← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 95

Sashe 45

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

~~Hannunta na rawa ta rik'e handle sai ta yi niyar ta bud'e k'ofar sai kuma tafasa yayin da gabanta yacigaba da fad'uwa, tak'ark'arewa ta yi ta danne numfashinta ta yi ta maza ta murd'a handle d'in kutt...sautin da k'ofar ta bayar kenan ta wangale saura kiris numfashinta ya fita daga gangar jikinta sakamako hango Habeeb Lamido ta yi yafito daga bathroom yana sanye da bathrobe yana goge sumar kanshi da d'an 'karamin towel Haleesa ta yi mugun tsorata da ganinshi domin bata yi zato yana cikin d'akin ta juya da sauri da nufi ta koma inda tafito har ta riko handle ta bud'e k'ofa, yadaka mata tsawa ke! Ta tsaya chak saboda tsabar tsoro numfashinta yafara Kara kaini, ke! Ba magana nake da ke ba ne"? Yafad'a azafafe a hankali Haleesa tajuyo ta dube shi, ta yi narai-narai da idanu kamar za ta fashe da kuka ta d'an rusuna cikin rawar murya tace _ina...kwana...yaya Habeeb"?_ Tagwaye harara ya watsa mata had'e da 'yar k'aramar tsoki, a dak'ile yace da ban kwana ba kya ganni meye dalilinki na dako samako ki shigo min bedroom batare da izzini na ba"? "Ka yi hankuri Dan Allah da ma na zo ne nayi maka gyaran d'akin kamar yadda ka umurce ni, duk magana da ke yi kanta na sunkuye a k'asa bata yarda sun had'a ido ba tabe baki ya yi amma shine don wulak'anci kina ganina za ki koma kina nufi tun da ina ciki bara ki gyara ba koh"? Ba haka bane yaya Habeeb na ga kafito daga wanka kana buk'atar "privacy shiyasa zan koma in kama abunda ka ke yi sai na shigo kallon k'asan ido yake mata ya ja iska kamar yaci yaji gaban Haleesa yafad'i a zuciyata tace kai Habeeb Lamido mugun shu'umi ne dube yadda yake ja iska sai kace d'an air ya lashe lips d'inshi batare da yatanka mata ba yanufi "dressing mirror d'auki robar mai yasoma shafawa yayin da Haleesa tacigaba da tsayuwa Imaan da ke kwance akan bed tana sharar bacci ta falka "Daddy na tashi 'Yar k'aramar muryarta ce tadawo da tunani Haleesa ta juya tana kallonta, Habeeb ya dire robar mai yanufi wurinta yad'aga ta sama "Morning my angel kintashi lafiya"? Imaan ta wangale d'an k'aramin bakinta tana dariya Haleesa ta tsura musu ido sunyi matuk'ar bata sha'awa ya bata peck a kumatu mu je ki yi brush na yi miki wanka da sauri Haleesa ta tari numfashinsa ta hanyar cewa yaya Habeeb kawota na yi mata yatsine fuska ya yi bar shi kawai yafad'a adak'ile ta girgiza kai wannan aikina ne zai fi kyau ka barni nayi mata ya tabe baki yadire Imaan k'asa yajuya yacigaba da abunda yakeyi Haleesa ta sunkuya tadauki imaan tanufi bathroom da ita tana jefa k'afarta a bathroom d'in ta yi turus mamaki ya baiyana akan fuskarta tasaki baki da hanci tana kallon tsarin bathroom d'in babban abunda ya yi mugun bata mamaki bai wuce gani katuwar plasma manne a jikin bango takara yadda ganinta akan stool na farin glass madauke da tarin news paper da magazines ikon Allah lallai in baka mutu ba kasha kallo wannan, ae dabi'ar nasara ce ko miye abun sha'awa da burgewa da har Habeeb zai dinga koyi da su d'ayan 6angare zuciyata yace Haleesa kenan kinmanta da Habeeb half caste ne {ruwa biyu}, ta tabe