Sashe 51
Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Bayan isar su gidan suka tarar dashi shima ya fito daga cikin gidansa da motarsa alamun wani guri zaije, ganin mutane a tsaye da akwatunansu mata tana É—aga masa hannu, cike da mamaki ya buÉ—e murfin motar ya fito sakamakon rashin gane kosu su waye ne, da sauri mommy ta nufi wajensa tana murmushin farin ciki, ganinta yasa malam Lawan tsorita da sauri yake ja da baya yana furta "innalillahi wa inna ilaihi raju'un, wacece kamar Hajia Fateema?..."
Mommy tsayawa tayi tana kallonsa daman tasan hakan zata faru, kafin su yadda da ita sai ta fahimtar da su tace "please malam Lawan kar ka tsorita dani dan Allah, wallahi nice Doctor Fateema ban mutu ba da raina..." cike da mamaki ya sake maimaita cewar "baki mutu ba?..." ɗaga masa kai tayi tana murmushi, sauƙe ajiyar zuciya yayi sannan yace "toh amma ya akai kika tsira kuma?.." Mommy tace "kafin kamun waɗannan tambayoyin ka fasa zuwa ko ina mu shiga cikin gidan..."
Malam Lawan ya ɗaga kai yana kallon mutumin da yake tsaye gefe guda yace "wancan fah kice masa ya iso cikin gidan..." yana kaiwa nan ya buɗe gate suka shiga daga ciki kai tsaye babban falo ya nufa dasu, a falon ya tarar da matarsa ya sanar mata cewar ta haɗo kayan abinci da drinks, yana tsaye saiga Mommy ta shugo da sallama a bakinta ya amsa mata cikin kulawa sannan ya nuna mata waran zama tareda tsokananta yana faɗin " Allah dai yasa ba Aljana bace ta fito a suffar Hajiya Fateeman mu...". ya ƙarasa maganar tareda zaunawa shima, dariya abun ya bawa mommy tace "in ma Aljana ce ai baza a guji mai suffar Hajiya Fateema ba..."
Daiden lokacin da Sarki Raamud shima ya shugo da sallama a bakinsa, ganin sarki Raamud yasa malam Lawan miƙewa da sauri yana kallon sarki Raamud, a ruɗe yace "Raamud?...". shima sarki Raamud tsayawa yayi yana kallon Malam Lawan cike da mamaki shima ya ambaci sunansa da cewa "Artaf daman kana duniya?..."
malam Lawan kallon mommy yayi sannan ya maida idonsa kan sarki Raamud yace "za zauna mana, nasan ka juma baka ji labarina ba shiyasa kake tambaya ko ban mutu ba daman, amma ni nasan kana nan amma ban taɓa tunanin zaka zo Nigeria ba..."
Sarki Raamud zama yayi tareda bashi amsar "eh nazo Nigeria ne saboda Æ´aÆ´ana amma ba jumawa zan koma saboda masarauta.."
Malam Lawan yayi murmushi haƙiƙa yaji daɗin maganar sarki Raamud yanzu ya ƙara tabbatarwa da cewar ya shiryu ya kuma rungumi Junaid a mazannin ɗansa...
Mommy dai sake baki tayi tana kallon ikon Allah baki na kakkarwa tace "am am daman kunsan juna ne?..."
jinjina kai malam Lawan yayi yana kallon mommy yace "ata sanadiyar wa kika Sanni?.." tace "ata sanadiyar marigayi mijina..." ya kuma cewa "okay meye matsayin wannan agurin mijinki?.." ya ƙarasa maganar yana nuna sarki Raamud,
Mommy tace "shi ɗin ɗan uwansa ne" malam Lawan yasau ƙayataccen murmushi sannan yace "toh kinga kuwa akwai kyakkyawar alaƙa dake tsakanin mu, domin ni ɗin ma ɗan cikin masarauta ne..."
Mommy ta zaro ido waje cikin ɗaga murya a ruɗe tace "tayaya hakan zata faru?..." malam Lawan yace "ki ƙwantar da hankalinki zan sanar miki amma sai mun haɗu gaba ɗaya dasu Junaid..."
