← Book details Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 85

Sashe 14

Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ayush jin gobe zasu tafi yaƙar iyayenta saita sake fashewa da wani sabon kukan,
daƙer Angel take rarrashinta har Ayush ta ɗan kwanta bacci...

daga nan Angel ta miƙe ta fice a ɗakin, da sauri ta sauƙa downstairs ta fice daga falon ma,
tana zuwa gurin parking motocin gidan ta zaɓi ɗaya ta shiga tareda tayar da motar ta miƙi hanyar get,
maigadi ne yayi saurin buɗe mata get ganin yanda ta tafo da gudun gaske, tana fita daga gidan ta miƙi hanyar gidansu Laylah..

Shi kuwa Junaid yana tsaye a bakin window ɗakinsa yana ganin lokacin da Angel ta fita masa da ƙaramin motarsa jeep,
Mommy ta daÉ—e da barin room É—insa domin yanzu haka tana kitchen...

Junaid komawa É—ayan room É—insa yayi yanason duba cameran tsaro na gidan shima,
yana zaune ya kafa eyes É—insa akan computer, a cikin camera video daya gani ya fuskanci abubuwa da dama,
jinjina kai ya shiga yi yana murmushi, tashi yayi ya koma bedroom ya É—auko phone É—insa yazo ya jona a jikin computer zai kamo location na contact É—in da aka turo da video ta WhatsApp bayan yayi tracking number,
computer ta nuna number a nan garin Abuja take, yana bibiyar number har ta kaishi yanda layin take a ajiye wanda tazararsu da É—an rata kaÉ—an,.
daya bi location kuma sai computer ta nuna masa gidan Doctor Hasheem,
ƙara jinjina kansa yayi yana zargin mutum biyu acikin gidan nan!
Doctor Hasheem ko kuma Lailah, duk da baiga Doctor Hasheem ya shiga É—akin Ayush ba amma yana konkonto akansa,
kodai Doctor Hasheem ne yasa Lailah ta haɗa Ayush da gardin nan ko kuma Lailah ce tayi hakan saboda ta ɓata sunan Yushert,
Amma kuma yana tunanin shin wacece matar nan mai liƙab....
yana cikin wannan tunanin wani abu ya faɗo masa arai dasauri ya shiga wani ɓoyayyen camera shutting na cikin ɗakin Ayush domin acikin ɗakinta ma yasa camera amma sai dai baya dubawa sakamakon ita kaɗai ce a ɗakin,
kafin ya shiga camerar ɗakin Ayush saida yasa security wanda ba wanda zai iya ganewa sai iya shi kaɗai, yana duba video abunda ya faru a cikin ɗakin bayan Ayush ta shiga da gudu tana kuka saiga wannan matar mai liƙab yana son ganin fuskar matar saidai kash camerar bayanta ya ɗauka banda fuskarta,
ga kuma lokacin da Ayush ta tafo zata rungumeta Umantata ta hankaÉ—ata tareda marinta,
sai abun ya ƙara ɗaurewa Junaid ƙwaƙwalwa,
dasauri ya ɗauki abun jin magana ya kara a kunnuwansa yana jin duk tattaunawar da sukeyi, yaji Ayush tana ƙiran Uma kuma duk maganar da sukayi akan Junaid ne yaji Uma tana cewa "idan baki Auri Junaid ba, Babu ni ba ke kuma bazaki sake ganina ba har abada.."
Junaid ƙwaƙwalwarsa ce ta fara juyawa yana faɗin "me hakan yake nufi? shin wacece wannan matar? daman Yushert tanada iyayenta a raye? kenam munafurtar mu take yi? shin meyasa ta ɓoye mana abubuwa da dama?..."
abunda yake masa yawo kenam a ƙwaƙwalwarsa,.
gani yayi matar ta shige toilet da gudu a yayinda Angel ta shugo,
bayan ta fita kuma matar ta fito, a lokacin ne yake da damar kallon fuskar matar saboda ta fuskanci camera saidai kash tin a cikin toilet tasau liƙab ɗinta ta fice a ɗakin,
amma saidai abunda ya ƙara ɗaure masa kai a camera waje baiga fitarta ba,
yana zaune can saiga Lailah ta shugo ɗakin, duk yana kallonsu yana kuma sauraron abunda suke faɗa, gani yayi Lailah ta curo magani ta bawa Ayush daga nan kuma hankalinta ya ɓace mata, daga baya kuma saiga mutumin nan ya shugo, yana kallon yanda Lailah take musu video,
Ran Junaid ne yayi matuƙar ɓaci sosai, ya dafe goshinsa tareda tusa tafin hannunsa cikin sumar kansa ido a rufe, shi kaɗai yasa irin raɗaɗin da yake ji aransa,

