← Book details Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 85

Sashe 84

Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ogah Junaid yana kwance ya ɗora Khubayr a saman ƙirjinsa sai bacci yaketa sha, ta gefen hannunsa kuma Amriish ce take kwance akan Damtsensa itama sai bacci taketa sha, ta ɓangaren ɗayan hannunsa ta dama kuma Angel ce itama tana kwance akan hannunsa tana shan bacci, Areeph kuma yana can gefen gado shima baccin yake yi,
Banda shi Ogan wanda idonsa biyu yana kallon ceilling fuskar Ayush kawai yake gani, har yanzu yana cikin wannan damuwar na kewar Matarsa,
yana cikin wannan tunanin yaji an turo ƙofar ɗakin Mommy ce ta shugo da sallama a bakinta tana murmushi saboda kusan kullum a haka take samun su, da kular abinci a hannunta,
ta ajiye akan table tana faÉ—in "toh Sarkin thinking kai baka bacci koh?..."
Murmushi yayi sannan yace "Hmmm! Mommy kenam .."
ta zauna a bakin gadon itama tana bin yaran da kallo tace "ka sabar wa yaran nan zama guri É—aya, basa wasa sannan basa zuwa makaranta why?..."
Yace "Mom it's not my fault, har yanzu akwai damuwar rashin mahaifiyarsu acikin zukatansu, na rasa yanda zanyi na cire musu, idan na matsa a kusa dasu gani sukeyi kamar nima zan tafi na barsu ne kamar yanda suke tunanin Mommynsu ta tafi ta barsu..."

Mommy tace "a hankali zakana cire musu abun a ransu, yanzu tsawon shekara biyu amma har yanzu basu daina kewar nan ba? waɗannan wasu irin yara ne haka, yanzu suke da shekara shida fah, gashi har sun koyawa ƙaramin ƙaninsu zaman kewar, yakamata suje su haɗu dasu Ummulkhairy da Abul suna yin wasa tare kuma su rinƙa zuwa school, kar ka sakalta su da haka .."
Ajiyar zuciya Junaid yayi yace "toh yazanyi especially Mamana duk ta fisu ɗankwara ganinta koda yaushe ajikina ne yasa suma suka biye mata, ina tsoron tashin ciwonta, inda ace Yushert tana nan da duk hakan bata faru ba, amma zanyi iya ƙoƙari na naga sunje school sannan duk zasu koma ɗakunan su da kwana...."
Mommy tace "toh kai kuma fah? Kaima ai kamar yaran haka kake kaƙi komawa gurin aikinka..."
Yace "saboda yaran ne yasa bana zuwa..."

Mommy ta É—anyi shuru kaÉ—an daga baya tace "Amm daman inaso zanyi magana dakai..."
Ogah Junaid cike da mamaki yace "ina jinki Mommy...'
Tace "daman maganar akan Aurenka ne, bai kamata ace kana zaune haka ba mata ba, idan kayi Auren suma yaran zasu fi jin daÉ—in kasancewa cikin nishaÉ—i..."
Junaid haka yake jin kalaman mommy a baibai cikin rashin fahimta yace "Aure kuma? da wa?..."
Mommy tace "mun zauna mun tattauna da Baffanunka akwai wacce zamu haɗaka da ita, Balarabiya ce ƴar ƙasar Makkah, tanada kyakykyawar zuciya, kuma zata riƙe maka yara tamkar mahaifiyarsu, idan har kaji halayenta da tarbiyarta zakaso kasancewa tareda ita a matsayin matarka, yaranka zasu ji daɗin kasancewa da ita domin ita ɗin uwar ƴaƴa ce tanada son yara sosai da sosai, ka yadda dani my son kasan bazan zaɓa maka abunda zai cutar dakai ba..."

