyausa cikass.....Haleesa na kyalla ido akan guiwar wandonsa taganshi a yagalgale ta waro ido had'e da dafe baki sai kace ta ga abun tsoro.
"tace yaya Habeeb bera ya yi maka tsiya ya cinye ma guiwar wando tak'arasa magana had'e da tintsirewa da dariya bakin rai Haleesa take kwasan dariya har da fad'owa daga kan kujera ta mik'e k'afafunta ita a dole ta ga abun dariya yayinda Habeeb Lamido ya yi tsaye hannayenshi zube cikin ajihun wandonsa yana kallonta cike da sha'awa saboda dariyarta ta yi mugun burgeshi.
"Ya yi murmushi ya shure k'afafunta ke dallah tashi villager kawai ni narasa wance irin k'addara ce tafad'o min na aure k'atuwar bak'auya irinki in ban da tsabar duhun kai irin naki ta ina ki ke tsanmani bera zai shigo gidanan da har zai cinye min wando"?
"Haleesa ta mik'e tsaye ta galla masa harara dallah! Malam dakata jiya ba yau ba karka kuskure kace za ka yi min yankar k'iri domin ba shiru zan yi ba a da ka ke da ikon wulaqanta ni na kyalle shima ba don ina tsoronka ba sai don biyayyar aure amma a yanzu ina mai maka albishir da cewa kan magge ya waye kana fad'a mun maganar banza nima ta wofi zan fad'a ma
yadda ka ke kuka k'addara ce ta had'a ka aure da ni nima haka nake kuka, kuma har abada bara daina zubar da hawaye nadamar aurenka da na yi tana k'arasa magana tajuya har ta Kai k'ofa tajuyo tace in ka ga dama ka zo ka cin abinci in kuma bara ka iya ba kaita tsayuwa har abusa 'kaho ba abunda yadame ni tak'arasa fita tabar Habeeb Lamido tsaye sake da baki tsananin mamakinta yahana shi motsawa.......

Jeeddah Aliyu🌹

[11:19PM, 01/12/2016] Hafsat Yau Abdullahi: [01/12 7:37 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```
Chapter 65 · 0% Book details