Sashe 78
Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A washe gari Areeph da Rapeekh sun zana exam ɗinsu na Mathematics kuma shine na ƙarshe, Mathematics yayi wahala sosai domin duk cikinsu babu wanda kansa bai ɗau zafi ba, don ko ɗan jami'a iya kacin exam ɗin da za'a masa kenam, duk da babu wanda ya cinye jarabawar gaba ɗaya amma an samu wanda ya fi ɗaya da marking ɗaya, saida akayi tsananin bincike akai tukun aka samu cewar Areeph yafi Rapeekh da marking ɗaya da rabi, ai kuwa a ranar Areeph farin ciki kamar kamar dai, Rapeekh shima duk da baici exam ɗin ba amma yayi farin ciki sosai ganin yanda Areeph yaketa tsalle yana murna shima saiya tsinci kansa cikin murnar abokin takararsa ya samu abunda yake so, sam Rapeekh baiyi baƙin ciki ba, saima taya shi murna da yayi, da haka har aka bawa Areeph kyaututtuka manya², shima Rapeekh an bashi wani abu amma bai kai wanda aka bawa Areeph ba,
Shima Areeph acikin kyaututtukan daya samu ya raba biyu ya bayarwa Rapeekh rabi shima ya riƙe rabi dake yaran ba masu son abun duniya bane, sunada dukiya sosai shiyasa basu wani damu akan kyautar ba, burinsu shine ɗaya acikinsu yafi ɗaya marking shine gwabzawar da suke tayi....
★★★★★★
Part of the kingdom..
Babban masarautar sarki Raamud ba ƙaramin tsaruwa yayi ba, domin an ƙara tsara shi, an mayar da masarautar part biyar, part ɗin farko shine yake ɗauke da Babban fadar sarki, daga nan za'a wuce cikin falon sarki Raamud da manya-manyan kujeru masu kyan gaske, ga babban plasman a manne da bango da wani glass table a tsakiyar kujeru, ta gefe guda kuma ƙaton dinning table ne da kujerunsa guda 12 a jere, daganan sai upstairs mai part biyu hagun da dama, upstairs na dama shine zai kai ka har bedroom ɗin sarki Raamud, upstairs na hagun kuma zai kai ka ne har ɗakin mommy....
Part na biyun gidan kuma saika wuce fadar sarki tukun a ƙara buɗe gate na biyu shine zai kaika part ɗin Ogah Junaid da iyalansa, kamar yanda na sarki Raamud yake haka shima nasu yake, daga nan sai anyi tafiya mai nisa an sake buɗe wani gate na uku sai kuma part ɗin Uncle Artaff wanda aka tanadar masa tinda shima yanada gado acikin masarautar shima kamar yanda aka tsara nasu part ɗin haka akayi wa nashi, daga nan sai babban hospital dake cikin masarautar wanda a wannan part ɗin Narasimha yake, shine mai musu magani da zaran basuda lafiya, sai kuma wani part na wasan yara, da kuma wajen buga ball, acikin masarautar akwai wani gate na ɓangare guda wanda ana buɗe shi sai lambun kayan fruits da vegetables da bishiyoyi mango da casho da banana da sauran abubuwa,
A wani part kuma akwai gate ɗin da idan aka buɗe wajen ma'ajiyin Dokunan sarakuna ne da wasu kayayyakin yaƙi, ga ta ɓangare guda kuma jerukan motoci ne na alhurma kala-kala...
Ga wasu karnukan turawa da aka zuba a kowani part na cikin masarautar, masu gadin masarautar kuma wasu manya-manyan sojojin Amurkawa ne da turawa, ga wasu munanan Bodyguards masu ƙarfin gaske da manya-manyan bindigunsu, mata masu ayyukan gidan, an nemosu ne ba ragwaye ba. Waɗanda kullum suna cikin Aiki,
Mommy ko ɗaga tsinke batayi acikin masarautar nan, komai yi mata akeyi da umarnin Sarkin amma ba'a son ranta ba, saboda ita ta saba da motsa jiki da wasu ayyukan gida, mommy tayi ƙiba sosai ta ƙara fari kamar jini zai fita, tayi kyau matuƙa, duk abunda take buƙata kuwa dasauri ake mata, duk wani kulawa tana samu a wajen sarki Raamud, domin ba ƙaramin ƙaunarta yake yi ba, baya ƙaunar ganin ɓacin ranta.....
Yau ranar Monday Around 12AM na dare. Mommy tana ɓangaren ɗakinta ita kaɗai ta tashi tana salati tareda jero addu'o'i daƙer ta tashi akan bed ɗinta ta nufi hanyar fita, kai tsaye downstairs ta sauƙo falo, daga nan ta nufi wani ɗakinta na magungunuwa taje ta ɗauko boxes sannan ta haura saman ɗakinta, tana shiga bedroom ta shige toilet, saida tayi kusan awa guda acikin toilet kafin na fara jiyowa kukan jariri,
Ni Asmeetah ina daga bedroom abun ba ƙaramin bani mamaki yayi ba, ina tsaye sai kuma na ƙara jin kukan jariri kuma du, kafin kace mai sai muryoyin jarirai suka fara kuka a jere a jere, banyi gaggawar shiga cikin toilet ba, na cigaba da tsayuwa can sai naga ta buɗe ƙofar toilet, cike da mamaki da kuma son ganin abunda ke faruwa na zurawa ƙofar ido ƙwatsam sai naga mommy ta fito hannunta riƙe da jarirai biyu, tazo ta kwantar dasu saman gado daman ta rigada ta yanke musu cibiya ta wanke su tas, ta buɗe wardrobe ɗinta ta ciro kayan jarirai na sanyi farare masu kyau, duk ta sassanya musu ta feshe su da turare masu ƙamshin gaske wanda bazai cutar dasu ba, still ta kwantar dasu ta lulluɓe su, acikin wannan daren ta sake shigewa cikin toilet ta haɗa ruwan zafinta na gaske tayi wanka ta gyara cikin toilet ta feshe da turare yanda bazaiyi ƙarnin jini ba, ta wanke kayanta wanda ta ɓata, ta shirya kanta tsab itama ta gama feffeshe jikinta da turare da duk gaba ɗaya ɗakin, sannan ta tottofa wa jariran addu'o'i ta ƙwanta gefensu har zuwa sallar asuba...
