← Book details Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 85

Sashe 26

Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan su kuma sai Diragogi🦖🦖🦖🦖 suma sun kai ɗari a jere..
Bayan su kuma sai macije masu dafin bala'i, sara É—aya suke yiwa mutum ya rasa rayuwarsa, suma suna nan a jere sun kai million....
daga su kuma sai a fafata da Munafurrr...

*****

Mommy daga Nigeria Alwala tayo sannan ta tsai da sallolin lafula tareda jero addu'o'i, tana faÉ—in
"Allah ya tsare sojojin da suka fita yaƙin nan, Allah ya dawo dasu lafiya, Allah ya basu nasara..."

Itama Ayush zuwa tayi tayo alwala itama ta fara sallolinta na neman kariya daga wajen Ubangiji...
tana addu'a Allah ya tsare mata iyayenta domin tasan yanzu mahaifinta bashida wani ƙarfin iko...

Munafurr Allah Allah yake sojojin nan su iso a fara fafatawa, domin ya tanadar musu da abubuwan mugunta, kamar yanda suma sojojin suka haÉ—a runduna guda...

Har yanzu kuma Damusa yana nan a ɓoye guri ɗaya ga kuma takobi a gabansa....

*Amm nace baa Ina masu fita yaƙi acikin readers nace how market🙌🙌*
*Masoyan Junaiduu ban hango ku ba👀 shin kunata inaa?*
*Cikin Egwa ne ko kuma kuna cikin motoci kodai kuma kuna kan Doki ko kuma kuna daga sama cikin elekwabta kodai kune a ƙasa masu gudu da ƙafafuwan ku?...*

*Masu cikin elekwabta kune gawar farko domin jegaru masu aman wuta furawa suke yi🤣🤣*
*Ga kuma mikiyoyi masu cire eyes😳😳😳*

Toh masu karatu anan zan dakata sannan na tafi hutun sati guda, na barku lafiya...

𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️

𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔

the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅

𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️

𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871

*💫💫{{N W A}}💫💫*

Book two

C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 31 ➡️ 32

Munafurr ganin sojojin sun kusan isowa yasa Dabbobinsa suka fara kai musu farmaki,
Dragon's 🐉🐉🐉🐉 ne suka fara tashi sama sunkai ɗari biyu suka nufi wajen rundunan sojojin,
Sojoji kuwa suna ganin abubuwa sun nufosu anan suka fara fitar da bindigoginsu suna harbawa, suma Dragogin haka suke amayar musu da wuta,
ga kuma jegaru suma suna bata nasu wutan, suma sojojin wasu suna harbi wasu kuma suna guduwa, haka motocin sojojin nan suka fara tashi sama suna bom kasancewar akwai bomabomai acikin motocin,
tin daga nan aka fara asarar rayukan sojoji saboda motocin da suke ƙonewan akwai sojoji aciki, waɗanda suke sauran motocin da wuta bai taɓa su ba haka suka rinƙa fitowa daga cikin motocin suna harbi kamar ruwan sama,
suma jegarun an harharbesu domin dragon's da jegaru an harbi sun kai É—ari saboda yawan harbin da ake musu,
Acikin motor gudà kuwa wata soja ɗaya ce take ciki bata fito ba sakamakon ƙafarta daya maƙale a tsakanin ƙarfe da ƙarfe na cikin motar, sai ihu take tayi ganin ko wani mota ƙonewa yake, tana ta ƙoƙarin cire ƙafarta amma ta kasa, sauran sojojin kuwa kowa ƙoƙarin ceton ransa yake ko sauraronta ba'ayi ba, tana cikin wannan halin sai ga Junaid ya nufo gurinta akan doki da gudun gaske zai cetota, kafin ya isa gurin kuwa har wani jegarin ya huro wutan bakinsa kan motar wuta da bom sun haɗu lokaci guda motar ta tashi sama tana kamawa da wuta ga sojar nan tana ciki sai faman kurma ihu take,
A razane Junaid ya ƙwalla ƙiran sunanta da ƙarfin gaske ya furta
"Rumaaanaaaa...."
daiden lokacin motar ta faɗo ƙasi ta dagargaje!
hatta shima Junaid saida ya yi sama shida dokinsa suka doku a ƙasi tsabar ƙarfin boom ɗin daya tashi da motar,
cikin firgici ya ɗago yana ƙiran sunanta "Rumana! Rumanaa!! Rumanaaa!!!...". Rumana kuwa tintinin ta dagargaje ita da motar babu sauranta, motar kuwa sai ci da wuta yake...

wani Dragon ne yazo ta bayan Junaid ya buɗe bakinsa ya amayo masa da wuta lokaci guda Junaid yayi wani irin juyi ya saita bindigarsa ya fasa masa kai da harsashi, takaicin mutuwar Rumana ne yasa ya harzuƙo ya fara harbin jegarun nan kamar mai, gani kake sunata faɗowa daga sama zuwa ƙasa, jegaru sunkai hamsin suka rufo kan Junaid suna hura masa wuta, wani irin juyi Junaid yakeyi yana tashi sama tareda faffasa musu kai, waɗanda suke cikin jirgi kuma tinin an rufe babinsu duk an ƙoƙƙone musu jirgaye da mutanen dake ciki duk da suma sunyi iya ƙoƙarinsu sun kashe jegaru da yawan gaske,
rabin sojoji duk sun mutu daga yaƙin farko, wasu kumá duk sun koma dá báyá sun gudu kuma yawancin su sojoji mata ne waɗanda suka gudu aciki kuwa har da Adity itama ta gudu,
iya waɗanda suke yaƙin ƙalilan ne basuda yawa daga Junaid ne sai Angel itama tana ƙoƙari sosai domin ta kashe dragon's ba adadi..
da haka duk saida suka gama da jegaru da dragon's ya rage babu ko É—aya, Angel juyowa tayi ganin mutanensu da yawa a kwance babu rai yasa Angel tsorita sannan ta dubi kansu iya waÉ—anda suke nan bazasu wuce su hamsin ba, kuka Angel ta fara yi tana faÉ—in "dan Allah kuzo mu juya, kunga bamuda yawan sojojin, kuma bamu san mai zamu tarar a gaba ba..."

