← Book details Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 85

Sashe 72

Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Junaid yana riƙe da little Angel akan cinyarsa yana wasa da ita tareda faɗin "Jaruma ta kenam, wannan ita ce jarumata kuma Soja ta...".
ta É—ago tana kallonsa cikin Muryar yara tace "Daddy nikam Soja zan zama idan na girma ko?..."
cikin so da ƙauna ya sumbaceta akan goshi yace "yawwa Jarumata shiyasa nake ƙara ƙaunarki ai, kinga takwararki ma Soja ce ta iya faɗa sosai..." tace "Daddy ai Mommy ta nuna mana photonta da kayan sojoji ajikinta tamun kyau sosai...". murmushi yayi yace "kema ai haka zaki zama, kiyi kyau acikin kayan sojoji..."
Little Angel cikin zaƙewa takai hannunta saitin goshinta tana faɗin "jinjina ga tutar sojoji..." daga nan ta sara wa Daddynta..
Gaba É—aya kwashewa sukayi da dariya, Ayush hannu tasa ta maki gadon bayanta tana dariya, kuma daman Little Angel ta fisu surutu da iyeyi, Junaid ya kalli Ayush cike da mamaki yace "duk waye ya koya mata wannan?..."
Ayush É—aga kafaÉ—arta tayi alamar itama bata saniba, Hafzat dake kujerar gefe dasu sosai tace "wallahi duk a Film take gani, kuma tafi kallon Film É—in sojoji..."
Junaid ƙara rungumarta yayi tareda lumshe idonsa yana hasasho fuskar Angel marigayiya, gaba ɗaya ta dabaibaye masa ƙwaƙwalwa,
saida ya gama tunaninta tukun ya buÉ—e eyes É—insa a hankali ya maida kallonsa kan Amreesh yayi mata alamar tazo ta, tana can tana kwance saman cinyar Hafzat ta taso tazo gabansa tace "gani Daddy..."
Da murmushi akan fuskarsa yace "ke kuma pah idan kin girma wani aiki zakiyi?..."
Ɗan turo ƙaramin lips ɗinta tayi tana haɗe gira tace "Ni nikam Aure zanyi..."
Zaro ido Junaid yayi yana binta da kallo,
Ayush kuwa ruwa ta kora a bakinta amma jin abunda Amrish ta faÉ—a yasa ta burtso da ruwan tana kwashewa da dariya harda kama cikinta,
Junaid yace "Keee leave my front dalla dubeta, waii Aure kuttt..."
Kallon Ayush yayi ganin sai dariya take yasa ya haɗe rai tareda faɗin "ke kika ɗorata akan keken ɓera koh?.."
Ayush toshe bakinta tayi da hannu tana ƙunsar dariya tace "Ni kuma? wallahi ban taɓa musu maganar Aure ba...". yace "amma tayaya tasan ana yin Aure?.."
tace "taya bazasu sani ba bayan yaran sunyi wayo yanzu fah shekara huÉ—u suka nufa, kuma ko a makaranta ai zasu ji ana maganar..."
Yace "ƙarya kike babu yanda za'ayi ƴan Nursery school ayi musu maganar Aure, dole ma duk na tattara ku mu koma ƙasar waje saboda kar a lalata mun yara da maganar Aure..."
ya ƙarasa maganar yana kallon Amrish ya kuma cewa "ke kuma ko Takwarar ki Mommy saida tayi karatu ta samu Aiki tukun tayi Aure, Babbar likita ce don haka kar na sake jin kinyi maganar Aure kinji koh?..". dasauri ta ɗaga masa kai ganin ransa a haɗe, ya kuma cewa "wai ma waye yace miki kiyi Aure?.." tayi saurin nuna Ayush da yatsa tace "Mommy ce..."
zaro ido Ayush tayi tana kallonta a ruɗe tace "Ni kuma Amriish? yaushe nayi miki maganar Aure?..." Junaid wani irin kallo yake watsa mata yace "yaro ai bazai yi ƙarya ba"
ta juyo da kallonta kansa tana faɗin "wallahi tallahi bani bace, taya zanyi musu maganar Aure bayan nasan har yanzu basu datu ba, du Da du yaushe aka haifesu balle nace zan sakasu a gaba nayi musu....". kafin ta kai ƙarshen maganar ta yayi saurin ɗaga mata hannu tareda cewa "ya isa haka banson long story.."
Ayush hararar Amrish take da gwala-gwalan idanuwanta tana mamakin yaushe yarinyar nan ta koyi ƙarya haka...
Amrish kamar zata fashe da kuka, ta nufi gurin Hafzat daman itace uwar É—akinta,
Amriish tafi kama da Ayush sosai kamar an tsaga kara, duk wata suffar ta irin na Ayush ce har tsayin gashi domin tafi little Angel sumar gashi, kuma tafi little Angel farin fata sosai duk da itama little Angel tanada haske amma bata kai Amrish haske ba,
Ita little Angel yanayin fuskarta irin na Junaid ne hatta launin haskensu, dan Junaid ko rabin É—auko farin Ayush baiyi ba,
Shi kuma Areeph duk wani hali na Junaid ya ɗauko su, kwata-kwata an rasa kamannin wa ya ɗauko acikin Sarki Raamud da kuma Baban Junaid wato Máahmud takwaran Areeph..