Kawar da video waransu Lailah yayi yana son bibiyar matar data fita daga É—akin Ayush kafin su Lailah su shugo domin matar tafi tsaya masa arai,
camerar wajen ɗakin Ayush ya buɗe gani yayi matar ta tsaya a bakin ƙofar Ayush bayan wasu ɗan seconni yaga ta ɓace ɓatt
A razane Junaid ya miƙe tsaye yana zaro ido waje yana ja da baya...

********

Angel ce ta shige cikin gidan su Lailah bayan maigadin gidan ya buÉ—e mata, saida yaje ya tambayo aka bashi umarnin ya buÉ—e mata,
dasauri Angel ta fito daga cikin motar ta nufi hanyar mashigar shiga falon,
Shiga tayi ta samesu sunata hira a falo ga plasman ana showing India film,
Iya su kaÉ—ai ne a falon daga Doctor Hasheem sai kuma Lailah,
Lailah tana bashi labarin abunda ya faru a gidansu Maimoon data je suna dariya,
Ganin Angel yasa duk suka miƙe tsaye suna kallonta
saida Angel taje gabansu kafin tayi musu sallama tana murmushi!
Lailah har da kuka ta tana faɗin "innalillahi Yayana sune suka mun duka a hospital Koh, yanzun ma sunzo su ƙara sumar dani wayyo Allah nasara.".
tana ɓoye a bayan Doctor Hasheem.

Dariya Angel tayi sannan tace "awww daman kinada tsoro Lailah? gaskiya ban taɓa tunanin kinada tsoro har haka ba, bani na dakeki ba kuma banzo gidanku don na dake ki ba amma kuma idan kika nuna mun rashin gaskiya akan abubuwan da zan tambayeki toh kuwa nima zan dakeki, duka ma irin wanda bakiyi zato ba...."
ta ƙarisa maganar tana zaro mata ido.

Doctor Hasheem ne yace "lafiya kuwa Malama ya za'ayi kinzo gidansu kuma kice zaki dake ta, ina ruwanta daku meyasa kuke son shiga rayuwarta ne, marainiyar Allah kodan kuna ganin ku sojoji ne shine kuke iya zalincin ku..."

Angel ce ta ɗaga masa hannu tareda cewa "dakata Mallam Hasheem ba gurinka nazoni ba amma kuma za'ayi komai a gabanka! ku zauna domin ba wani ɓata lokaci zanyi ba..."

Gaba É—ayansu zama sukayi,
Angel tace "Lailah nazo gurinki ne saboda muna zargin wani abu daya faru, ki sani duk tambayoyin da zan miki karki sako mun ƙarya a ciki domin faɗar gaskiyarki shi zai sa ki kuɓuta daga zargin da ake miki..."

Gaban Doctor Hasheem ne ya buga da ƙarfin gaske a zabure yace "Please meya faru?.."
Angel É—aga masa hannu tayi ta dakatar dashi tareda cewa "koma meye ne ai zaka ji.."

Doctor Hasheem shi tunaninsa kar maganar akan Maimoon ce,
Ita kuma Lailah tintinin tasha ruwan jikinta domin ta saddaƙar akan video Ayush ne,
zuciyar ta kuwa sai bugawa yake da ƙarfi-ƙarfi...

gyara zama Angel tayi sannan tace "Lailah a ranar shagalin Ogah Junaid da misalin ƙarfe 5 meya kaiki ɗakin Ayush?.."

Duk da fankan da yake kaÉ—awa a É—akin amma haka Lailah take ta sharar gumi tana muzurai bakinta na motsi mutsil-mutsil,
Angel ce ta katseta da cewa "magana nake miki Lailah, ko ba amsa?.."