baki tanufi bathtub ta tara ruwa ta darje imaan tass wurin wanke fuska ne suka fara artabo Imaan ta yi tsaye kai da fata bataso a wanke mata fuska cikin sigar rarrashi Haleesa tace haba! Imaan ki bari na wanke miki fuskarki kinga da hannu zan wanke miki ba da soso ba" Imaan ta mak'e kafada banaso ni ki kyalle ni Haleesa ta zare mata ido tace Allah ba ki isa ba sai na wanke miki fuska, ta goga sabulu a hannunta tana murzawa akan fuskar Imaan ta kwala d'an uban ihu za ka yi tsanmani idanuta ne Haleesa ta kwakwale "Wayyo Daddy ido na wayyo za ta cire min ido"! Habeeb da ke tsaye yana rufe bottoms d'in rigarshi jin ihun Imaan yakarade gida yasa cikin hamzari yanufi bathroom, d'in _ke! Menene"?_ _Me ki ka yi mata ne"?_ A tsorace Haleesa tad'ago ta dube k'ofa inda Habeeb yake tsaye cikin sark'ewa halshe tace wai bataso na wanke Mata fuska "Habeeb ya ja tsoki yace Imaan ki bari aunty ta wanke miki fuska miye amfani wanka ba'a wanke fuska ba Imaan ta turo baki yayin da Habeeb yajuya yafita Haleesa tadauko towel karamin ta rufa mata koda Haleesa tafito Habeeb yafice daga d'akin bayan ta Shafa mata mai tace imaan je ki tambayo Daddy ina ya ajiye kayanki, Imaan tace aunty nasan Inda ya ajiye ta bud'e wardrobe tasoma kacaniya janyo wata k'atuwa Leda Haleesa ta dakatarda ita ta hanyar cewa bara na dauko miki ta bud'e Leda kayan sawa ne birjik Imaan ta yi karaf tace aunty jiya "Daddy yasiyo min su yace nadawo gidanan da zama zai dinga siya mini chocolate da ice cream kuma ya......dariya da Haleesa ta yi ne ya katsiwa imaan surutu ta Haleesa ta tsagaita da dariya da ta ke yi tariko hannun Imaan uhm....Imaan sarki surutu irin wannan zuba ba "comma balle full stop Imaan ta washe hak'ora aunty miye comma da full stop"? Dariya Haleesa ta yi tace zan fad'a miki amma ba yanzu ki zo nasaka miki kaya ki je ki yi "breakfast ta Ciro wando Jean's blue had'e da White top mai Zane teddy bear kayan sunyi matuk'ar kar6a Imaan Haleesa tace oya ki je parlour ganinan zuwa kinji"? Imaan tad'aga kai tafice da d'an gudunta "A hankali Haleesa ta bi room d'in da kallo idanuta suka sauka bisa bedside a hankali ta taka zuwa wurin ta mik'a hannun tad'auki d'an k'aramin frame mai d'auke da photo Habeeb da salma suna manne da juna ga annuri shinfid'e akan fuskoki su Haleesa batasan lokacin da ta tsintsire da dariya a zuciyata tace kalli wannan luk'ek'iya mata ace ita ce matar Habeeb da ganinta za ta girme mishi, wannan shi ake kira to match takara kyalkyalewa da dariya da sauri ta rufe bakinta ta dube bakin k'ofa daga bisani tafara wurwurga idanuta kamar tana neman wani abu a sannu ta ajiye frame d'in tafara karkade bed ta tattara kayan da yacire ta zuba a laundering basket nan take ta gyara d'akin ya yi fass ta fesa air freshener masu k'amshi gaske tanufi bathroom ta wanke shi tass duk ta bi ta jek'a k'asan, rigarta a hakan tafito kaitsaye ta doshe downstairs parlour Habeeb da Imaan na zaune a 2 sitter Imaan na ta fama zuba masa, surutu yayin da shi kuma yake zabga murmushi, a zuciya Haleesa tace uba kurma 'ya parrot ta tabe baki da sallama takarasa shiga parlour ta zauna a 1 sitter da ke facing d'in Habeeb ta talabe kumatu ta da hannunta na dama ta sukunyarda kai kallon k'asan ido Habeeb ya watsa mata ya yatsine fuska peter yashigo parlour ya dan rankwafa cikin girmamawa yace "Boss breakfast is ready" Chan k'asan mak'oshi ya amsa masa "okay yarik'o hannun Imaan suka nufi dining area peter ya yi musu serving dai-dai lokacin da Bala P.A yashigo fuskarshi d'auke da murmushi yace _ina kwana amaryar boss"?