Ogah Junaid jinjina kai yayi shi ya rigada ya tsara cewa bazaiyi Aure ba, zai tsaya ne ya kula da yaransa....
Yana cikin wannan tunanin yaji mommy ta katse shi da cewa "na roƙe ka my son ka amince dan Allah, ina neman alfarmanka..."
Kallon mommy yayi tareda haɗiyar yawu yace "shikenam Mom, babu abunda zaki roƙeni akan nayi shi banyi ba, domin kin wuce haka acikin zuciyata! duk abunda kika tsara dai dai ne saboda haka na Amince, indai kin yadda da tarbiyarta nima na yadda..."
Murmushi mommy tayi tana hamdala cike da farin ciki tace "Nagode sosai Yarona, Allah Ubangiji ya maka Albarka, Allah ya ƙara maka haƙuri da juriya, Allah ya ƙara buɗa maka ƙofofin Alkhairi..."
Junaid ba ƙaramin jin daɗi yayi da waɗannan addu'o'in mommy ba, shima yayj murmushi yace "Nagode Mom, Allah yabar mun ke..."
ta Amsa da Ameen sannan ta sanar masa cewa "Gobe insha Allahu su Baffanunka zasu je su ɗauro maka Aure acan ƙasar Makkah..."
Zaro ido Junaid yayi sannan yace. "Mom da sauri haka?..."
Tace "kai baka saniba har an gama komai yanzu Aure ne ya rage, inada yaƙini zaka amince shiyasa tinda ban sanar maka ba..."
Murmushi kawai yayi ba tareda yace komai ba,
Mommy ta fice a É—akin cike da murna...

Bayan fitar ta kwantar da kansa yayi akan pillow kansa na kallon ceilling shi yasan irin damuwar da yake ciki na rashin Ayush......

Washe Gari su Uncle Artaff da Sarki Raamud sun shirya tsab zasu tafi Makkah,
Ga jirgi na jiransu haka suka tafi,
Junaid yana tareda yaransa bai ma san sun tafi ba saboda bai saka abun aransa ba, mommy haka tasa Æ´an aiki suka gyaggyara ko ina na gidan, part É—in Ogah Junaid an gyara wuri yayi kyau sosai,
A wannan lokacin a falo suke zaune suna kallo Angel tace "Daddy ya naga duk an gyara gidan, waye zai zo?.."
Junaid yayi murmushi sannan yace "Aunty za'a kawo muku gidan..."
Angel tace "Aunty kuma aina?..."
Yace "Aunty za'a kawo muku wacce zatana kula da ku.."
Angel kamar zatayi kuka tace "kenam Mommyn mu bazata dawo ba har abada?...". Junaid jiki ba ƙwari haka yake kaɗa mata kai.

Amriish tace "mommy ta gudu ta bar mu, ta guje mu, bata son mu, nima yanzu na daina damuwa da ita inaso a kawo mana wata Aunty wacce zatana kula damu, kuma zata zauna a matsayin Mommyn mu..."

Ogah Junaid yana kallon Amriish cikin tausayawa yace "Mommyn ku bata guje ku ba..."
Kafin ya ƙarasa maganar Areeph ya katse shi da cewa "mommy fah mutuwa tayi.."
Junaid cike da mamaki yake bin Areeph da kallo daƙer yake motsi da lips ɗinsa waran cewa "waya gaya maka cewa Mommynku ta mutu?..."
Areeph yace "na daɗe dajin labarin nan a wajen su Mamy....." kafin ya rufe bakinsa Amrish ta cabki wuyansa tana kuka tana faɗin "wallahi mommy bata mutu ba, ƙarya kake yi mommyna bata mutu baa.." nan suka fara kokuwa tsakanin Areeph da Amrish Ogah Junaid ganin Areeph ya ware hannunsa zai zabga mata mari yasa yayi saurin riƙe masa hannu tareda rabasu kowa yaja shi gefe, gaba ɗaya ya rasa mai zaice mAh,
Ita kuwa Angel fashewa tayi da kuka jin ance Mommynsu ta mutu,...
Daƙer ya rarrashe su sannan yaja su suka nufi bedroom.....

Su Sarki Raamud basu tashi dawowa ba sai washe gari suka tafo da Amarya tareda wasu matan waɗanda suka yo rakiya, ana kawo Amarya aka wuce da ita part ɗin Angonta wanda yasha tsaruwa sai ƙamshin turare ne yake faman tashi,
Shima Ogah Junaid yasha Gizner abunsa ba ƙaramin kyau yayi ba, sannan Angel da Amrish suma an haɗesu da dogwayen riguna na kanti masu kyan gaske da tsada kayansu iri ɗaya, shima Areeph da Khubayr sunsha Gizner irin na Daddynsu, sun sha kyau sosai kamar ƴan indiyawa kodama asalin ƴan India ne...