Dasauri Lailah ta ɗago tana ƙiƙƙina tace "wallahi tallahi ba abunda ya kaini ɗakin Ayusher, kawai dai mun samu matsala ne shine aranar naje neman yafiyarta kuma ta yafe mun..."

Angel tace "toh meye kike ta faman wallewa shin kinsan abunda ke faruwa ne? abunda na tambaye ki kenam fah amma dubi yanda kika rikice mun,
kina É—akin Ayush akwai wanda ya shiga É—akin shin wayene?.."

Lailah tana zazzarowa ido waje tace "ehhh to ina zaune da Ayush akwai wanda ya shugo shine nake tambayarta ko wayene wannan tace mun baƙonta ne, daga nan na tashi na barsu a ɗakin..."

Jinjina kai Angel tayi sannan tace "Lailah bana son ƙarya! nagaya miki idan kika mun ƙarya babu ke babu fita daga cikin wannan case har a gano gaskiyar, idan kuma Junaid yasan kina cikin wannan Case toh kiyi kuka da kanki, zaki raina mun wayo naga kusan awanku guda a cikin ɗakin Ayush, mutumin yana ciki kuma kusan a jere kuka fito daga ɗakin shine farkon fitowa before ke.."

Lailah fashewa tayi da kuka tana faÉ—in "wallahi tallahi fitowa nayi na shiga É—akin Ogah Junaid nayi bacci..."

Angel hannu tasa a aljihun wandonta mai kakin soja ta ciro bindiga tace "ƙarya kike Lailah ɗakin Ogah Junaid da hannuna na kulle da key kuma lokacin key ɗin ɗakinsa na hannuna, shin zaki gaya mun gaskiya ko saina ragargaza miki ƙafa ki zama gurguwa..."

A ruÉ—e Lailah take faÉ—in "a'ah dan Allah ki rufamun asiri karki harbeni Æ´ar uwa zan gaya miki,
Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! ki temakeni fitowa nayi na tsaya a bakin ƙofa ina jiran su, amma ni bana cikin ɗakin.."

Angel tace "kenam iya su biyu kika bari a É—akin?.."
A gigice Lailah tace "eh eh ehh wallahi..."

Jinjina kai Angel tayi tana murmushi tace "toh amma waye ya musu video?.."
Lailah tace "nima ban saniba.."

Kunna kunamar bindigarta Angel tayi ta saita ƙafar Lailah tace "ina dai baki saniba?.."
Ihu Lailah ta fara kurmawa a gidan tana magiya,
Shima Doctor Hasheem ɗin tasowa yayi da sauri yana roƙon Angel yace "kiyi haƙuri mana Angel kibi komai a hankali kar tsautsayi yasa ki harbeta.."

Angel juyowa tayi tana kallon Doctor Hasheem cike da takaici tace "whattt! tsautsayi fah kace Hasheem, ni ai bansan tsautsayi ba, abunda yake raina kawai nake aikatawa, domin mu harbi ba komai bane a gurin mu! bazan harbeta a wajen da zata mutu ba amma idan bata gaya mun gaskiya ba zan harbeta agurin da zata jikkata,
Doctor Hasheem kaje ka zauna inajin kunyarka fah, banaso ka shiga lissafin da ba naka ba..."

komawa Doctor Hasheem yayi ya zauna domin yasa Angel wani sa'in batada Annuri idan Alluran sojan ta ya motsa...

Durƙusawa ƙasi Lailah tayi tana kuka tareda faɗin "dan girman Allah kiyi mun rai Aunty Angela wallahi banida laifi bansan komai ba, kuma bansan wanda ya tura video baaa.."
ta ƙarasa maganar tana kuka.

tsawa Angel ta darara mata tace "kiyi mun shuru, ai Lailah kin ƙara jefa kanki cikin masifa indai baki gaya mun gaskiya ba, taya kika san an tura video?..."

Shuru Lailah tayi bata ma san ta faÉ—in hakan ba,
ƙiƙƙina ta soma yi maganar ta na rawa ba'a jin abunda take faɗa ma, tsabar rikicewar da tayi..

A fusace Angel ta tashi taje har gabanta ta zabga mata wani irin gigitaccen mari tace "ki buÉ—e baki kiyi mun magana ko kuma na tafi dake headquarters su Ogah Junaid yanzun nan..."
Chapter 14 · 0% Book details