← Book details Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 85

Sashe 42

Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Bayan isar su Junaid gida zama yayi a bakin gado yana karanta rubutun jikin takardar, abunda Ayush ta furta wa Junaid a yayin da yake bacci kafin ta tafi shi ta ƙara maimaita wa ajikin takardar!!
Junaid ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba har da ƙwallarsa a hankali ya furta "why Yushert meyasa zakiyi mun haka? ke da yarona bansan halin da zaku shiga ba, ya zama dole na nemoku a yanda kuke...."
tashi yayi ya fara tattara kayansa ya shirya duk wasu abubuwansa ya haɗesu a cikin jakarsa, sannan ya shiga wanka shaf-shaf ya fito yayi shirinsa a nutse, yana sanye da blue jeans da t-shirt mai zanen White and blue, da blue cover shoe a ƙafarsa, yana tsaye a gaban mirror yana taje suman kansa daya ƙwanta luf-luf zuwa kafaɗarsa, ga ya gyara sajen fuskarsa shima ya ƙwanta har gemunsa kamar wanda ya wanke da shampoo gashin yayi baƙi ƙirin ga laushi, farinsa kuma saiya ƙara fitowa sosai ba karamin kyau yayi ba, ɗaukan turare yayi mai shegen ƙamshi yana feshe duk ilahirin jikinsa dashi,
Daiden lokacin malam Lawan ya shugo da tray ɗin abinci a hannunsa ganin Junaid yanata shiri kamar wanda zai bar ƙasar yace "ha'a mutumin ina zuwa ne haka naga ka fitar da akwatuna lafiya dai koh?..."
Junaid ƙarasowa gaban malam yayi ya karɓi tray ɗin hannunsa ya ajiye a saman table ya ɗago yana kallonsa da damuwa a fuskarsa,
Malam Lawan kansa a ɗage shima yana kallon Junaid, domin Junaid ba ƙaramin tsayi ne dashi ba, duk da malam Lawan nada tsayi amma bai kai kafaɗar Junaid ba, asalin sangami ne ga ƙiran jikin ƙarfi, duk jikinsa a mummurɗe babu alamar tamowa ajikinsa😜
Yace "malam kayi haƙuri bazan iya zama anan gidan ba, inaso zan koma ɗaya daga cikin gidaje na, tin shekaran jiya nasa aka gyara mun gidan da zan zauna, saboda haka yanzu inaso zan koma ne, kuma acan ni kaɗai zan fi jin daɗin gudanar da aikina! Nagode sosai malam, ka bani kulawa yanda ya kamata..."
Malam yace "toh shikenam Junaid ba laifi amma kafin ka tafi ka zauna kaci abinci ko..."
taɓe fuska Junaid yayi sannan yace "gaskiya bana jin zan iya cin komai a halin yanzu, idan akwai milk shi nake buƙata..."
Malam Lawan da hanzarinsa ya nufi gurin tray É—in abinci yana faÉ—in "eh akwai mana bari na haÉ—a maka..."