Har gari ya waye sarki Raamud bai san mommy ta haihu ba, hatta suma ma'aikatan gidan mommy ta hanasu shiga cikin É—akinta a yau, bata sanarwa kowa ba, kuma dake É—akinta yana saman Upstairs ba kowa ne zai iya jiyowa kukan jariran ba,
Dalilin yin haka shine haihuwar nan ba ƙaramin kunyata mommy yayi ba, ita har cikin zuciyarta bata so ta haihu a halin nan ba, saboda a cewar ta bai dace ace yaranta suna haihuwa itama tanayi ba, taso ace tabar musu haihuwan ita kuma ta haƙuri amma saidai sarki Raamud ne ya tsayar mata akan cewa dole saita haifo masa wasu yaran, hakan yasa ta haƙura tabi umarninsa, shine dalilin da yasa yanzu ta haihu kuma ta gagara sanarwa kowa,
Saida wata daga cikin kuyangen tazo zata ƙonƙosa ƙafar ɗakin mommy taji kukan jariri, da gudu ta juya baya bata tsaya a ko ina ba sai a ɓangaren sarki Raamud, tana zuwa ta durƙusa a gabansa tana maida numfashi tace "mai martaba sarauniyarka ta haihu naji kukan jariri acikin ɗakinta..."
Sarki Raamud bai tsaya jin ƙarashen maganar ba ya miƙe tsaye da hanzarinsa ya nufi hanyar fita kai tsaye part ɗin mommy ya nufa, yana zuwa ya tura ɗakin yaji a rufe ta ciki, bugawa ya soma yi da ƙarfi yana ƙiran sunanta, daƙer tazo ta buɗe masa cikin jin kunya kanta a sunkuye, sarki Raamud kamar zai tashi sama tsabar farin ciki, cike da mamaki yake bin jariran da kallo sai kuma ya ɗago ya kalli mommy gaba ɗaya har shirin zaucewa yake tsabar farin ciki, dasauri yakai hannu ya rungumo mommy sosai kamar zai mayarta cikinsa,
tsawon shekara uku taƙi haihuwa sai a wannan lokacin, nan ma saboda ta farantawa sarki ne yasa ta haihu, yana cikin godewa Allah yaji tace "dan Allah ina neman alfurmanka mai martaba .."
juyowa yayi cike da farin ciki yace "ki faÉ—i duk abunda kike so zanyi miki Sarauniyata...."
Tace "dan Allah inaso ne kar a sanarwa su Junaid cewa na haihu, Ni kar a sanarwa kowa ma, dan Allah...."
Sarki Raamud yace "indai abunda kike so kenam shikenam nayi miki Alƙawari bazan sanarwa kowa ba saidai su zo su tarar dake da ƴaƴanki..."
Kallonsa tayi sannan tayi murmushi, yace "amma zaki ban mamaki, taya kika haihu ke kaÉ—ai? Sannan ba wani jikkata ko rashin lafiya a tattare dake?"
tayi murmushi sannan tace "ikon Allah kenam, haka Allah yaso dani..."
Shima yayi murmushi yakai Idonsa kan yaran yace "Masha Allah duk mai aka samu?.."
Mommy tace "Namiji da kuma Mace..."
Sarki Raamud lokaci guda kuma sai yake jin hawaye yana shirin gangaro masa saboda ya tuno da Bara'at uwar Ayush, itama twins ne a cikinta akazo aka salwantar dasu tareda mamansu sai kuma gashi Allah ya maido masa su ata ɓangaren mommy,
Zama yayi ya É—auki yaran ya tottofa musu addu'o'i sannan yace "na sanya wa yaron suna Artaff wato mai sunan Uncle Artaff (malam Lawan)...
Macen kuma na sanya mata suna Bara'at..."
Mommy taji daÉ—i sosai dajin sunan da ya sanya musu....
★★★★★
Ranar Bikin Hafzat da Judan kowa acikin danginsa sunzo É—aurin Aure har shima kansa Judan, sarki Raamud shima yazo Nigeria amma banda mommy, ita mommy abunda ya hanata zuwa shine jariranta waÉ—anda suka ci sati guda a duniya, itama Hafzat ta koma Kano domin daga can za'a É—aukota acikin Æ´an uwanta...
Itama Lailah aranar aka ɗaura mata Aure ita da Doctor Mansur ɗinta, an kaita gidan mijinta cikin ƙoshin lafiya.
Itama Hafzat aranar aka sata a jirgi sai ƙasar Jidda ƙasar su judan kenam, anan zata zauna...
Ayush ba ƙaramin kewar Hafzat tayi ba, ga Ogah Junaid duk ya kori ƴan aikin gidan, saita jita shuru ba daɗi, ga yara na school shima idan ya fita yawonsa baya dawowa da wuri, gaba ɗaya zaman kaɗaici yayi mata yawa ga ayyukan gida sunyi mata yawa gaba ɗaya ta shiga damuwa sosai....