← Book details Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 85

Sashe 21

Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tace "Junaid kenam ai Ayush tafi sonka ma akan son da kake mata sai dai abu ɗayane yasa yanzu bata kula dakai shine ƙuntata mata da kake yi kana nuna mata zafin nama wanda duk son da take maka zata janye ne, tsorone ya hanata ayi muku baiko a wancan lokacin kuma kana dukanta taya zata amince da kai..."

Junaid ya ɗan sauƙe numfashi yana murmushi yace "koda ta amince dani ma bazan Aureta ba..."
Mommy tace "saboda mai kenam?.."
ya juyo yana kallon mommy yace "saboda batada asali kamar yanda nima banida asali toh amma gwara ni ai tinda ina da ke kuma ansan dangin mahaifiyata...."

Mommy jikinta ne yayi sanyi jin abunda Junaid ya faÉ—a, É—agowa tayi tana kallonsa wanda shima kallonta yake, bata ankara ba taji ya sake jifanta da wata tambaya "shin su waye dangin mahaifina? sannan aina suke? meye asalinsu? duk bakisan wannan amsar ba, kawai kin Auri mutu bakisan ko shi wayene ba, baku tsaya kunyi bincike akansa ba, kunyi abunda yanzu nine nake jin zafinsa!
kuma haka kikeso ki sake aikata kuskuren da kika aikata a baya? kina so na Auri wacce ba'a San asalinta ba, koda danginta baki saniba, kinaso na Aureta Æ´aÆ´ana suzo suna kukan gorin da ake musu cewar ba'a San asalin dangin mahaifin ubansu ba haka kuma ba'a San asalin dangin uwarsu ba, haka kenam zasu tashi da wannan takaicin?
hatta Æ´an uwanki ba sona sukeyi ba saboda basu san waye mahaifina ba, suma kansu Æ´an uwanki gori suke mun balle azo cikin gari kan abokai da sauransu...."

Mommy tana zaune kamar wanda ruwa ya cinye, bakinta har wani kakkarwa yake maganganun Junaid sun ƙona mata rai tace "Junaiddd ka dakata haka, duk da ba'a San ko waye mahaifinka ba amma shi ɗin mutumin kirki ne, yanada kyakkyawan zuciya wanda hakan yasa mahaifina ya damƙa masa amana ta saboda yasan zai kula dani, kuma Alhamdulillah tinda mukayi Aure har muka haifeka har mahaifinka yabar duniya bamu taɓa samun matsalar zamantakewar Aure ba, har yau ban taɓa yin danasanin Aurensa ba, hakan ma ka gode wa Allah tinda shi yayi sanadiyar zuwanka duniya, koda bashi na Auraba ba lalle ne kazo duniya ba saboda wani baya taɓa haifan ɗan wani, bazaka taɓa fitowa daga cikina ba saidai na haifi wani daban domin kai ɗin jinsin mahaifinka ne, saboda duk wanda yasan mahaifinka toh tabbas idan an ganka anga suffarsa...."
Mommy ta ƙarasa maganar tana sharar hawaye,
ta cigaba da cewa "Junaid bazaka taɓa tozarta ba a duniyan nan Insha Allahu koda bayan rai nane domin wannan dukiyar da muke sarrafa shi ya faro asaline daga mahaifina wato Alhaji Junaidu kafin rasuwarsa ya mallaka mun dukiyarsa da mahaifinka domin iya mu biyu kawai yake gani kuma ya yadda da mu duk da niɗin dole dukiyarsa nawa ne saboda ni kaɗai ya haifa,
dukiyata dana mahaifinka amfanuwarka ne na kai É—aya...."

Junaid ne ya katseta da cewa "pleaseee Mommm it's okay ni ba maganar dukiya nake buƙatar ji ba, inason sanin su waye dangin mahaifina, daga wata ƙasar ya fito..."

