← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 95

Sashe 33

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ita ce ranar da aka fara gudanar da shagalin biki kamu za'a yi a gidan Aunty Juwairiyya tun daga Lagos Madam Hindu ta yo "Booking d'in Aunty funke da yaranta suka k'awata gidan Aunty Juwairiyya da "Decoration yayinda Aunty funke za ta yi wa Amarya Haleesa Makeover tun lokacin da Haleesa tashiga "bathroom da suna wanka ta rufe k'ofa tun Aunty funke tana saka ranta fitowar ta har tagaji da jira tafito daga bedroom ta nufi parlour wurin Aunty Juwairiyya ta Fad'a mata abunda ke faruwa a harzuk'e Aunty Juwairiyya tanufi bedroom d'in tadinga knocking in k'ofar had'e da kiran sunan Haleesa shiru kamar ba mai rai a ciki Haleesa da ke Zaune dirshan a tiles d'in bathroom tasaka kanta tsakiyar cinyoyinta sai faman shashekar kuka take bata tunani akwai Wanda ya isa yasaka ta ta bud'e k'ofar nan har sai sun gama shirme su, jin yadda Aunty Juwairiyya take duka k'ofa yasa Haleesa tace Aunty ki daina wahalarda kanki bara ta6a bud'e k'ofar nan har sai kun gama shagalin bikinku.
Cikin 6aci rai Aunty Juwairiyya tace a gidan uban wa Haleesa kika ta6a gani anyi kamu ba Amarya"?
"Daga yau za'a fara a kaina Haleesa tafad'a had'e da murgud'a baki...

Jeeddah Aliyu🌹
[10/24, 11:44 AM] ‪+234 813 417 9191‬: [15/10 4:53 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*

```62```

Note:- _na yi kuskure a wurin fadar sunan garin a farko labari mai karatu zai ji nace yola a wani wurin kuma zai ji nace Yobe to yola ne ba Yobe da fatar za'a gafarce ni_

_10:30am_

"Habeeb na tsaye gaban "dressing mirror yana sharce suma shi da "Comb Mus'ab ya murda handle ya shigo ta mirror ya had'a ido da Habeeb ya kyalkyale da dariya da sauri Habeeb ya had'e rai ya d'auke kai yace banaso iskanci Mus'ab hali yanzu ka fara kaini bango tun dare jiya ka ke ta fama yi min dariya shin akwai uban da baya mafalki ne da za ka sakani a gaba kana dariya, Mus'ab yak'ara kyalkyalewa da dariya har yana dukan gefen bed abunda yak'ara harzuk'a Habeeb ya jefa masa comb in hannunshi ka ga Mus'ab na rok'e ka da ka had'a "luggage in ka ka bar min gidana Mus'ab ya tsagaita da dariyar da yake yi au abin har da su kora to ba ida zan tafi ina nan tare da kai har sai Amarya ta zo''
Amma kuma kaima kana da gida sai ka je gidanka ka tare ka jira zuwan Amarya ni kan bara iya cigaba da zama da mahaukaci"
Kyalkyalewa da dariya Mus'ab sake yi yace to ae ni narasa gane tsakanin ni da kai waye mahaukaci ko ka manta kuka ka ke yi wa mace a mafalki wannan ke nuna cewa kai d'in zarare ne Mus'ab bai jira me Habeeb zai ce ba ya juya yafi ce daga d'akin yana dariya shak'iyanci Habeeb ya bi shi da kallo daga bisani ya ja tsoki kai amma yarinya nan ta gama da ni me ke shiri faruwa da ni da na ke mafalki na sadu da ita"?
Lallai sai na musgunawa yarinya nan sai ta yi danasani zuwa mini a mafalki cike da takaici ya murd'a handle yafi ce Mus'ab ya tarar akan dining table yana breakfast batare da ya dube ida yake zaune ba ya ja kujera ya zauna, chef Peter ya yi masa "saving har suka gama breakfast ba Wanda ya tankawa d'an uwanshi Habeeb ya dube ida yake zaune yadauke kai in ka ga dama katashi mu tafi Mus'ab ya yi murmushi had'e da cewa gaskiya tsarin gidanan ya burgeni matuk'a ba k'aramin more rayuwa za Ku yi kai da Amarya Haleesa wai... Ina nufi dream girl domin Haleesa bata kai matsayin da za'a more rayuwa da ita ko ba haka bane aboki na"?
Ran Habeeb yak'ara 6aci jin yake kamar ya zabgawa Mus'ab mari ya ja tsoki ya fice daga parlour Mus'ab ya Mara masa baya yana dariya har suka iso gidan Madam Hindu Mus'ab yana tsokanar Habeeb tun yana jin zafinshi har yagaji ya zuba masa na mujiya.

_8:00pm_

