← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 95

Sashe 68

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

~~Haleesa ta yi k'ayatace murmushi ta kad'a kwayar idonta a yangance tanufi wurin Habeeb kamar za ta shige k'irjinshi, sai kawai tanufi gefen bed ta zauna tana yi masa dariya.
" Habeeb ya yi murmushi had'e da ya mutsa sumar kansa da baya-baya yafad'a bisa bed ya runtse idanunshi, lek'a fuskarshi Haleesa ta yi tana mai cigaba da dariya, cikin tsokana tace _hey Mr pretender whats is wrong"?_
Ya mirgino yadawo saitin fuskarta kallon ido cikin ido yake mata ya ja iska yace kina nufi ko yau pretending d'in ne yakawo ki d'akina"?
''Kaima kasan in bayan shi ba abunda zai kawo ni d'akinka
Cije lips d'inshi ya yi yana kallonta a yatsine da sauri ta d'auke fuskarta da barin kallonshi.
Shiru sukayi ba Wanda yak'ara tankawa d'an uwanshi Haleesa tajuya ta sace kallonshi ya yi pillow da hannayenshi idanunshi a rufe ruf kamar mai bacci, kasa d'auke fuskarta ta yi akansa tashiga nazari kyakyawa fuskarsa ta yi ajiyar zuciya a kasalance ta mik'e tanufi gefenshi ta kwanta, tana mamaki d'abi'un Habeeb bata ta6a ganin mutum mai abubuwan mamaki irinshi ba ta yi nisa a tunaninshi batansan lokacin da ya matso daf da ita sai jin ta ta yi cikin jikinshi, cikin kunnenta ya rad'a mata bai kamata ki dinga wahalarda zuciyarki da tunanina bayan gani kusa da ke yak'arasa magana had'e da hura mata iskan bakinshi a kunne.
"Da sauri ta lumshe idanu, Habeeb yak'ara matso da ita cikin jikinshi ya hard'e k'afafunshi cikin nata yasaka hannaye shi ya layyace gadon bayanta fuskokinsu na facing d'in juna duk abunda yake yi idanunshi suna rufe kasa motsi Haleesa ta yi sai fama zazzare ido kawai take yi numfashinta na fita da k'arfi, ta k'urawa Habeeb ido a zuciyata tace ina ma ace da yaya Habeeb d'inta take kwance ba da wannan arrogant d'in ba mutumi da ya furta mata cewa sha'awarta yake yi ba sonta yake ba tabbata duk ranarda ya yi nasara cima burinshi akanta zai goge babinta ne a zuciyarshi, tausayin kanta yakamata hawaye suka zubo mata saboda tuni ta fahimce cewa ta fad'a tarkon so Habeeb Lamido tacigaba da kallonshi, yayinda Habeeb bai masan tanayi ba saboda tuni bacci ya yi awo gaba da shi ta ja karan hancinshi ta lumshe idonta a haka bacci mai dad'i ya yi nasara d'auke ta.
*************************
_11:00am_
Haleesa da Habeeb na zaune a dining table suna taking breakfast cikin kulawa Habeeb ya dube Haleesa, yace k'arfe nawa flight d'insu aunty Juwairiyya zai tashi"?
Saida Haleesa ta hadiye chips d'in da take tauna tace _11:30am_ Habeeb ya gyad'a kai suna gama breakfast suka nufi parlour inda aunty Juwairiyya take jiransu su kaita airport, kafin su wuce da ita airport nasiha ta yi musu sosai basu baro airport ba saida suka ga tashin jirginsu.
"tun akan hanyar su na dawowa gida Haleesa ta daure fuska Habeeb ya dube ta ya yi murmushi yad'age gira sama yana kallonta hannunta yarik'o cikin zafin rai ta firzge hannunta, a yatsine tace aunty Juwairiyya ta tafi daga yanzu ba wani sauran pretending, the game is over.
"Habeeb yak'ara fad'ad'a murmushinsa ya wani kad'a kai batare da yace da ita uffan ba har suka isa gida Bala na yi parking
tun kafin ya bud'e mata k'ofa ta bud'ewa kanta da sauri tanufi cikin gida.
Habeeb yafito daga cikin mota ya yi mik'a ya bi Haleesa da mayen kallo a baiyane ya furta _the game is not over baby this is just the beginning_
Bala ya matso daf da shi ya yi k'asa da murya kamar munafuki yace "boss wannan wane irin game ne jikina yabani wasan zai yi dad'i kuma na tabbata Kaine winner.
"Da mugun mamaki Habeeb ya kalli Bala daga bisani yadafa kafad'arsa suka jera suna tafiya a hankali Habeeb ya ja iska yace nima ina ji a jikina ni ne winner amma basan how long wasan zai dauka kafin nayi winning.
''Bala ya washe hak'ora yace karka damu da tsawon lokacin da wasan zai dauka abu mafi mahimmancin ka yi nasara cinye wasan amma boss wannan wane irin wasa ne"? Bala yak'arasa magana yana dariya.
