← Book details Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 85

Sashe 29

Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin ihuuuu Munafurr yayi na azaba Junaid yana durƙushe ya fara ji suna girgiza, tsabar ƙarfin ihun Munafurr a gigice Junaid ya waiwaya yana kallon gurin da Munafurrr yake a tsaye yaga wani halittar Mutum ne ya caka masa takobi na tsafi ta bayansa, ga yanda takobin yake fidda farfatsin haske, zaro takobin yayi sannan ya ƙara datsa masa a saitin zuciyarsa still wannan takobin yana bada haske,
wannan mutumin ba kowa bane face *NARASIMHA* ga kuma Damusa shima yana tsaye ta gefen Narasimha,.
Junaid sake baki yayi yana kallon Narasimha cike da mamaki yana maganar zuci "wannan wani irin halitta ne shima? mutum mai kama da biri..."
Narasimha yana zare takobin Munafurr ya faɗi ƙasi ya durƙusa da gwiwowinsa,.
Narasimha ya kalli Junaid yace "ka tashi kazo ka cire masa kayi da hannayenka yaa Sarkin wannan masarautar na gobe...". Junaid ɗaukar takobi yayi ya riƙe sosai tareda tahowa da gudun gaske a fusace ya taka kafaɗar Munafurr yayi tsalle ya fille masa kai sannan ya dirƙo ƙasi yana huci,
Kayin Munafurr ne ya faɗo ƙasi, gangan jikinsa shima ya faɗi,
Junaid zuwa yayi wajen da kayinsa yake a yashe ya saita idanuwan Munafurr masu hatsari ya caccaka musu wuƙa, shikenam an gama da rayuwar Munafurr!
Narasimha yana kallon Junaid yace "ba dan wannan Damusan ba da bazaku samu tsira ba gaba ɗayanku, domin shi yake ajiye da wannan takobin mai tasirin gaske a gurinsa, wannan mutumin bazai taɓa mutuwa ba indai ba'a yi aiki da wannan takobin ba, na zo ni ne domin na kawo muku agaji yanzu kuwa zan tafi, zan koma daga yanda na fito saboda ba'a duniya nake zaune ba, kwanana ya daɗe da ƙarewa daga zaman nan duniya sakamakon rashin wannan takobin..." ya ƙarasa maganar yana nuna takobin hannunsa, ya fiddo da wani ƙaton littafi ya miƙawa Junaid yace "ga wannan karɓi.." Junaid ya karɓa sannan Narasimha ya cigaba da cewa "kaine magajin wannan masarautar, duk abunda kake son sani akan wannan masarautar toh wannan littafin ya ƙunshi komai a ciki, idan kanason yin tambaya to duk amsoshinka yana cikin wannan littafin, nasan baka san asalin mahaifinka ba to ka duba wannan littafin domin shine ɗan asalin mai asali, kakanka wanda ya haifi mahaifinka shine sarkin wannan masarautar shine wanda ya mulki mutanen wannan ƙasar, wancan mutumin wato sarki Raamud wanda kake ƙiyayya dashi shine ɗan uwan mahaifinka domin sun kasance ƴan biyun kakanka ne, yana da ƴa mace guda ɗaya wanda suka haifa shi da matarsa Sarauniya Bara'at wacce Allah ya karɓi rayuwarta a halin yanzu, Gimbiya Mayushaert wacce kake tareda ita a gida itace ɗiyarsu, wannan littafin ni na rubuta shi da hannuna daga farko har ƙarshen labarin zaka gani, da zarar ka kammala karanta tarihin labarin zan ɗauke littafi na domin ban gama rubutuna ba kuma bazan gama ba har ƙarshen rayuwarku, wannan littafin na biyu ne littafin na ɗaya yana gurinka cikin ɗakinka kaje ka duba zaka gani, ga kuma amanar Damusa ka riƙe shi a wajenka domin amanar kakanka ne, na Barka lafiya sarki na gobe...."
Narasimha yana kaiwa nan yayi ɓacewarsa ɓatt.
Har saida Junaid ya tsorita, gumi ne yake yanko masa zuciyarsa cike da tambayoyi da al'ajabi gaba ɗaya kansa ne ya kulle yana wani irin tunani tunani ya furta a hankali "kenam mahaifina ɗan masarautar wannan ƙasan ne? toh amma taya mutane zasu fahimci haka? kenam sarki Raamud ɗan uwan mahaifi nane shiyasa ya addabi rayuwata a baya kenam? to amma wacece ɗiyarsa Gimbiya Mayushart? shin aina take?...". zuciyarsa cike take da tambayoyi ga hannunsa riƙe da littafi, ɗago kansa yayi ya kalli damusar dake kallonsa shima sai kallon juna suke shi da damusa,.
Damusan ne ya tafo gaban Junaid ya tsaya shima Junaid sunkuyawa yayi ya ɗora hannunsa akan Damusan yana shafa shi, tsananin ƙaunar Damusan ne ya shiga zuciyar Junaid,
miƙewa Junaid yayi ya nufi cikin fadar masarautar, shi kuwa Damusan nufan gurin sarki Raamud yayi yaje ya kwanta a kusa dashi ya ɗora kansa akan ƙafarsa, duk abunda Narasimha ya sanarwa Junaid sarki Raamud yana ji saidai babu halin yin magana domin yana alhinin mutuwar sarauniyarsa...

