← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 95

Sashe 38

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

_5:00Pm_
Haleesa na zaune a parlour har zuwa lokacin Habeeb bai dawo ba Maryam da zeely suka fad'o parlour ba ko sallama sai kace tumakai Haleesa tad'ago tana musu kallon mamaki daga bisani ta sauke idanuta akan wata kyakyawa yarinya da ke rik'e da hannun Maryam da shekaru ta basu haura 5-6 yrs nan take Haleesa tagano cewa ita ce imaan domin tana kama da Habeeb "sannu Ku da zuwa bissimillah ga wurin zama Haleesa tafad'a cikin 'yar gajeriya fara'a maryam ta yi mata kallon sama da k'asa ta yi tsoki tafinciko hannun zeely suka haura upstairs suka soma zagaya gidan kowane bedroom da parlour saida suka shiga part d'in Habeeb ne kadai basu samu damar shiga saboda yana rufe Haleesa ta juya wurin imaan da ke tsaye tana kallonta ta rik'e hannunta baby ya sunanki"?
Da k'arfi imaan ta fincike hannunta ta wani 6ata fuska cikin 'yar muryarta mai cike da yarinta tace "don't touch me ni bana sonki kuma aunty Maryam tace ke ba mommy na bane ke 'yar talakawa ce gidanku na jar k'asa ne irin gidansu hajjo mai aiki tak'arasa magana had'e da murguda d'an k'aramin bakinta Haleesa tasaki baki da hanci tana kallon Imaan a hankali ta dinga ja da baya tafad'a bisa kujera da6ass ta yi zaman 'yan bori cabdijam! Ana wata ga wata lallai ina da Jan aiki a gabana Maryam da zeely suka dawo cikin parlour Maryam tace, zeely yanzu kin gansu da abunda na ke Fad'a miki"?
"Kwarai kuwa k'awata ga zahiri nagani tajuya wurin Haleesa tace ke! Figa tsiyo kaza mayu wannan wane irin talauci da zallan kwad'ayi Ku ke da shi ke da iyayyenki"?
Ace ko allura ba su kawo ki da ita duk fad'in gidanan bakida tsinke naki na kanki Maryam ta kar6e zance ta hanya cewa wallahi, wallahi sai na yi nassara raba ki da yaya Habeeb domin bai dace da 'yar talakawa irinki mai k'ashin tsiya sai na sa kin yi kuka da hawayenki, masifa da bala'i da zan haddasa miki sai sun sanya ki fita gidanan da k'afarki haka su ka cigaba da yi wa Haleesa cin mutunci da yanka k'auna Haleesa na hakince tana kallonsu daga bisani ta yi murmushi tace kun gama"? Inaso ki bud'e kunnenki da kyau Maryam ki saurare ni kin riga kin tafka babban kuskure da ki ka yi sake na shigo gidan yaya Habeeb Wannan ne ya tabbata min da cewa ke d'in bakida Sa'a a rayuwa kuma da ki ke zance kayan d'aki tsabar na nunawa duniya ni nake juya yaya Habeeb yasa na zo ni kadai batare da ko tsinke, banda ke dak'ik'iya ce Maryam ae so ba ruwanshi da kyalekyale duniya ```NI DA YAYA HABEEB ``` nan gani nan bari dukiyar uban wani 'yar talakawa ta riga ta mallake zuciya abunda ki ke so.
Ran Maryam ya yi matuk'ar sosuwa da jin furuci Haleesa sai fama huci take kamar kubunbuwa motsin shigowar Habeeb ce ta janyo hankalinsu, da gudu Imaan tanufi wurinshi "Daddy oyoyo yad'aga ta chak had'e da mannata a k'irjinshi "how you my Angel"?
Am fine "Daddy
Ya yi pecking nata a cheek ya nufi kujera da Haleesa ta ke kai ya zauna daf da ita har jikinshi yana guga nata rass! Gaban Haleesa yafad'i ta wani d'id'ice Maryam ta mak'e murya tace "sannu da zuwa yaya Habeeb
Batare da ya dube ta yace sannu ya mayarda hankalinshi wurin Haleesa yarik'o hannunta "baby ba dai fushi ki ke yi da ni"?
Tsanani tsoro ya lullu6e Haleesa tad'ago had'e da tsura masa ido shin me Habeeb Lamido yake nufi da wad'annan kalamai nashi....??

Jeeddah Aliyu🌹

[04/11 7:06 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*

```64```
Chapter 38 · 0% Book details