← Book details Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 95

Sashe 66

Nida Yaya Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*

```82```

~~Tsawon lokacin Habeeb yadauka a tsaye ya kad'a kai yanufi part d'in Haleesa tana zaune a parlour yashigo ko kallonta bai yi ba ya ratsa ta gefenta yanufi dining table, ya zauna ya dube inda Haleesa take zaune yace ke! Magge zo ki yi min serving.
"Da sauri Haleesa tajuya saboda maganarshi ta yi mugun bata mamaki a tunaninta da yafito sai ya yi mata wulaqancin da yasaba, sai kawai taci karo da sa6anin tunaninta.
A fusace yak'ara cewa
"Ke ko bakyaji ne"?
Ta mik'e tsaye da sauri tanufi wurinshi fuskarta a daure ta zari plate ta yi serving d'inshi ta ajiye a gabansa.
Duk abunda take Habeeb yana kallonta yarik'on hannunta yana murzawa idaunshi na akan fuskarta, ita ma shi take kallo ya lumsashe idanunshi can! K'asan mak'oshi yace ke ni za ki yi wa rashin kunya koh"?
''Turo baki ta yi had'e da d'auke fuskarta tajuya tana kallon TV da ke manne a bangon dining area.
"A yatsine Habeeb yace wai ke wannan daure fuska na menene ni ban daure miki fuska ba sai ke ce za ki daure Min"?
"Haleesa tafisge hannunta daga rik'on da ya yi mata kacin abincin ka kada ya sanyi.
Batare da yace da ita komai ba yafara cin abincin Haleesa ta zagayo ta zauna a kujera da ke facing d'inshi, bai wuce cin spoon hudu zuwa biyar ba ya ture plate.
''Haleesa ta tabe baki tace kana nufi ka k'oshi kenan"?
"Ba ki ga alama bane ko ke makauniya ce"?
Shiru Haleesa ta yi tana kallonshi, shima ita yake kallo tsawon _4 minutes_ suka dauka suna kallon junansu, yayinda kwayar idanuwansu take isa ma zuciyoyinsu da sak'o Haleesa ce tafara d'auke idanunta daga kanshi ta mik'e tsaye.
Habeeb ya ja iska yana murza saman goshinsa, kamar Wanda aka mintsina ya mik'e da sauri lokacin har Haleesa takai cikin parlour yana zuwa ya ja birki a gabanta.
"Haleesa ta d'an tsorata da ganinsa a rikice ta furta kana buk'ata wani abu ne yaya Habeeb"?
Hannunta ya rik'o ya matse gam... Cikin nashi da k'arfi ya fizgota ta fad'o k'irjinsa yafara romance d'inta yana sauke numfashi da sauri-sauri, gaba d'aya Haleesa ta rikice tsigar jikinta ta tashi Yarr...tafara k'ok'arin kwacewa cikin kunnenta ya rad'a mata _sha'awarki ta yi min munmuna kamu tun ina 6oyewa har na kai faggen da bara iya jurewa ki taimaka min pls_
"Idanun Haleesa suka ciko da hawaye haushin Habeeb ya turnuke ta, yana nufi ba sonta yake yi ba sha'awarta yake yi da ya samu abunda yakeso zai cigaba da wulaqantata wani irin k'unci ya ziyarce zuciyarta ta runtse idanunta sai ga hawaye na bin kuncinta, bata ankara ba taji Habeeb ya had'e bakinshi da nata, jin ta yi k'afafunta sun kasa daukarta tasoma k'ok'arin zubewa k'asa ya rik'enta sosai.
"Can ya dauketa yanufi part d'inshi direct bedroom yawuce da ita, Haleesa tadawo kamar idol{gunki} ko kwakwaran motsi takasa tana kallon Habeeb yacire rigar jikinsa, gadan-gadan yanufo ta.
"Sai lokacin brain d'inta yafara aiki zuciyarta tafara sak'a mata wasi-wasi karki sake ki mallakawa Habeeb kanki da ya biya buk'atarsa, zai cigaba da wulaqanta ki ne da bakinsa yace sha'awarki yake yi sha'awa kuma ba so bane da sauri Haleesa tafara ja da baya tana girgiza kai.
Kai wane yaya irin mugu ne yaya Habeeb"?
Yanzu kai ko kunya bakaji ka dube tsabar idona kace kana sha'awata, wallahi ko za ka mutu bara ta6a Mallaka maka kaina, har sai ka bani matsayin a zuciyarka.
Kunya ta lullu6e Habeeb a sanyaye yadauki rigarsa yajuya da sauri yafice daga d'akin.
Haleesa ta kifa kanta akan pillow tafashe da kuka, zuciyarta na mata zafi, me yasa Habeeb bara iya furta mini kalma so sai ta sha'awa wannan wance irin k'addara ce tafad'a min mijina na aure babu sona a zuciyarsa sai sha'awa wannan wane irin rayuwa ne na riski kaina a ciki"?
"A parlour Habeeb ya tsaya yasaka rigarsa yadauki phone's d'inshi da ke zube akan center table yafice tun kafin yak'arasa compound yake kwadawa Bala kira da a tsorace Bala yadanno da gudu.
"lafiya Boss na ga kamar ranka a 6ace"?
Tsaki ya ja cike da jin haushin yace wannan ba matsalarka bace mu je ka kaini ademola adetakumbo street ayi min aski nagaji da wannan k'asumba yana magana ne had'e da tafiya.
"Wannan gaskiya ne boss k'asumba nan ta yi mugun rage maka kyau
Bala yafad'a cikin 'yar dariya.
"Habeeb ya tabe baki had'e da yatsine fuska Bala ya bud'e masa k'ofar mota yashiga, Bala ya ja motar gate man yabud'e musu gate suka fice.
" lokacin-lokacin Habeeb yake Jan tsaki ya yi danasani furtawa Haleesa abunda ke ranshi, shikenan yanzu za ta renashi, har da wani cewa sai na taba matsayi a zuciyata, in banda k'arancin shekaru irin nata akwai wani matsayi da zan bata da yawuce, wannan yaushe nake da lokacin zama na dinga furtawa mace kalaman soyayya, iya tsawon rayuwar da na yi da aunty salma banta6a furta mata wata kalma da ta dangancin soyayya, iya Sanina ina matuk'ar tausayin aunty salma Wanda hakan ne yajanyo mata babban matsayi a zuciyata, to ita wannan yarinya me yasa bara ta amince mu yi rayuwarmu a haka"?
"Yak'ara Jan tsaki yacigaba da zance zuci banta6a sanin me ye so ba kuma bana tunani akwai wata 'ya mace da zan so.
"Boss mun k'araso maganar Bala ce tadawo da shi natsuwarsa a sanyaye yafito daga cikin mota.
************************
_2 day's later_
Chapter 66 · 0% Book details