← Book details Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 85

Sashe 65

Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Suna sauƙa falo suka tarar da kowa a zaune a kujerar falo ga Uncle Artaff shima yazo da matarsa Aunty Zainab da yaransa su uku, Junaid yana ganinsu ya fara sakin murmushi domin shi yanzu kamar bazai mutu ba tsabar farin cikin cikar ahalin mahaifinsa, gaba ɗaya gaggaisawa suka shiga yi ga mommy ga sarki Raamud suna zaune a kujera 3 seater saita ɗayan kujera kuma Judan ne sai kuma Hafzat dake zaune a ƙasan carpet, shima Junaid kujera ya samu ya zauna tareda faɗin "yanzu nake shirin zuwa muku ai..."
Uncle Artaff yace "wallahi kuwa ɗazu maimartaba ya ƙirani ai yake cewa akwai matsala agidan nan duk ya sanar mun abunda ke faruwa na Aurensa da Hajia...."
Mommy kallon sarki Raamud tayi ita sam bata san har ya sanar musu bama,
Junaid yayi murmushi kansa a sunkuye,
Ita kuwa Ayush dinning ta wuce ta zauna tareda tsiyayan ruwan tea duk tana jin abubuwan da suke faÉ—i, ji tayi Junaid yace "Ni wallahi so nake ace zuwa gobe an É—aura Auren mommy da Abbah..."
dasauri ta burtsar da shayin data kurɓa tareda zaro manya-manyan idanuwanta tana kallon yanda Junaid yake,
Mommy tace "a'ah yayi sauri ai My son"
Junaid yace "ohh soyayyar wajen bata ƙare ba kenam?..."
Duk suka tintsire da dariya suna wasa da dariya a tsakaninsu, Sarki Raamud yace "daman matsalar akan Ɓingel ɗina ne bansan meye matsalar ta ba, kwata² bata son Auren nan, shine nake so a bincika mun ita ko akwai wani abu aranta ne..."
Junaid yayi saurin cewa "meye abunda yake ran natan wanda zai hana Aurenku? kawai ku rabu da ita daman zaman da tayi a daji Aljanu sun shafeta shiyasa kuka ga tana wasu abubuwa kamar mahaukaciya..."
Mommy tace. "Aljanu kuma?..."
yace "sosai ma Aljanu ne na masifa acikin wannan dajin, nima na gansu da idona balle ita da tayi watannu a wajensu, kuma akwai wani malamin daya tabbatar mun da cewa Yushert tana da Aljanu na rashin ji da fahimta, sun ɗanso su taɓa mata ƙwaƙwalwa, kawai kar ku biye mata..."
ya ƙarasa maganar tareda kallon wajen da take, itama ido ta zazzaro tana masa wani irin kallo, acikin ranta kuwa cewa take "tabb ɗin amma Yaya Junaid ba ƙaramin raina mun wayo yayi ba wallahi, kenam zaisa su rinƙa mun kallon mahaukaciya alhalin babu komai a jikina, toh wallahi Auren nan bazan bari ayi ba, zan hura wa Abbana wuta ne har saiya haƙura da maganar Auren aikin banza kawai, yaushe aka taɓa yin haka surkuwarka ta zamo matar ubanka mttssw..."
Uncle Artaff yace "toh amma meyasa baka sanar mana haka ba tin abaya? ai da mun tashi tsaye akanta..."
girgiza kai Junaid yayi sannan yace "yanzu ne abubuwan suka fara bayyana..."
Mommy tace "Allah sarki my daughter insha Allahu za'a nema mata magani, ga zaman da tayi a prison Sam banji daÉ—in haka ba, shiyasa gaba É—aya nake ganinta a fizge..."
Sarki Raamud kawai yana jinsu ne amma yasan Ɓingel ɗinsa bata da wasu Aljanu, domin tin lokacin da aka haifeta yayi mata wani sihirin da ba wani Aljani ko Aljanar da zata raɓeta ko ta cutar da ita ko kuma ta tsoritar da ita, duk Aljanun da sukayi gigin raɓan jikinta zasu iya ƙonewa, wannan sihirin yana nan a jikinta kuma haka shima kansa,
kuma duk mai Aljanu indai Sarki Raamud ya ganta saiya san tanada akwai, saboda ya zauna dasu kuma yanada alaƙa sosai dasu, kamar ita Hafzat yana ganinta yasan tanada Aljanu akanta amma saidai Aljanunta ba masu cutarwa bane shiyasa baiyi magana akansu ba, Aljanunta masu yawan ibada ne haka kawai tana cikin bacci zasu yanke mata baccin ta tashi tayo alwala taita salloli, kuma lokacin sallah yana yi bata barin lokacin ya wuce zata tashi tayi ga yawan azumi da tasbihi kuma intaji anyi karatun Alkur'ani sau ɗaya a gabanta zata riƙe a ƙwaƙwalwarta yanzu sauƙar Alkur'ani Hafzat sau biyar, tayi na waresh sannan tayi na hafs, shu'uba, ƙalun, warshu, durii, susii, ƙumbul, bazzii, ibni kasiir, duk tayi sauƙa akan su ...

