← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 95

Sashe 40

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai misali k'arfe 9:00pm Habeeb yadawo yana sa6e da Imaan a kafad'arsa ta yi bacci, yana shigowa parlour Haleesa ta mik'e da sauri tanufi wurinshi sannu da zuwa yaya Habeeb Imaan ta yi bacci ne"?
Kallon sama da k'asa ya yi mata ya ja d'an siriri tsoki cikin husky voice in shi, yace ba ki ga alama bane ko ke makauniya ce"?
Murmushi ta yi ta lamgwabe kai dallah matsa ki bani wuri ki yi wani tsare da tambayoyinki na shirme Allah ya ba ka hankuri kawo ta na kaita bedroom kamar ba zai mik'a ta ba saida ya yi mata kallon da ta tsana sannan ya mik'a mata Imaan garin amsa ta hannushi ya goge k'irjinta saura kiris Haleesa tasaki Imaan cikin zafin nama yarik'e Imaan jikin Haleesa yadauki rawa sai fama zarar ido take wani mugun kallo ya watsa mata had'e da daka mata tsawa ke! Wance irin mahaukaciya ce"?
Don kawai hannuna ya goge k'irjinki shine za ki sake min yarinya Allah yaso ki da tafad'i Allah da sai na 6arar da ke Humm! Haleesa tasauke ajiyar zuciya cikin tsanani jin kunya tasada Kai k'asa ya ja tsoki ya ra6a gefenta ya haura upstairs bedroom in shi ya wuce da Imaan ya shinfid'e ta had'e da sauya mata kayan jikinta zuwa sleeping dress ya kwa6e kayan jikinshi yadaura "bathrobe towelling yanufi bathroom yacika bathtub da ruwa masu dumi-dumi ya zuba bath perfumes masu k'amshin gaske ya yi kwance cikin bathtub ya d'auke remote control ya yi switch on in TV ya murd'o BBC channel ya murza liquid soap mai k'amshin "guava fruit a skin in shi saida ya share "20 minutes yana wanka sai kace zai sauya skin colouring d'inshi daga bisani yafito daga bathroom d'in ya yada zango a gaban dreesing mirror ya shafe jikinshi da lotion ya bi lungun da sak'o na jikinshi da perfumes yasaka pajamas sky blue colour ya fice zuwa downstairs parlour Haleesa na zaune ta rafka tagumi kallo d'aya ya yi mata yadauke kai yanufi dining area Haleesa tad'ago ta sace kallonshi ta tabe baki ga ni zai yi serving in kai shi yasa ta tuna da nasiha da baffa da Ammi suka yi mata akan ta bi Habeeb lamido sau da 'kafa domin aljannata tana k'ark'ashi k'afarshi bai kamata furuci shi yayi tasiri akanta tak'i yi masa biyayya da sauri ta mik'e tanufi dining area har ya yi nufi ya bud'e warmers kamar daga sama ya ga hannun Haleesa ta dafe murfi ta wani lamgwabe kai tadawo kala tausayi "please yaya Habeeb ka bani dama nasamu wannan lada kallon hadari kaji ya yi mata ya murtuk'e fuska ya janye hannunshi ke! Ban Fad'a miki a rayuwa na banaso shishigi ni za ki yi wa kilinbibi da kissa da kisisina shine don tsabar iskanci har da su saka "transparent night gown don ki ja hankalina wallahi ki yi a banza ki yi yawo nicked a gidanan ko dar bara ji ba Co's bana kallonki a matsayin mace, ki gaugauta ki bace mini da gani na tsani kallon wannan "ugly face naki duk k'ok'ari Haleesa ta yi ta danne hawaye ta ta k'asa shar hawaye suka tsiyayo akan fuskarta ke! Dallah bace min da gani banza 'yar k'auye "classless kawai da gudu Haleesa tanufi bedroom in ta tafad'a bisa bed tasaki kuka mai tsunma zuciya dama ga Haleesa da kuka banza marigayi yaya Habeeb ya riga ya sagarta ta abun d'a k'ank'ani ya isa yasaka ta kuka har da su majina ta bangare Habeeb kuwa yana gani tafice ya ja tsoki ya Ciro phone ya yi dialling number Bala P.A kai! In ka ga dama ka zo mu ci abinci bai jira amsar da Bala zai bashi ya yi "hanging up after 4-6 minutes sai ga Bala yashigo direct yanufi "dining area cikin zolaya yace "Boss na yi zato Amarya ta ture gwanati na kadaina cin abinci da ni ashe har yanzu matsayina na nan bai sauya ba yak'arasa magana yana dariya shak'iyanci Habeeb ya wani dage gira sama ya cize lips in shi yana yi wa Bala kallon k'asa ido daga bisani yace wallahi Bala ka kiyaye ni karka ga kamar bara iya firing naka kanemi ka raina mini hankali Bala yadafe baki yana dariya k'asa-kasa ya bud'e warmer ya yi musu "serving Habeeb yad'an tsakare abinci ya mik'e batare da ya dube Bala ba yace bacci nakeji zan