Misalin ƙarfe 10 na dare Ogah Junaid yana zaune a falo shida Yara suna kallon Film saiga Mommy ta shugo da flask a hannunta tana ganin Junaid ta tsaya tana kallonsa gira a haɗe,
Junaid yana ganin mommy a haka yayi murmushi yace "Mom what's wrong?..."
Tace "haba My Son yanzu fisabilillah hakan ya dace kenam!?.."
Yace "me kuma nayi?..."
Tace "meyasa kabar Amarya ita kaÉ—ai acan room É—inka baka je ka ganota ba?..."
Murmushi yayi sannan yace "Mom zanje so nake sai yaran sunyi bacci ."
Tace "a'ah basu ga Auntyn nasun ba zasuyi bacci?..."
Angel tace "Daddy nikam zanje naga Auntyn namun..." Itama Amrish tace "nima zanje naga Auntyn mu wacce zata zamo Mommyn mu.."
Mommy tana tsaye sai Dariya take tayi tace "toh shikenam kuje room É—in Daddynku tana can, kuje kuce mata ta fito kuci Abinci...". Suka amsa da toh suna tsalle suka haura upstairs...
Shikam Areeph ƙin zuwa yayi yana tsaye sai faman haɗe rai yake tayi, shi daman baiyi murnar Auren ba, mommy ce ta fahimci Areeph yana cikin ɓacin rai tace "Angona lafiya kuwa meyasa bazaka je gurin Aunty ba?...".
ya kawar da kai gefe tareda faÉ—in. "Ni indai ba mommy nah bace bana sonta, kuma naji kunce mommyna ta mutu..."
Gaba É—aya jikinsu ne yayi sanyi daga mommy har Ogah Junaid, duk suka kasa cewa komai, ga Khubayr a cinyar Daddynsa sai tsotsar babbar yatsarsa yake idonsa akan TV dake yaro ne bai san me ake tattaunawa akai ba, kuma shi baiyo wayon yayunsa ba, saboda shi har yanzu Khubayr bai iya magana ba, su kuma triplets tin suna yashi suka fara magana...

Suna cikin wannan halin saiga Amriish ta sauƙo down tana kuka Mommy tace "takwara meya faru ne?..."
Tana kuka tana faɗin "wannan Auntyn namun taƙi buɗe fuskarta mu ganta kuma taƙi zuwa muci abinci..."
Mommy tace "a'ah kuyi mata uzuri kunya take ji..."
Mommy ta kalli Junaid sannan tace "tashi muje na rakaka É—akin Amaryarka inyaso saiku ci abinci gaba É—aya acan..."
Junaid bai Musa ba haka ya tashi tareda ɗora Khubayr saman kafaɗarsa sannan ya riƙo hannun Areeph suka fara taka upstairs, itama mommy tana biye dasu a baya tana riƙe da flask ɗin ferfesun chicken duk suka haura, suna shiga ɗakin suka tarar da Angel a kusa da ita tanata kokarin leƙa fuskar Amarya ta cikin mayafinta, mommy tace "Amarya bakya laifi ƴaƴanki suna son ganin fuskar Auntynsu ki temaka su ganki mana..."
Amriish itama kusa da ita taje tana cewa "muna so ki zama Mommyn mu, kinga Mommyn mu ta guje mu, ta gudu ta barmu bata son mu...."
Itama Angel tace "bamu san laifin mai mukayi mata ba, har ciwon zuciyan Amrish yaita tashi sauran kaɗan ta mutu amma taƙi dawowa..."
Amriish fashewa tayi da kuka tana cewa "bata tausayin mu, ciwo na yaita tashi ina aman jini, ƙirjina yaita ciwo sosai...". Itama Angel kuka take ta riƙo hannun Amrish tana cewa "kiyi haƙuri Amrisha kar ciwonki ya ƙara tashi kinga mommy ba zuwa zatai ba, kawai muma mu manta da ita...."
Amriish tace "Ni daman babu ruwana da mommy, yanzu bana sonta tinda ga Auntyn mu kawai sai ta zama Mommyn mu koh?...". ta ƙarasa maganar tana gayawa Angel,

Ogah Junaid yana É—auke da Khubayr lokaci guda ya tsinci kansa a wani irin yanayi, tinin hawaye suka wanke masa fuska, jin yanda yara suke ganin laifin mahaifiyarsu wacce ta daÉ—e da barin duniya...
Chapter 84 · 0% Book details