Mommy kallonsa take kai kawai ta É—aga mashi gaba É—aya ta shiga cikin zullumi,
Sarki Raamud ne yayi magana tareda faÉ—in "ina su Junaid ne?.."
sauƙe numfashi malam Lawan yayi yana girgiza kai yace "wato abunda ke faruwa shine!. duk abubuwan daya faru saida ya ƙwashe tas ya sanar musu,
Hankalin mommy ba ƙaramin tashi yayi ba jin irin ƙalubalen da yaranta suka shiga Kuma duk ata sanadiyar ta, dafe goshi tayi tana faɗin "innalillahi wa inna ilaihi raju'un, Ayushert tana prison shi kuma yana kulle a gurin aikinsu..." a zabure mommy ta miƙe tsaye tana faɗin "a gaskiya bazan bar yarana su ƙara ƙwana acikin wannan halin ba, dole zanje na karɓe su, daman ai saboda ni akayi musu haka koh? toh yanzu zanje na karɓo kayana...". tana kaiwa nan tayi ficewarta daiden lokacin da aka shugo musu da kayan abinci, mommy ko tsaya kallon abincin batayi ba, suma haka suka biyo bayan ta malam Lawan yace "ku tsaya na kaiku da motata, kamata yayi mu fara zuwa dubo Junaid daga nan sai mu wuce prisoner..."
haka kuwa akayi kai tsaye headquarters suka wuce,
★★★★★
Junaid kuwa yana ƙwance ga zazzaɓin da yake damunsa gaba ɗaya ya fita hayyacinsa, duk ya rarrame sakamakon rashin cin abinci domin idan ya tashi yaga abinci ba ci yakeyi ba saidai ya ɗan kurɓi lemo shikenam, sumar sajensa zuwa gemu duk yayi tsayi harta suman kansa saboda tsawon wata uku babu gyaran gashi balle ya rarrage sumar sai fuskar tayi fiyau, shima babu maraba da wanda yake zaman gidan prison, sai dai shi Junaid ana kawo masa abinci mai kyau ne sannan muhallin da yake shima mai kyau ne, fita ne kawai aka haramta masa,
yana ƙwance ya lulluɓe kansa da mayafi kamar mai yin bacci, shi kaɗai yanata saƙe² aransa, tinda yake ba'a taɓa ɓata masa rai kamar na wannan karan ba, yana tunani aransa cewa "an raina mun wayo wallahi amma na yanke hukuncin koda sun nemi na dawo aiki wallahi bazan dawo ba, ni gurin da za'a rainani bana yadda na zauna a gurin, bansan kuma yaushe zasu buɗe mun ƙofa nayi tafiyata ba, waɗannan mutanen ba ƙaramin cutana sukayi ba dole naɗau fansan abunda suka mun, bazan ƙyalesu ba bansan a wani hali Yushert take ciki ba, ko sun kasheta ko tana gidan prison Allahu a'alamu, ya Allah ina neman agajinka! ya Allah ka temakeni banida wata mafita sai abunda ka zaɓa mun..." ya ƙarasa maganar yana kukan zuci..
bai ankara ba yaji ana ƙoƙarin buɗe ƙofar ɗakin, a zabure ya tashi zaune yana sauƙe numfashi daƙer, wani daga cikin sojojin ne ya shugo ya sanar masa cewa "ya fito ana son ganinsa..." yana kaiwa nan yayi ficewarsa a ruɗe Junaid yabi bayansa gudun kar a sake ƙarƙame shi, yana fita kuwa kayinsa ya fara juyawa wani irin hajijiya ne yake shirin ɗaukarsa, yana dafe da kayinsa, ganin bazai iya tafiya da kansa ba dasauri yasa hannu ya dafe jikin gini yana shirin kaiwa ƙasi,
wasu sojoji ne su uku suka nufo kansa suna faɗin "lafiya kuwa Ogah Junaid, meyake faruwa ne?...". hannu suka kai suna shirin ɗago shi jin jikin yanda yaɗau masifar zafi yasa suka razana suka ce "wannan ai bashida lafiya ne, muyi saurin kaishi Office ɗin da General yake da iyayensa suna ciki.." a haka suka ɗaga shi yana jan ƙafa daƙer su kuma suna riƙe dashi,