''Habeeb ya galla masa harara yadak'i kafad'asa yace na tsani shissshigi Bala.
Murmushi Bala ya yi yace "yes boss.
"Direct Haleesa ta wuce bedroom d'inta ta qargame k'ofa, tun daga lokacin suka koma 'yar gidan jiya za ta girka masa abinci ta jejjera akan dining table ta shigewarta d'akin ta murza key.
idan Habeeb yaga dama yaci ranar da yaji baya ra'ayi ci yabar mata kayanta a haka suka share _1 week_ suna gida d'aya amma kowanesu rayuwarsa yake yi.
_10:00pm_
Habeeb yana kwance a bedroom d'inshi abun duniya yataro ya yi masa yawa, tunanin Haleesa na azabtarda ruhinshi da yarufe ido ita yake gani, ba abunda yake buk'ata irin ya ji d'umi jikinta da sanyaye k'amshinta kamar Wanda aka mintsina da sauri yasauko daga kan bed yanufi part d'inta.
Yana murd'a handle ya ji k'ofar d'akinta a rufe ya yi tsaye kamar zai kurma ihu tsawon lokacin yadauka yana safa da marwa can! Idea tafad'o mishi da sauri yafice sai gashi yadawo rik'e da mopper da k'arfi yafara dukan kujerin parlour da mopper hannnushi yature d'an k'aramin glass madauke da flower da ke ajiye akan center table yafad'o yadak'i tiles ya tararatse.
''Haleesa na kwance har bacci yafara d'aukarta taji k'arar fashewar glass, ta zabura da k'arfi ta diro daga kan bed tanufi parlour da gudu tun kafin tak'arasa ta hango Habeeb yana watse da pillowcases na kujeri gaba d'aya ya hargitsa mata parlour a rikice tak'arasa wurinshi, muryarta na rawa tace lafiya yaya Habeeb"?
Banza yayi da ita yacigaba da watsi da kaya rik'e mai hannnu ta yi yadakatar da abunda yake yi, yana sauke numfashi, wai yaya Habeeb me ka ke nema ne duk ka bi ka rikita min parlour"?
"Habeeb ya karkace kai yafara tsara Haleesa ta hanyar cewa _ina zaune a dining area na ga wani abu mai bindi ya rugu da gudu yashigo parlournki shine na biyo shi da mopper yashige k'ark'ashin kujeri_
Zo ki ta ya ni mu fiddo shi Haleesa ta zaro ido cikin sark'ewar halshe tace ni fa ban fahimce abunda ka ke nufi ba"?
Habeeb yadafe goshi yace ina wannan abin mai tsawo yana da dogon bindi ya ma sunanshi yashiga tunani kamar da gaske karaf Haleesa tace bera
Habeeb ya yi shiru yana kallonta ya girgiza Kai yace No....ba bera bane ae bera baya cizo koh"?
''Haleesa ta gyad'a kai to ko k'adangare ne yaya Habeeb"?
Haleesa tafad'a da alama tafara tsorata shiru Habeeb yana nazari maganarta daga bisani yace k'adangare kai bashi bane domin shima baya cizo wannan abu mai tsawo jikinshi yana da tsantsi, za ki tuna suna wannan abu da na ta6a siyowa Imaan na roba a Canada har yabaki tsoro"?
tun kafin Habeeb yak'arasa magana Haleesa tadaka mahaukacin tsalle ta chukuikuye shi jikinta na rawa tace yaya...Habeeb....Maciji
Wicked smile Habeeb ya yi yace eh! Maciji ne nima na yi matuk'ar mamaki yadda aka yi yashigo parlounki.
"Haleesa tafashe da kuka tak'ara qanqame Habeeb kamar za ta shage k'irjinshi Dan Allah yaya Habeeb kafita da ni gidanan wallahi tsoro nakeji.
Kinga me ye kuma abun tsoro tun da ba'a bedroom d'inki yake ba yanzu yadda za'ayi ki shage bedroom ki qargame kamar yadda ki ka saba gobe da safe zan kira securities su fito da shi.
Cikin shashshek'ar kuka Haleesa take girgiza kai bara iya ba yaya Habeeb, zai iya shiga har bedroom ni dai ka fita da ni.
Habeeb ya fakace idonta ya yi mata gwalo yace saidai in za ki je part d'ina mu tafi amma ni basan inda zan kai ki ba.
Kuka yaci k'arfinta takasa furta komai sai faman d'aga kai ta ke yi cike da farin ciki Habeeb yadauke ta cak......da kyar ta amince yasauke ta bisa gado Habeeb ya dube fuskarta ya ga yadda ta kwa6e da hawaye had'e da majina, tausayinta ya yi mugun kamashi ya mik'a hannu bisa mirror ya yago tissue ya goge mata fuska yace kwanta ki cigaba da baccinki.
Girgiza kai ta yi ta rik'e mishi hannu gam yayi k'asa da murya ki kwanta ba abunda zai same ki bathroom zan shiga bara d'auki dogon lokacin ba zan fito kinji"?