Ayush kifar da kanta tayi akan table tana kuka jin yanda ake ta janyo mata Aljanu an É—auketa mahaukaciya,
tana cikin kukan taji Abbanta yace "Ɓingel Abba zo mana..."
tana jinsa amma ko motsi batayi ba, ya sake ƙiranta taƙi amsawa nan ma! Junaid ya juyo yana kallonta cikin ɓacin rai yace "ke ba magana ake miki ba?..."
ɗagowa tayi tana kuka ta taso kamar mai tambayar ƙasa da haka ta ƙaraso cikin falon fuska duk tayi ja da idanuwanta, tsayawa tayi ta kasa zama saida Abbah ya sake yi mata magana yana ƙiranta cikin lallami yace "zo ki zauna anan maza Ɓingel Abbah..."
zuwa gurinsa tayi ya riƙo hannunta ya zaunar da ita a tsakiyar su shi da mommy, tallafo fuskar Ayush mommy tayi ta juyo da ita suna fuskantar juna tace "Ayush ki dubi fuskarki yanda duk ta kokkoɗe lokaci guda? dan Allah ki sanar mana meyake faruwa dake, idan bakya son Auren nan ki sanar mana mu zamu san yanda zamuyi, muna buƙatar ganin farin cikin ki..."
kuka Ayush take ta juyar da kanta gefe gaba É—aya ta rasa meyake mata daÉ—i a ranta, Uncle Artaff ne shima yayi mata magana yace "Ayshert ki faÉ—a mana meyake damunki ne haka?.."
Junaid yace "ku rabu da ita kawai.." Uncle Artaff yace "a'a ka barmu da ita kawai dole musan ƙwaƙƙwaran hujjarta na cewa bata son Auren ."
Ayush hararar Junaid tayi tareda cewa "wai kai Uba nane kam.." ciki-ciki tayi maganar ba tareda sunji abunda tace ba saidai sunji kamar tana gunaguni,
Junaid kallonta yayi cikin rashin fahimta yace "me kika ce?.."
duk babu wanda yaji abunda tace sai mommy da Abbah dake a gefe da gefenta suke, murmushi mommy tayi tareda sunkuyar da kanta tana murza zoben yatsanta,
Uncle Artaff yace "kaga Junaid ya isa haka, yakamata kana sanyaya zuciyarka kaga matarka ce kar ka shiga hakkinta..."
sannan ya dawo da ganinsa kan Ayush ya kuma cewa "ehen muna jinki Ayshert..."
tana motsi da lips É—inta kamar mai yin magana tace "babu komai.."
Hafzat tana zaune a ƙasan carpet tana tunanin dalilin da yasa Ayush bata son Auren nan kuma alhalin abun farin ciki ne...
shi kuwa Judan tashi yayi yabar falon ganin tattaunawa ne akan ahalin gidan bai shafeshi ba, bayan ya bar wajen itama Hafzat tashi tayi zata tafi kasancewar maganar manya ne, har ta fara tafiya mommy ta ƙirata tareda faɗin "Judan ya manta earpiece ɗinshi ɗauka ki kai masa, saida Hafzat taji rass a zuciyarta saboda tasan naci irin na Judan yanzu saiyace zai tsayar da ita, ɗauka tayi jiki a sanyaye ta nufi part ɗinsa...
itama Aunty Zainab tura yaranta tayi akan suje suyi wasa..

Uncle Artaff yace "Ayshert magana muke miki meyasa bakya son Hajia Fateema ta raɓi mahaifinki? Alhali ta temake ki a rayuwa ta baki gata, ta nuna miki soyayyar gaskiya, ta riƙe ki tamkar mahaifiyarki, inda ace cutar dake zatayi toh da tin farko bata kawoki gidanta ta zamar dake mutum ba,
da farko kinsa musu wuta a gida kuma kinsan Hajia Fateema tana gidan kinyi niyar ki ƙonata Allah kuma ya kawo mata agaji, idan ace wata ce da tinin kun raba hanya domin zata ɗauka ke maƙiyiyarta ce amma mai? saita danne hakan a zuciyarta ta gagara cireki a ranta kuma ta cigaba da zama dake, ta ɗauke ki tamkar ɗiyar data haifa a cikinta amma ke baki ɗauketa a matsayin mahaifiya ba, ganan yaronta shi da yake ganin mahaifiyarsa ce ai koda wasa bazai taɓa gigin cutar da ita ba,
kinzo kinyi nadama daga baya munji mun karɓi tuban ki amma meyasa yanzu kuma abun ƙaruwa da farin ciki yazo mata kuma kike mata ƙyashin samunsa ko hassada da baƙin hali! kenam kin nuna mata cewa ke butulu ce kenam? kuma a hakan mijinki zaiso ki bayan yasan bakya son mahaifiyarsa? Ehhh...."
ya ƙarasa maganar cikin fushi yana zazzaro mata Ido domin Uncle Artaff bai taɓa shiga ɓacin rai irin na yau ba, koda a baya datasa wuta a gidansu ma ransa ya sosu amma bai nuna mata ba saboda a lokacin basu san alaƙar da ke tsakaninsu ba,
Daman can Uncle Artaff (malam Lawan) ya fi su zafin rai sosai kuma zai fito ya gayawa mutum magana koda ran mutum zai ɓaci,
mai sanyin zuciya daman Máahmud ne baban Junaid shi wannan mai haƙuri kenam ko kaɗan bashida matsala, kuma ba'a taɓa samun wanda akace yayi faɗa dashi ba,
Sarki Raamud kuma shi saidai mugunta, duk wani aikin mugunta ya iya shi tin yana yaro, amma yanzu kam Masha Allah ya daina wannan muguntar nashin...
Chapter 65 · 0% Book details