Mommy tace "Junaid abunda kake son sani nima ban saniba, abunda na sani akan mahaifinka shine mahaifina ya haɗu da mahaifinka ne a titi yana yawon neman aikinyi saboda abincin da zaici ma gagaransa yake, wata rana mahaifina yaje office ɗinsa dadaddare yana kan hanyar dawowa gida kwatsam saiga ɓarayi sun tareshi kuma alokacin yana tareda maƙudan kuɗaɗe na kamfani wanda zaiyi kimanin Billion 100 acikin akwati, ɓarayin nan sun so su illata mahaifina sannan su karɓe kuɗin sai Allah ya turo mahaifinka a yawace-yawacensa yazo wajen ganin abunda ake shirin aikatawa ne yasa yazo da gudu ya ceci mahaifina sannan yayiwa ɓarayinnan dukan gaske wanda har kasa tashi sukayi daga ƙarshe aka ɗauke su aka kaisu hannun hukuma,
toh daga wannan lokacin ne mahaifinka ya shiga zuciyar mahaifina har ya ɗora shi akan kasuwancinsa, ansha tambayar asalinsa amma ya kasa gaya mana sakamakon ciwon mantau daya haɗu dashi duk ya manta daga inda ya fito, amma zubinshi ba ɗan Nigeria bane, irin bahindiyawan mutanen nan ne anfi tunanin daga ƙasar India yake, amma sai dai har yanzu ba'a gano ba har yabar duniya..."

Junaid tsayawa kallon mommy yayi bayan ta kammala bashi labarin abunda ta sani ya turo ɗan ƙaramin bakinsa yace "Hmmm matsalar ƴan Nigeria kenam shikenam daga temakon da yayi muku sai kawai ki Aure shi?..."

Mommy tashi tayi tana faÉ—in "your very stupid Junaid, bari naje kitchen domin nasan yunwa kake ji shiyasa ka kasa fahimta ta.."
Har zata fita ta sake juyowa da sauri tace "Junaid bakayi sallar mangarib ba gashi har ana ƙiran Isha'i, why Junaid?
please kaje masallaci banson sallarka a gida..."
tana kaiwa nan tayi ficewarta...

Shima tashi yayi ya nufi toilet zai É—auro Alwala...

Kitchen mommy ta shiga ta haÉ—a mana haÉ—aÉ—É—en girki!
Abinci kala biyu ta girka kowa ta dafa masa abunda ransa yake so,
Shi Junaid indai a night lunch ne yafi son sakwara da miyan ugusi da kifi haka Angel ma ra'ayinsu yazo iri É—aya,
Mommy kuma ita da Ayush sunfi son tuwon shinkafa da miyan ƙwai ko jar miya 😋😋😋😋😋

Junaid ne ya dawo daga masallaci zama yayi a falo yana kallon labarai, ta ko wani tasha labarin zuwa yaƙi ƙasar California ake, ana nuno photon Sarki Raamud a tv, sannan aka dawo nuno photunan sojojin da zasuje yaƙin! kowani ƙasa ana zaɓan sojojin da zasuje,
Aka zo kan sojojin Austaraliya Junaid yana ganin yanda aka nuno photon Rumana, murmushi kawai yayi tareda girgiza kai shi inda ason ransa ne da baza'ayi yaƙin nan da mata ba, domin a tunaninsa mata babu abunda zasu iya sai shirme da kuma suzo suyita ihu a mutane,
gani yayi anzo kan sojojin China, nan ma yaga an nuno photon Aditi dariya yayi a fili yace "gwara ke Sarkin faÉ—a..".
Bayan su sai aka nuno sojojin ƙasan da za'ayi yaƙin wato California Army aciki har da Angel ɗinsa lokaci guda kuma sai yaji tausayinta duk da Angel commander ce amma bayaso a tafi yaƙin nan da ita domin ita ɗin tanada rauni sosai ba kamar su Aditi ba,
Anan ana wuce ƙasashen sojojin da zasuje har aka zo kan ƴan Nigeria,
tsuka Junaid yayi yana faɗin "Nigeria Army kam ba abunda zasu iya, ni ban taɓa ganin ragwayen sojoji irin na nan Nigeria ba wallahi, sai gadarar aita jefar da bindigu suna guduwa..."
gani yayi an nuno photonsa ana sanar da cewa shine na É—aya acikin jaruman sojojin Nigeria,
tsuka yayi ya tashi yana faɗin "banson shirme, kuna wani ƙirana da jarumi wato so kuke azo mun ta baya a hallaka ni kenam..."
yabar kallon ma ya nufi dinnig table sabo ƙar dashi saboda a yau ɗin nan aka kawo shi wancan table ɗin Junaid ya dagargaza shi...
Zama yayi yana ƙiran Mommy tareda cewa "Ni har yanzu ba'a kammala girkin bane.."