Junaid yana shiga cikin fadar idonsa suka sauƙa akan babban photon dake manne a saman bango, zaro ido waje Junaid yayi da ƙarfi ya furta "Yushert..." yana girgiza kai yace "a'a ba ita bace amma kuma kamar dai ita ɗin ce, wallahi Yushert ce! itace wallahi Yushert ce!! daman tana da haɗi da masarautar nan? kenam itace Gimbiya Mayushart?...."
yana cikin wannan halin yaji ƙarar jirgaye, da gudu ya fice yayi waje yaga har sun buɗe get sun shugo, ganin sojojinsu ne suka zo yasa yayi ajiyar zuciya ya furta "Alhamdulillah"
Jirgaye ne sun kai ashirin suka zo kwasan matattun sojoji waɗanda aka rasa rayukansu, yana tsaye yana ganin an ɗauki Angel nan danan hawaye suka fara gangaro masa, haka yana kallon yanda aka ɗaga Bara'at yana tunanin "maiyasa ta zaɓi ta mutu akan ni na mutu? meyasa? Bayan nazo da niyar ɗaukan fansata akanta shine ita kuma ta bada rayuwarta akaina? kuma ga tsohon ciki a jikinta innalillahi wa inna ilaihi raju'un Allah ya gafarta miki na gode da sadaukarwarki agareni sarauniya..." Haka yake wannan maganar zuci har aka zo kan sarki Raamud yana ganin yanda aka ɗaɗɗaure shi da igiyar kaca saboda suna ganin shine mai laifin kuma shi aka kawowa farmaki, girgiza kai Junaid yayi yana kallonsa amma ya kasa ai watar da komai shidai acikin ransa yasan bazai taɓa bari a cutar dashi ba tinda yanzu ya shiryu kuma bayan haka mahaifi ne a waransa tinda ɗan uwan mahaifinsa ne,
Munafurr kuma a leda aka tuttusa ɗan banza suka yanke shawarin za'aje can bayan gari a ƙone shi..
Junaid yana tsaye yaji wani daga cikin sojojin yace "Captain Junaid sannu da ƙoƙari, naga kaji ciwo sosai muje cikin jirgi a duba maka raunin..."
Junaid ba tareda ya furta komai ba yayi gaba abunsa, yana dab da fita daga cikin masarautar yaji sojoji sun fitar da bindigunsu sun saita Damusa zasu harbeshi, a gigice Junaid ya É—aga musu hannu yace "ku dakata Please...."

******

Ɓangaren su Ayushert

Ayush ce take ta zirga-zirga a cikin ɗakinta zuciyarta sai faman harbawa take ga hawaye shaɓe-shaɓe akan fuskarta,.
tana cikin wannan zirga-zirgar sai ga mommy ta turo ƙofar ɗakinta da sallama a bakinta tana sanye da hijab ganin Ayush a wannan halin yasa ta faɗin "lafiya kuwa Ayush meyasa kike ta faman zarya a ɗakin ko abincin rana baki ci ba gashi yanzu anata ƙiraye-ƙirayen sallar Isha'i,
Ayush tafo wa gurin mommy tayi tana kuka tace "mommy ki taɓa zuciyata kiji zata fashe, bugawa take da ƙarfi hankalina ya kasa kwanciya inaji a jikina wani ya mutu..."
Mommy tace "ki kwantar da hankalinki Ayush Insha Allahu babu wanda zai mutu duk zasu dawo lafiya ƙlau..."
Ayush tace "a'ah Mommy sanyi nake ji na rasa wani ɓangare na jikina, akwai abunda ya faru, ba haka kawai ba..."