kwanta inda ka gama ka rufe mana k'ofa "Bala yacika baki da katuwar loma pounded yam don tsabar k'arfi hali irin na shi saida ya furta abunda ke ranshi "Boss bacci tun yanzu kwata-kwata 10:08pm sai naga kamar ka yi sauri kwanciya yak'arasa magana had'e da tand'e yatsunshi wani mugun haushi yak'ara turnuk'e Habeeb rasa abunda zai ce da Bala ya ja tsoki yajuya kawai yanufi bedroom d'inshi ya gyarawa Imaan kwanciya ta ya yi pecking nata a goshi yanufi doguwar kujera kwara d'aya chal da ke cikin room d'in da alama had'e take da bed yaciro System d'inshi da ke soke a socket tana charging ya zauna a tsakiyar kujera ya langwashe k'afafu shi yasoma kallon pic's d'in motoci a wani Company motoci da ke Japan suna turo masa simple na new models na car's har 2:00 o'clock ta buga yana zaune sai fama zabga hamma yake bacci yakeji sosai ya mik'e tsaye da kyar ko rufe laptop d'insa bai yi ba yafad'a kan bed ya karato addu'a kwanciya bacci ya tofe Imaan ya dauki remote yak'ara gudun Ac al'ada Habeeb ce Sam baya iya kwanciya sai yaji sanyi Ac na ratsa k'assa jikinshi sosai, ya jawo blacket ya lullu6e su ya lumshe sexy eye's d'inshi bai d'auki "long time bacci ya yi nassara kwashe shi ta 6angare Haleesa kuma ta ci kuka ta ita kadai ba mai rarrashinta gani kuka ba zai amfane ta da komai ba ta mik'e tashiga bathroom ta daura alwala tasoma Nafilla saida ta yi raka'a 11 ta d'aga hannaye ta sama hawaye na zuba akan fuskarta tasoma kai kukanta wurin Ubangiji da baya bacci _ya Allah ina tawasali da kyawawa sunaye ka masu girma da d'aukaka Allah Kaine_ _masani sirri da ke boye da sirri da ke baiyane ya Allah ina rok'o ka idan har aure na da Habeeb Lamido akwai alkhairi a cikin sa Ya Allah kabani_ _hankuri da juriya cinye wannan jarabawa ya Allah ka tausaya mini ka cire min son marigayi yaya Habeeb a zuciyata, ka maye mini zuciyata ka mini zuciyata da son mijina_
_Ya Allah kabani iko yi biyayya a gareshi Ameen_ ta Shafa addu'ar ta mik'e had'e da linke pray mat tanufi bed ta kwanta sai kawai ta ji duk wani b'aci rai da takeji yafita bacci mai dad'i gaske ya yi awo gaba da ita.

```HABEEB```
Zaune yake akan resting chair yana shan ice cream yashak'i k'amshin turare "musk Al-ghazal, bai Sam lokacin da ya lumshe idanushi daga bisani ya bud'e su yasauke ganinshi akan pretty face d'inta sai fama zuba masa murmushi take cikin tafiya kassaita tanufi wurinshi tashige jikinshi ta lafe kamar magge Habeeb yasaki sanyayar ajiyar zuciya, chan k'asan mak'oshi sa ya kira sunanta _leesa_ shiru ta yi bata amsa ba ya daura bakinshi akan kunneta ya maimaita sunan nata ta sigar Jan suna iska bakinshi ya ratsa dodo kunnenta ba bu shiri tad'ago dara-dara idanuta ta dube shi kallon-kallon mai cike da tsan-tsan so suke yi wa junansu daga bisani leesa ta d'auke kanta had'e da kar6e roba ice cream d'in hannunshi ta ciko spoon tasaka masa a baki bai ankara ba yaji bakinta akan nashi a hankali take shan ice cream d'in da tasaka masa a baki saida tashanye shi tass sannan ta debo tasaka a nata baki ta turawa Habeeb bakinta ta lumshe idanuta ga bakinta a bud'e Habeeb ya dube ice cream d'in da ke shinfide akan halshenta ya matsa face d'inshi daf da nata ya zura bakinshi cikin nata firgigit Habeeb ya zabura ya mik'e zaune daga mafalki da yakeyi yadafe goshi zufa ya tsatsafo masa yajuya ya dube Imaan da ke ta fama sharar baccinta
"Ya sauke ajiyar zuciya yafi a kirga yasoma aikawa brain d'inshi zafafa tambayoyi _meke faruwa da ni"?_
_miyasa nake yawan mafalki yarinya nan"?_
_iya sanina bana sonta batada muhalli a zuciyata amma a duk lokacin da na kwanta bacci sai nayi mafalkinta to me hakan yake nufi"?_
Ya ja iska mai zafin gaske ya furza Haleesa tanaso ta zamewa rayuwata karan tsaye ya lumshe idanushi mafalki da ya yi yasoma yi masa shawagi sai kawai ya tsince kanshi da sakin dogon tsoki, ya shafi sumar kanshi had'e da lashe lips d'inshi wani irin haushi da tsanar Haleesa suka mamaye masa zuciya cike da takaici ya gyara zaman pillow ya kwanta.

```WASHE GARI ```

_10:00am_
Chapter 40 · 0% Book details