Mommy ce ta fito É—auke da kulolin abinci ta jejjerasu,
É—agowa tayi tana kallon agogon É—akin, da sauri tace "na shiga uku ina yaran nan suka shiga ne?.."
Junaid yace "ina suka je ne?.."
tace "wallahi ban saniba, tinda rana suka fita gashi yanzu har ƙarfe 10..."
Junaid yana kallon kular abinci yace "Mom yunwa nake ji, ai ba ɓata zasuyi ba..."

Mommy tace "Dan Allah Junaid kafin ka fara cin abincin kaje ka nemo su mana..."
Junaid ya ɗago yana kallon Mommy tareda faɗin "whattt sorry I can't leave my food, ai su ba ƙananun yara bane da har sai an fita nemansu, idan sunada hankali ai da sukaga dare yayi sai su dawo gida..."

Mommy tace "toh ai su basuda hankali sai an nemo su.."
Junaid yace "toh su kwana acan indai ni zan nemo su.."

Mommy zatayi magana kenam ya katseta da cewa "Please Mom am hungry, wallahi idan nabar abincin nan toh na basshi kenam zan kwana da yunwa ne..."
Mommy tace "toh toh gashi ka fara cin abincin tukun saika je ka dubo mun su, idan ka gansu a hanya ka daka mun su..."

ta ƙarasa maganar tareda zuba masa abincinsa a plate, yace "toh shikenam kije ɗakina ki buɗe wardrobe zakiga dorina ki ɗauko mun, yau zasu raina kansu tinda yawo zasu koya..."
Mommy kallonsa take tace "toh bari na É—auko.."
a cikin ranta kuwa cewa tayi "tab wannan ai kaine sarki zalimun É—in..."
ta nufi upstairs tana takawa har ta iso É—akinsa...

Gari kuwa hadari ne ya haɗu sosai lokaci guda kuwa aka fara ruwan sama da ƙarfin gaske don ko yayyafi ba'ayi ba, irin ruwan nan mai haɗe da iska ake yi,
Junaid yana cin abinci haka ya ƙara kallon agogo yanzu har 10:30 kuma ruwa ake sosai, ɗaukan wayansa yayi yana dialling call number Angel wayar ce take ringing har ta katse ba'a ɗauka ba,
tsuka yayi ya ajiye wayarsa a gefen table har ya kammala cin abinci ya zauna kamar mai yin tunani...

Mommy ce itama ta sauƙo down stairs hannunta riƙe da dorinar da Junaid yace ta ɗauko, tsayawa tayi ta jingina da jikin gini gaba ɗaya ta shiga damuwa,
kallon yanda Junaid yake a zaune tayi tace "gashi anata ruwan sama kaima ba halin fita, na ƙira wayar Angel shuru bata ɗauka ba Allah dai yasa lafiya.."
Junaid ne ya kalli Mommy yace "shine kika shiga damuwa haka?..."
Junaid yana rufe baki sai suka ji an turo ƙofa da ƙarfi, da gudu Angel da Ayush suka shugo cikin falon duk sunyi jirib sai haki sukeyi kamar waɗanda sukayi gudun tsere...

Mommy sake baki tayi tana kallonsu tama rasa bakin magana,
shima Junaid kallonsu kawai yake yi,
shine ma ya fara yin magana yace "daga ina kuke?.."

Angel tana fitar da numfashi daƙer tace "wallahi motar mu ne ta ɓaci mana a hanya, tin daga teepa garage muke tafe da ƙafa har muka iso gida, babu abun hawa ko ɗaya..."

Mommy tace "toh ina zakiga masu abun hawa acikin ruwan nan ga dare yayi yanzu sha ɗaya saura, na ƙira wayanki no picking kuma kafin ku fita saida na tambayeku ina zakuje baku gaya mun ba, wani irin hauka ne wannan..."
Chapter 21 · 0% Book details