_ Haleesa ta yi dumm" takasa amsawa gani haka yasa Bala ya yi murmushi yanufi dining area _Good morning Boss_ Bala yafad'a had'e da Jan kujera ya zauna kallon banza Habeeb ya yi masa yacigaba da cin abinci shi Bala yace Imaan ba gaisuwa"? Imaan ta turo baki had'e da cewa nayi fad'a da kai tun da ka k'i siya mini goriba, Bala ya kyalkyale da dariya kai Imaan har yanzu baki manta da zance goriba nan ba"? Imaan tad'aga kai "To shikenan zan nemo duk inda goriba yake na siyo miki Habeeb ya mik'e yanufi parlour har yanzu Haleesa na zaune idan yabarta, ya zauna had'e da murtuk'e fuska a wulaqance yace ke! A nutse tad'ago ta amsa da na'am" Saida yadauki tsawon dak'ik'a uku yana mata kallon da ta tsana, ki je bedroom d'ina a cikin bedside drawer akwai file's ki dauko min kiyi sauri Karki bata min lokacin. "Haleesa ta mik'e tanufi stairs Habeeb ya rakata da ido sai lokacin idanunshi suka hasko masa rabin zip d'in rigarta a bud'e har yana iya hango brown colour bra d'inta ga wani dingo bak'i a bayanta{Mole} cike da takaici ya girgiza kai tuni Haleesa ta yi nisa domin har takai last stairs ya ja tsoki yadauke kanshi kamar Wanda aka mitsina ya mik'e da k'arfi ya haura stairs Haleesa na shiga d'akin tafara bubbud'e bedside drawers gaba d'aya ta duba a tafarko ba komai a ciki ta nufi gudan d'ayan wance ke d'auke da frame akai tana bud'ewa taci karo da tarin file's tana daukowa Habeeb na murd'a handle yashigo ya jigina jikinsa a jikin k'ofa ya hard'e hannaye shi a k'irji a firgice Haleesa ta dube shi ta ware idanu ta tsanani tsoro ya lullu6e ta, zuciyata tasoma yi mata wasi-wasi me yashigo da Habeeb"? Ko dai wani tuggu ne ya had'a mata"? Kafin ta lalla6o amsa tambayoyinta Habeeb ya yi mata alama da yatsanshi ta zo tak'ara rud'ewa 'yan hanjinta suka hautsine takasa bin umurninshi ganin haka yasa yafara dunfaro ta a tsorace tafara ja da baya yayin da Habeeb bai fasa tunk'ara ta jin ta yi karo da bango yasa tagano ba bu saura wurin gudu, kawai ta sadakat hannunshi yasa a bayanta yadafa bango ya rankwafa dai-dai bakinta da sauri Haleesa ta runtsi idanuta a tunani ta Habeeb sumbata ta zai yi hakan yasa jikinta yadauki rawa, ke! Banaso iskanci bud'e idanuki yak'arasa magana cikin d'aga murya ba bu shiri Haleesa ta bud'e idanuta ya dank'ara mata uwar harara nasan kwakwalwa ki yabaki cewa zan sumbace ki, in har tunaninki yabaki hakan kin yi kuskure, domin da na sumbace wannan bakin naki gwara na sumbace bakin akuya yak'arasa magana yana Shafa lips d'inta da yatsanshi ya ja iska a bakinshi jikin Haleesa yacigaba da rawa kidaina wannan karkarwa da ki ke yi ni tambaya ki zan yi Haleesa tad'ago idanu ta fuskarta shinfide da mamaki, wance irin tambaya ce Habeeb Lamido zai yi mata da har sai ya matsita a jikin bango _Miye dalilinki na barin
Chapter 45 · 0% Book details