Wayar Mommy ce ta fara ringing a hannunta, ɗaga ƙiran tayi gabanta na faman tsinkewa tana gudun abunda za'a sanar mata, "kar kuma a sanar mun mutuwar yaro nah.." hannunta na kakkarwa tayi picking call tareda karawa a kunne tace "hello officer Sadik..." sanar mata yayi akan taje ta kunna tv domin ganin labarai akan yaƙin da aka gudanar,
"Amma Sadik Junaid fah yana nan lafiya kuwa?..." ya bata amsar cewa yana nan cikin ƙoshin lafiya sai raunikan da baza'a rasa ba...
daga nan hankalin mommy ya kwanta ta katse ƙiran tareda jan hannun Ayush tace "zo muje muga labarai..."
Bayan sunje sun sauƙa falon zama sukayi mommy ta kunna tv abunda suka fara ganin ana magana akai shine akan sojojin da suka gudu za'a sallame su a aiki sai lokacin da aka nemesu, gasu yanda akaita nuno photunansu har da Adity.
Mommy dariya tayi tana faɗin "yanzu Adity duk faɗanki har ki gudo a gun yaƙi."
Ita kuwa Ayush ko motsawa batayi ba balle ta murmusa fuskar nan ba Annuri ita kaÉ—ai tasan abunda take ji a zuciyarta,
A labarai aka nuno waÉ—anda suka mutu a cikin sojojin aka nuno photon Rumana wacce boom ya tashi da ita,
Mommy ta girgiza sosai dajin mutuwar Rumana har da hawayenta, daga baya aka nuno Angel har da photon gawarta,
Ba mommy ba hatta Ayush saida ta miƙe tsaye, mommy cikin firgici da tashi hankalinta a tashe tace "ehhhhh Angel ta mutu innalillahi wa inna ilaihi raju'un Angelll..."
Ayush kam fashewa tayi da kuka tana faɗin "Aunty Maryam innalillahi wa inna ilaihi raju'un Allah ya jiƙanki Aunty Maryam" cikin kuka Ayush take magana, can sukaji ance mutum ɗaya ne ya tsira a cikin sojojin!
Ƙirjin mommy ne ya buga da ƙarfin gaske domin tana tunanin Junaid ma ya mutu tinda ance mutum ɗaya ne ya tsira, itama Ayush dakatawa tayi da kukan tanason ganin wayene ya tsira kar taji cewa Junaid ɗinta shima ya mutu, gani sukayi an nuno photon Ogah Junaid, sannan anyi masa video gashi ga Damusa a gefensa,
Sunyi farin cikin ganin Junaid a raye, mommy tace "toh aina ya samu Damusa kuma?..."
Ayush gabanta ne yaketa faÉ—uwa kar ace an kashe mata iyayenta, amma ta gane Damusan mahaifinta,
Gani tayi an nuno videon mahaifinta an É—aÉ—É—aureshi da kaca anata jansa, ana sanarwa cewa an kamo babban mai laifi wanda ya gagari mutane....
Ayush hawaye ne ya fara wanke mata fuska ganin mahaifinta a cikin wannan yanayin,
Mommy miƙewa tayi tsaye tana zaro ido waje gani tayi sarki Raamud kamarsu ɗaya da mijinta wato mahaifin Junaid, kamar wanda aka tsaga kara hatta tsayin sumar kayinsu, shima mahaifin Junaid lokacin da yazo Nigeria haka sumar gashinsa yake daga baya ya aske,
Mommy ƙafarta ne ya fara kakkarwa ga hajijiyan da yake shirin ɗaukarta a hankali ta zauna akan kujera tana dafe da goshinta, ga hawaye yanda yake ta gangaro mata....

Ayush gani tayi an nuna photon Umanta da tsohon ciki a jikinta wai an kasheta,
A zabure ta tashi tsaye tana zazzarowa ido ta furta da ƙarfi cewa "Umaaa, wayyo Allah nah Umaaa na ta mutu sun kasheta, Junaid ya cuceni ya kashe mun mamanaaa...."
Chapter 29 · 0% Book details