*****

*AFTER 30 DAYS*

Ayush ce take tsaye a jikin bishiyan mangoro da wani dogon ice a hannunta sai faman tsalle take tana son ciran mango🥭, tayi nasarar ciran guda biyar ana shida ne ta soma jin gurnani ta bayanta, tsayawa tayi tana ƙoƙarin juyawa a hankali, idonta ne ya sauƙa akan wani ƙaton kura yana fuskantar ta,
a tsorace ta soma ja da baya juyawa tayi da gudun gaske shima kuran bin bayanta yayi yana binta da gudu itama gudu take har ta iso saitin ɗakin da take zaune tana zuwa ta ciri wani ƙaton mashi mai tsayin gaske kafin ta ankara kuran yayi sufa yakai mata yakushi, buɗe baki yayi zai kai mata cizo a gigice tayi ihuu tare da kai mashin nan cikin bakinsa ta caka masa har saida mashin ya fito ta bayansa, faɗuwa kuran yayi ta gefen ta yana shure-shure ga jini yanda yake fitowa ta bakinsa, itama Ayush ƙwanciya tayi ta gefen kuran tana maida numfashi hannunta kuma akan tumbin cikinta wanda ya fara girma tana jin yanda cikinta yake ta motsawa da ƙarfi tana jin raɗaɗin hakan jurewa kawai take idonta a lumshe,
Bayan ta ɗan huta kaɗan ta tashi ta maida mashinta yanda yake a ajiye sannan ta fara jan kuran nan har saida ta kaishi can nesa da ɗakinta ta jefashi cikin wani ƙaton rami ta juyo tana jan ƙafa daƙer domin ba ƙaramin gajiya tayi ba, zuwa tayi ta ɗauko mangwarayenta ta dawo ɗakinta,
Ayush haka take rayuwa a cikin dajin nan ita kaÉ—ai, duk ta cire tsoro da fargaba a ranta gani take zata iya tinkarar kowa duk wanda yace zai kawo mata farmaki mutum ko dabba,
Abincinta daga mangoro sai kashu sai kuma ayaba da wasu kayayyakin itacuwa wanda baza'a rasasu acikin jejin ba,
Ruwa kuwa tana kusa da rafi takan je ta É—ebo ruwa a cikin jarkan ta kawo É—akinta na kara,
cikin ɗakinta kuwa babu komai in banda bunannaki data haɗa gado dasu ta shimfiɗa mayafinta take ƙwana akai,
Ga cikinta kuwa yanzu yana 5months....

******

A ɓangaren Ogah Junaid kuwa ba yanda bai shiga neman Ayush ba amma ko labarin ta babu, cikin dare bai hanashi fita nemanta ba, haka ya ƙauracewa bacci saboda Ayush, ya shiga cikin damuwa sosai,
Haka sauran sojojin da akasa su nemo ta suma babu wani labari akanta,
Shi kaɗai yake zaune a gidansa babu kowa sai iya wani ƙarfaffan maigadi daya nemo sai kuma karnuka daya zuba a cikin gidan waran su uku irin buzajen nan na ƙasar waje,
gidane haÉ—aÉ—É—e wanda aka tsara shi, falon gidan ma abun kallo ne balle idan ka haura can upstairs mai hawa na biyar nan ne É—akin Junaid tsararren É—aki na alhurma,
(gaskiya idan nace zan tsaya tsara kyan gidan zamu ɓata lokaci ne...)
yana zaune a bakin gadonsa ya dafe kansa da hannu biyu yana kallon ƙasi duk abun duniya yabi ya isheshi, tunanin Dr Hasheem ne ya faɗo masa a rai wanda yake can a hannun sojoji a zabure Junaid ya miƙe tsaye yana faɗin "na manta da wancan mutumin tsawon wata guda yana headquarter ya kamata naje na sallame shi..."
yana kaiwa nan ya yi ficewarsa...

Doctor Hasheem yana zaune shi kaÉ—ai acikin gadurum na sojoji ya zama abun tausayi, duk wanda ya ganshi saiya zubar masa da hawaye,
Gaba É—aya an canza masa kamannunsa,
fuskan nan ya kumbura sosai! leɓɓerin bakinsa yayi dogo kamar bakin kare tsabar naushin hannun gardawa daya sha, idanuwansa sunyi fusu-fusu sun kumbura sosai don daƙer yake iya buɗe eyes ɗinsa, sun ƙaramce sunyi ciki sosai tsabar kumburi, gefen fuskarsa ɗaya yafi ɗaya kumbura ɗayan ɓangaren fuskarsa ta dama yanda kasan an hura filfila tsabar kumburi, hancinsa ya baje ya zama ƙatoto tsabar naushi,
wani irin rashin mutunci ma da suka tashi yimasa sai suka haske masa kayinsa gaba ɗaya sukayi masa malu tanɗal yanda kasan madubi haka kayin yake sheƙi ga sun faffasa masa kayi duk ya kumbura,
(Allah Sarki Dr Hasheem Allah zai saka maka wallahi😭😭)...
Chapter 42 · 0% Book details