Junaid ne ya fara waige-waige yana faÉ—in "Ni ina Areeph ne?...". Ayush tace "yana É—akinsa.."
Yace "ha'a toh shi baya fitowa cikin mutane ne?.."
Little Angel tayi cabb ta tari bakinsa da cewa "Laaa Daddy shikam baya zama acikin mutane, daga É—akinsa sai cikin É—akinsa, kuma yana wasan game É—in harbi da bindiga a cikin computer sa..."
Junaid yace "kenam shima soja zai zama ...".
Little Angel ta kuma cewa. "ehh mana ai we are together me and him...". Yace "wow my Jaruma Ina yinku over, jeki ƙira mun shi oyaaah..." ta sauƙa akansa da gudu ta nufi ɗakinsa, tana zuwa ta tura ƙofar ɗakin ta shiga ta tarar dashi yanata wasan game ɗinsa na sojoji da ƴan fashi, juyowa yayi yana kallonta up and down rai a haɗe yace "ke Ni abokinki ne zakina shugo mun ɗaki babu excuse?..."
tace "toh Daddy ne yake ƙiranka..." yace "yi mun kneel down a wajen"
turo baki tayi tace "cab ɗin wallahi bazanyi ba kai Uba nane..." Areeph tasowa yayi a fusace yana zuwa gabanta ya talleta da mari da ɗan ƙaramin hannunsa, yana faɗin "Ni ba abokinki bane...".
Da gudu little Angel tabar ɗakin tana kuka hannu riƙe da fuska, tana zuwa falon tace "Daddy ya mareni..."
Junaid cike da mamaki yace "ya mareki kuma?..." sai a lokacin Ayush tayi magana tana cewa "daman ai nasan hakan zata faru, shifa Areeph baya barin kowa ya shigar mar É—aki sai iya Ni kaÉ—ai..."
suna cikin maganar sai gashi ya fito yana kuncume da fuska ko alamar dariya babu, yana zuwa ya nemi guri ya zauna, yana fuskantar Ayush yace "Mommy ke kike ƙirana?..". girgiza kai Ayush tayi tana nuna masa Junaid da yatsa baki ya gagara buɗuwa tsabar ƙunsar dariyar da take yi a cikinta saboda ganin yanda Junaid ya ƙafe idonsa akan Areeph ko ƙibtawa baya yi gaba ɗaya yaron ya bashi mamaki ganin yanda yake abu kamar babban mutum,
Areeph kallon Daddynsa yayi sannan yace "gani toh, sauri nake ina uzuri...". Junaid ne ya danƙwale shi tareda faɗin "dan ƙaniyarka uzurinka yafi ƙirana muhimmanci?.."
Girgiza kai Areeph yayi tareda cewa "a'ah shiyasa na bar uzurin nazo Ni ai...". jinjina kai Junaid yayi sannan yace "meyasa ka mari Angel?..". kawar da kai Areeph yayi gefe yana mutsil-mutsil da baki daƙer ya iya furta "ta raina Ni ne kuma a ƙarƙashina take...". Zaro ido Junaid yayi yace "kai kake iko da ita?..."
Areeph yace "eh mana Daddy saboda duk gidan nan nine namiji, ni kuma bazan jure raini ba zan iya murÉ—e musu wuya..."
sake baki Junaid yayi yana kallonsa,
Ayush kallon Junaid tayi tana tuna yanda shima yake maganarsa a baya Abu kaÉ—an sai yace zai murÉ—e wa mutum wuya toh gashi yaronsa duk ya É—auko irin halayensa da kuma yanayin maganarsa,
Jinjina kai Junaid yayi baiga laifinsa ba saboda shima yayi ire-iren waɗannan abubuwan, daƙer ya buɗe bakinsa yace "okay it's okay, daman tambayarka zanyi idan ka girma wani irin aiki zakayi ?..."
Areeph saida ya gama juye-juyensa da ɗagun kai saida yaɗau kusan mintuna tukun ya buɗe baki yace "Doctor.." ataƙaice...
Junaid yace "kenam a ƙarƙashin mata zaka ƙare?..." Areeph kallon Daddynsa yayi sannan yace. "ra'ayina na faɗa zan kuma iya canzawa idan naso..."
yana kaiwa nan bai tsaya sauraron abunda za'a ƙara cemasa ba ya tashi zai koma ɗakinsa, har zai haura stairs ya sake juyowa yace "nifa kar a sake shugo mun ɗaki, duk yarinyar data shugo kuma zan karyata ne...". ya maida kallonsa kan Ayush ya kuma cewa "mommy kizo ki mun wanka...". yana ƙarasa maganar ya fara ɗale stairs yankinsa daban ne, ba kowa ne yake zuwa wannan yankin ba sai Ayush kawai, ita zataje tayi masa wanka sannan takai masa abinci domin baya ci acikin mutane, idan lokacin tafiya makaranta ne haka Ayush zataje ta shirya shi ya fito su tafi makaranta, amma bayan makaranta baya fitowa daga cikin ɗakinsa,
Shikam Areeph har yaso yafi Babansa girman kai da jiji dakai da kuma É—agun kai...