Uhm!...uhm...ni dai mu tafi tare zaro ido Habeeb ya yi yace a ina za mu tafi"?
Bathroom tafad'a cikin murya kuka, komawa Habeeb ya yi zauna kusa da ita yace na fasa zuwa bathroom d'in saboda bara yarda ki bini ciki ki k'are min kallo.
Da sauri Haleesa ta matsa tashige cikin jikinshi, a hankali yake bubbuga bayanta har yasamu tadaina kuka ya ja mata pillow ta kwanta cike da nishad'i Habeeb ya kwanta kusa da ita ya rungumeta tsanm.
**********************
_washe gari_
Habeeb da Haleesa suna zaune a parlour Habeeb ya yi pillow da cinyoyinta, ita kuma sai faman damuk'a mishi gashi take yi idanunshi na lumshe yace ke! har yanzu ba'a gama Kitso bane"?
"Turo baki ta yi sumarka yacika tsantsi da yawa da na kitsa sai ya warware, ayya kuwa yaya Habeeb ba relaxer ka ke sakawa ba"?
Tsaki ya ja ya mintsine ta a gefen cinya angaya miki ni d'an daudu ne da zan sakawa suma na relaxer"?
Uhm..!ka ga bawan Allah maida wuk'a ni bance maka d'an dauda ba kawai dai naga kai d'an gayu ne tak'arasa, magana tana lek'on fuskarshi.
Habeeb ya yatsine fuska yace gayanci na bai kai can ba kinji koh magge"?
Tashiga ture masa kai daga cinyoyinta d'aga mun daga jiki tun bara ka daina kira na da magge ba ni dama dole ce tasani zama a part d'inka.
Ke fa ki ka ce sunanki magge"
Yaushe nace da kai sunana magge"?
Kafin yabata amsa phone d'inshi ya yi ringing Haleesa ta mik'a hannu bisa center table tadauko masa, kamar ba zai d'aga kiran ba sai da yagama Jan ajinsa sannan yad'aga _Hello Maryam ya akayi ne"?_
Rass...rass...gaban Haleesa yafad'i da ta tuna wacece Maryam a wurin Habeeb nan take wani irin kishi ya turnuk'e ta har Habeeb yagama waya batasan inda kanta yake ba saida taji yana mata tafiyar tsotsa a gefen cinyarta, buge mishi hannu tayi kamar daga sama ta ji muryarshi yana cewa Maryam ce ta kirani wai gobe za ta turo driver yad'auki Imaan ta je musu hutu.
"Ajiyar zuciya Haleesa ta yi tace uhm...
Tun daga wannan lokacin shak'uwa mai k'arfi yashiga tsakanin Habeeb da Haleesa yau Habeeb yashirya zai tafi Lagos, kuka Haleesa tasa mishi bara ta iya zama ita kadai ba saida yakira Hannah a waya ta turo masa yarinye Housemaid d'in madam Hindu ta tayata zama saboda Hannah exam take yi Haleesa tana tsaye a palour tana matsar hawaye Habeeb yafito rataye da briefcase d'inshi gani tana kuka yasa jikin Habeeb ya yi sanyi ya rungumeta yana rarrashinta kidaina kuka bara wuce _1 week_ ba zan dawo kinji"?
Yak'arasa magana had'e da d'ago fuskarta ya tsotsi lips d'inta na k'asa wani irin quncin ya ziyarce zuciyarta tana tunani yadda za ta share tsawon sati d'aya batare da Habeeb ba.
Cikin muryar kuka tace ni ban damu da kowane lokacin za ka dauka ba ka dawo ba babban damuwa na yadda za ka tafi kabarni da maciji a cikin gidanan.
Tsaki Habeeb ya ja cike da takaici yake kallonta da ya dauka kukan da take yi saboda zai tafi yabarta ne har yafara murna ita ma tafara jin abunda yakeji a game da ita shiyasa ma yake d'aga mata k'afa kafin ya ga iya gudun ruwanta, ashe ita abun ba haka bane a wurinta.
Kukan Haleesa ya tsananta Habeeb ya galla mata harara cikin zafin rai yace, maciji ya kashe ki kafin in dawo yaciro bundle na 'yan N1000 ya jefa mata bisa kujera yafice da sauri saboda jin yake yi kamar zuciyarsa za ta tarwatse.
Haleesa ta yi sororo baki sake ta bi bayanshi da kallo dama tasan har abada Habeeb Lamido bara ta6a sonta ba ko 'yar wannan shak'uwa da tashiga tsakaninsu, duk lokacin da ya bud'e bakinshi saidai yace tana burgeshi tana bashi sha'awa, ita kuma ta tsani jin wad'annan kalamai daga bakinshi saboda ta kai k'ololuwa a sonshi tak'ara fashewa da kuka ta kwasa da gudu tashige bedroom d'inshi..........
Chapter 68 · 0% Book details