Gaba É—ayansu ja da baya suka soma yi sun É—auki maganar Angel,
Junaid ya dakatar dasu da cewar "lusarai ne idan sunje gurin yaƙi suke guduwa, sojoji babu tsoro a zukatansu saboda haka ku saki jikinku insha Allahu mune da nasara, kamar yanda aka umarce mu damu kawo sarki Raamud haka kuwa zamu kamo shi dumu dumi a hañnu, idan kuwa bai kamu ba sai mu dagargaza masa kai shikenam..."

Daganan suka saki jikinsu, a mata kuwa Angel ce kawai take nan amma sauran wasu sun mutu wasu kuma sun gudu..
Junaid ne ya kalli Angel sannan yace "ina camera?.." irin mai hango abu daga nesa,. tace "gashi nan ta miƙa masa.."
Saitawa yayi a idonsa É—aya yana hango irin abubuwan da aka tanadar dasu, Junaid jinjina kansa yayi yace "kowa ya zauna akan shirinsa, kowa ya saka hular glass saboda akwai manya-manyan tsuntsaye masu cakan ido, sannan a tanadi boms domin akwai corocodiles da kuma macizai...."
wani ne a ciki yace "Oga ina dai ba Aljanu? inhar babu toh abun zai zo da sauƙi...."
Junaid yace "wasu su shiga Egwa da zaran mun isa saiku fara harbi ku tattaka su da motar, wasu kuma su hau doki tinda akwai sauran dokunan..."
haka kuwa akayi ita Angel motar ta shiga ta miƙe tsaye tayi ready da bindigarta...

Su Junaid sune tafiyar farko domin sune akan dokin, basu fi su ashirin ba masu dokunan,
waɗanda suke cikin motár Egwa kuma an barsu a baya saboda rashin gudun motar amma daga nesa zasu rinƙa harbi har su iso gurin,
Mikiyoyi kuwa haka suka rinƙa tashi sama suna kai musu yakushi da carkwala, sojojin nan haka suka rinƙa harbesu suna faɗowa ƙasi, shi Junaid bai tsaya harbi ba kai tsaye wucewa yayi da gudu yana rataye da bindigarsa ga kuma jakar bom yana riƙe dasu,
so yake ya tsallake gate ɗin domin a rufe yake, shi kuma wanda za'a yaƙa yana ciki, toh shi da Ogan yake so ya yi bada dabbobi ba,
dayazo gurin corocodiles haka ya rinƙa jefa musu bom yana samun hanyar da zai wuce, duk suna kawo masa hari sosai yana kauce musu da haka ya tsallake su, yazo kan macijai suma bom ya rinƙa jefa musu, yana gudu da dokinsa, macizai kuma tsabar na masifa ne haka suke tashi sama suna sarar dokinsa, shi basu samu isoshi ba saboda miƙewa tsaye yayi akan dokin yanda maciji bazai taɓashi ba domin sara ɗaya suke wa mutum,
Junaid daƙer dokinsa ya ƙarasa dashi waran ginin masarautar a yayin da dokin yake shirin faɗuwa tsabar saran da macijai sukayi mishi, a lokacin kuma Junaid yayi wani irin tashi sama kamar mai furawa haka ya yi sama sosai ya kamo wani ƙarfen jikin ginin masarautar wanda yake rabin tsayin ginin, ba ƙaramin dogon gini akayi wa masarautar nan ba, duk tashi saman da Junaid yayi amma a iya rabin ginin ya tsaya, haka ya rinƙa jawuwa yana ƙara yin sama, yanason tsallake ginin...

Sojojin da suke ƙasi kuwa wasu sake baki sukayi suna kallon Junaid, suna kuma mamakin yanda suka ganshi yayi tsalle ya tashi sama kamar ɗan China ko kuma super man ko bad man ko spider man, suna cikin wannan tunanin kusan su goma haka kadoji suka rinƙa kayar dasu suna fata-fata da naman su, yayin da wasu kuma suke fafatawa da mayaƙan dabbobin, Angel ce ta ƙwalla ƙiran Junaid tana faɗin "wannan wani irin garaje ne, ina zaka iya tsallaka katangar nan? zaka iya faɗowa fa kuma idan har ka faɗo sai dai ƙashshushuwanka...." ta ƙarasa maganar itama tana mamakin yanda yahau wannan katangar mai uban tsayi ga tsantsi duk jikinsa..."
wani kada ne yayo kanta tareda buÉ—e bakinsa zai rufa mata a fusace Angel ta wurga masa bom a cikin bakinsa nan danan corocodile ya dagargaje haka ta cigaba da faffasa musu kai da harsashi, wasu kuma suna jejjefa musu bomabomai,
Chapter 26 · 0% Book details