← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 95

Sashe 73

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Haleesa tana kwance akan 3 seater Hannah tayi sallama tashigo a gajiye tafad'a bisa kujera washh....matar yaya Habeeb wallahi na kwaso gajiya, akwai abinci a gidanan"?
"Haleesa ta mik'e zaune ta tabe baki ki kira yarinye ta kawo miki.
Bayan Hannah tagama cin abincin ta zuge zip d'in handbag d'inta tafito da invitation card ta mik'awa Haleesa ga invitation d'in auren yaya Sageer d'a wurin Aunty Mami a Sokoto za'ayi bikin
''A kasalance Haleesa ta kar6i invitation d'in ta duba ta ajiye a gefenta, yaushe za Ku tafi ne"?
"Maybe ranar Wednesday saboda mom tace tafiyar mota za mu yi kada mutum yaje yarasa mota da zai dinga fita da shi ko za ki je ne"?
Ajiyar zuciya Haleesa tayi cikin sanyi murya tace zan je ko zan rage wannan zaman kadaici da zaman tunanin mutume da bai da mu da ni ba tak'arasa magana hawaye na zuba akan fuskarta.
"Hannah ta mik'e tadawo kusa da ita ta zauna, kina nufi har yanzu ba wani canji Haleesa ta girgiza kai cikin muryar kuka ta kwashe yadda suka yi da Habeeb tafad'awa Hannah saboda ta yarda da Hannah d'ari bisa d'ari.
''Cike da takaici Hannah ta ja tsaki narasa gane yaya Habeeb wane irin shu'umin mutum ne"? In banda wulaqancin da rainin hankali don baya sonki sha'awarki yake bai kamata yafito fili ya fad'a miki ba.
"Ae gwara da ya gayamin matsayina a zuciyarshi kinga yanzu nasan cewa jikina yakeso ba ni ba amma zahirin gaskiya Hannah d'an uwanki yayi min illah domin zuciyata tayi nisa a sonshi sai nakeji kamar banta6a son wani d'a namiji ba sai akanshi.
Hannah ta rungume Haleesa tafara rarrashinta ta hanyar furta mata kalamai masu dad'i har tayi nasara shawo kanta tadaina kuka shawara da zan baki duk lokacin da ya zo miki da buk'atarshi ki bashi had'in kai da haka za ki kama shi duk abunda yakeso ki dinga yi mishi kada ki ta6a nuna masa kema kina sonshi ki nuna masa kawai biyayyar aure ce tasa kike masa abunda yakeso koda dutse ne a k'irjinshi ba zuciya ba dole wata rana yabaki gurbi a zuciyarsa.
''yanzu Ki tashi ki had'a kayanki mutafi gidan mom tunda jibi ne tafiya domin banga amfani zaman nan da ki ke yi ba.

_8:00pm_

Madam Hindu na zaune a katafare parlournta tana waya da Habeeb tana gamawa tafara kwallawa kira Haleesa da sauri Haleesa tafito daga d'akin Hannah.
''Gani mom!
Yanzu nan nagama waya da mijinki yace mini baki fad'a masa za ki je sokoto ba don haka ki kira shi a waya kinemi izzinshi duk da nasan ba zai hanaki ba.
"A sanyaye Haleesa tajuya ta koma d'akin ta kwanta kusa da Hannah tace Hannah kinji wata sabuwa"?
"Inji 'yan caca meke faruwa ne? Hannah tafad'a had'e da kallon fuskar Haleesa.
"Wannan kiran da mom tayi Min wai tayi waya da yaya Habeeb yace da ita ban fad'a masa ba zan bi Ku sokoto ba wai na kira shi na nemi izzinishi.
''Hannah ta ja tsaki wallahi mom ita ke k'arawa yaya Habeeb girman kai me ye na wani cewa sai kin nemi izzinishi mtww...tak'ara Jan tsaki.
''Haleesa tace ni babban tashin hankalina tun lokacin da muka dawo daga Lagos na rufe wayana.
"Ki daure kawai Haleesa ki kira shi kada mom ta fahimce akwai rashin jintuwa a tsakaninku.
"Ajiyar zuciya Haleesa tayi ta mik'e tadauko wayarta ta koma ta kwanta, tajuya wajen Hannah tace Hannah, ina masifar son yayanki
"Dariya Hannah tayi tace don't worry ta hannun dama na shima insha Allah wata rana sai ya zubarda hawaye akan sonki.
"Haleesa ta girgiza kai tace kuka fa ki ka ce Hannah wannan shu'umin ne zai yi min kuka"? Ke dai bara in kira shi ki ji yadda za ta kaya a tsakaninmu gabanta na fad'uwa tayi dialling numbershi..........

Jeeddah Aliyu🌹
[10:02PM, 09/12/2016] Hafsat Yau Abdullahi: [09/12 4:55 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*

```89```

~~Wayar tayi ringing har ta tsinke bai d'aga ba Haleesa ta ja tsaki tace Hannah kinga halin yayanki koh"? Yanzu nan mom tak'are waya da shi amma ni gashi na kira shi yak'i picking.
"Yi masa uziri ki K'ara kira watakil yana ja miki class ne kinsan yayana mai tsada ne tak'arasa magana tana dariya tabe baki Haleesa tayi tace hum.....ae naga alama tak'ara danna kiran number Habeeb still har ta tsinke bai yi picking, 3 misscall Haleesa tayi mishi ranta abace ta ajiye wayar a gefenta.
"Share shi kawai anjima ki k'ara kira idan bai dauka ba ruwanshi kedai ba kinsan kin kirashi wulaqancin shine yahanashi d'auka.
"Ajiyar zuciya Haleesa tayi narasa me nayi wa yaya Habeeb ya tsaneni haka"? kwanakin da suka gabata yaya Habeeb yana bani kulawa, a koda yaushe za ki tararda mu manne da juna cikin d'an k'ank'ani lokacin yayi nasara raba zuciyata da soyayyar margayi yaya Habeeb.
''A lokacin har tunani nake ko yafara sona ne ashe, tunanina ne kawai yabani haka.
Hannnayen Haleesa Hannah tarik'o cikin sigar rarrashi tace Haleesa nasan abunda yaya Habeeb yake miki Sam baya kyautawa amma Dan Allah ki yi hak'uri ki cigaba da kai kukanki wurin Allah, sannu Allah zai kawo miki karshe wannan matsala kafin mu kwanta bacci ki daure ki k'ara kiranshi.
"Batare da Haleesa tace da Hannah komai ba ta miyar da hankalinta wurin film d'in da suke kallo.

_1 hour later_
Haleesa please ki K'ara kiran yaya Habeeb wallahi banaso mu yi tafiya nan batare da ke ba.
"Huh....Hannah kema kinsan ko na kira bara dauka ba amma tun da kin matsa bara na kira ta call had'e da k'ara wayar a kunne.

```JAPAN```
Chapter 73 · 0% Book details