```HALEESA```

Duk lokacin da Haleesa ta tuna cewa saura kiris ta zama mallaki Habeeb Lamido sai ta zubar da hawaye ta yi nisa a tunani Aunty Juwairiyya tashigo Haleesa ki tashi ki je wanka Aunty funke na jiranki za ta yi miki makeover na tafiya _Dinner_ Haleesa ta kwa6e fuska wai ni Aunty dole ne sai na je dinner"?
"Dole ne Haleesa sai kin je don haka ki tashi ki je ki yi abunda na umurce ki Karki 6atawa mutane lokacin''
Haleesa ta shar6e hawaye na fahimce cewa Aunty Juwairiyya ko tausayi na bakyaji ta kare magana had'e da mik'ewa Aunty Juwairiyya ta tabe baki sai anan a gaba za ki gano alkhairi da ke cikin wannan aure"
Tun da zuciyata bataso
Ya za'a yi na fahimce akwai alkhairi a wannan aure kawai zan yi biyayya da dukkan Umarni da ki ka bani domin banida mafita bata jira jin abunda Aunty Juwairiyya za ta fad'a ba tashige "bathroom.
"Aunty Funke tsantsarawa Haleesa kwalliya wance tafi ta jiya kyau da tsaruwa Amarya Haleesa ta yi matuk'ar kyau cikin wedding gown "golden colour" da head blue colour kafarta sanye da blue hill's hannaye da k'afafuta sun sha Zane k'umshi ja da baki Haleesa ta nemi gefen bed ta zauna ta zabga tagumi gani take wannan abun kamar almara hawaye suka wanke mata fuska da sauri Aunty Funke ta rik'o hannunta haba! Haleesa me yasa bakya gajiya da kuka"?
Haleesa ta sada kai k'asa had'e da ja majina da k'arfi tana k'ok'ari danne hawayeta Aunty Juwairiyya tashigo d'akin ta yi turus ya akayi ne sarkin kuka"?
Ki sausautawa kanki Haleesa wannan kuka bara ya K'ara ki da komai ba kullum kuka abu yak'i ci yak'i cinyewa sai hawaye ki sun kare a wofi tashi mu tafi karki 6atawa mutane lokacin''
Da kyar Haleesa ta mik'e hawaye na ta ambaliya akan fuskarta Aunty Funke ta rik'e ta Haleesa ki daina kuka karki 6ata kwalliyarki kinji"?
Saida tak'ara Jan majina sannan tad'aga kai Aunty funke tayago tissue ta yi wiped in hawaye fuskarta ta k'ara Shafa mata powder sai ga fuskar Haleesa na kyalli kamar ba ita ne tagama kuka Aunty Juwairiyya ta wuce gaba Haleesa da Aunty Funke suna biye da ita har zuwa "Compound Aunty Funke ta bud'e mota kirar "Lexus 2016 model'' ta zaunar da Haleesa cikin dusashiya murya Haleesa tace Aunty bara iya tafiya ni kadai ki kira Zainab da khadeejat mu tafi tare'
"Aunty Juwairiyya ta kya6e baki tace tuni Zainab da khadeejat suka tsofa a "Hotel in da za'a yi dinner in kin je kya had'u da su Aunty Funke ta rufe mata k'ofa driver ya ja mota yayinda Aunty Juwairiyya da Aunty Funke suka shiga ta su mota had'e da marawa motar da Haleesa take baya.

```HALL```
Chapter 33 · 0% Book details