Junaid kamar wanda aka watsa mar ruwan sanyi haka ya ƙafe a wajen, a tsorace ya kalli Ayush yace "anya ba ƴaƴan Aljanu kika haifa mun ba? especially Areeph du Da du how many years ?? Bai fa shiga shekara huɗu ba?...". a ruɗe yake wannan maganar idonsa akan Ayush,
Itama Ayush jiki a sanyaye ta tashi ta nufi É—akin Areeph ba tareda tace komai ba,
Girgiza kai yayi ya furta "impossible zan gyara shi, I'll make him a good parson..."
ya kalli su Little Angel da Amrish yace "Oyaah kuje É—akinku kuje ku kwanta ko, gobe akwai school...". tashi suka yi suka nufi É—akinsu suma É—akinsu yana can saman stairs...

Shima miƙewa yayi zai tafi ya kalli gurin da Hafzat take yace "ke ma Yakamata kije ki kwanta koh dare yayi ƙarfe 10 yanzu?.."
ta amsa masa da "toh"
har ta miƙe zata tafi ɗakinta ya tsayar da ita yana cewa "Judan yamun magana yace next week zai turo iyayensa daga nan zamu wuce dasu can garinku muje mu samu iyayenki akan maganar Aurenku, tinda har kin kammala karatun ki...."
Hafzat bata san lokacin data sau murmushi ba tace "toh Uncle Allah ya kaimu..." ta juya da gudu ta nufi É—akinta,
Shima Upstairs ya haura ya nufi É—akinsu...

Itama Ayush saida ta wanki Areeph ta shirya shi cikin sleeping dress ya ƙwanta akan gadonsa ta tottofa masa Addu'o'i tukun ta rufe masa ƙofa, kai tsaye ɗakin ƴan mata ta nufa suma taje ta gyaggyara musu ƙwanciya ta rufesu da mayafi sannan ta yi musu addu'o'i suma ta kulle musu ƙofa, daga nan ta nufi ɗakinsu,
tana zuwa ta tara da Junaid har ya shiga wanka, itama shiryawa tayi cikin kayan bacci ta haura saman gado, ba jumawa shima ya fito ya shirya sannan ya haura shima, anan aka fara love an daÉ—e ba'a haÉ—u ba, kowa yana kewar kowa,
Kashe hasken É—akin sukayi daga nan suka shige mayafi,

(Asmeetah kuma tayi ficewar ta, domin kar taga abunda zai hanata bacci🤪🤪)

★★★★★★
Chapter 72 · 0% Book details