Sashe 47
Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Bayan kwana biyar da yankewa Dr Hasheem hukuncin zaman gidan prison na tsawon shekara 25 akan yiwa yarinya fyaÉ—e...
a ranar da aka kai Dr Hasheem prison a ranar Maimoon ta santalo kyakkyawan yaronta, amma saidai mahaifinta yayi fushi da ita ko amsa sallamarta bayayi da zarar tazo yanda yake, haka idan ta gaishe shi baya amsa mata, amma saidai yayi halacci ɗaya daya siyo ƙaton rago yace a yankawa jariri sanna kuma shi ya bada umarni a sanyawa jariri sunan mahaifin Dr Hasheem wato Abubakar, Maimoon taji daɗin haka sosai saboda ko ba komai ya nuna yana son yaronta, Maimoon ta saka wa yaron sunan inkiya wato "Rapeekh", saidai ba'ayi wani hidimar suna ba...
yayin da shi kuma Dr Hasheem yana can cikin mawuyancin hali shi kaÉ—ai kamar wani marar gata haka yake zaune yayi tagumi yanata nazarin abubuwa, gaba É—aya duk ya rarrame ya fita hayyacinsa, suturar dake jikinsa irin na Æ´an cikin prison ne kowa an rubuta masa number a bayan rigarsa...
******
Shi kuma Junaid ya kulle kansu a cikin gida saboda sojojin da suke yo masa zirga-zirga akan ya bada Ayush su tafi da ita amma sam yaƙi, yanzu baya fita aiki saboda wannan matsalar, koda yaushe suna cikin ɗaki a manne da juna yauma kamar kullum suna ƙwance akan gado a yayin da ita kuma Ayush take kwance saman ƙirjinsa, tace "Yayana.." ya amsa mata da "na'am ƙanwata ya akai?.." ɗagowa tayi ta zauna tana fuskantarsa tace "meyasa ka kasa cika alƙawari?.." shima idonsa akanta yana cije leɓɓen sa yace "Alƙawarin mai?.." ɗan turo baki tayi a shagwaɓe tace "ka ɗaukarwa sojojinku Alƙawarin zaka kaini gurinsu da hannunka yanzu kuma yau kusan sati guda suna binka amma kaƙi sauraronsu ka kashe wayanka gaba ɗaya, ai baka kyauta musu ba koh kuma zasu ɗauke ka maƙaryaci marar cika alƙawari kuma suna ganin girmanka..". ajiyar zuciya Junaid ya sauƙe yana lumshe ido yace "Yushert a halin yanzu bana ƙaunar rabuwa dake, bansan wani hukunci zasu yanke miki ba, bazan iya barinki ina ji ina kallo su hukunta ki ba..."
Ayush katse shi tayi da cewa "amma baka ganin abunda kayi zai iya shafar aikinka?..." yana kwance saida yayi jinkiri kaɗan kafin ya bata amsa da cewa "sosai ma hakan shi yafi sauƙi saboda na karya doka, bayan haka shuwagabanni nane suke son ganina amma naƙi zuwa, banaso wani abu ya taɓaki Yushert ga kinada juna biyu..."
kuka Ayush ta fara yi ta riƙe hannun Junaid duk biyun tana faɗin "dan girman Allah Yaya Junaid kada ka shiga matsala saboda ni, ka ɗauke ni ka kai musu ni kamar yanda kayi musu alƙawari, ni inada tabbacin babu abunda zasuyi mun na zalunci, hukunci ɗaya ne shine nasan za'a kaini kotu ne, kuma nasan duk hukuncin da za'a yanke mun a kotu baza ayi mun yanzu ba dole sai an bari na haihu tukun, ka kwantar da hankalinka, haka kaddara ta tazo mun, kuma kowa baya tsallake ƙaddararsa saboda haka dan Allah ka tashi muje mu gurin aikin nakun, dan Allah badan ni..."
shima binta da kallo yake kamar zaiyi kuka yace "Yushert ki barni dasu kawai".
"a'ah ni kawai ka tashi muje mu, idan ma bakaje ba ni zan kai kaina..." tana ƙarasa maganar ta tashi da sauri ta nufi wardrobe ta zaro hijab ɗinta har ƙasa, ta sanya sannan ta fidda hannayenta waje ga ciki kuwa ya fito sosai...
tashi yayi shima ya tsaya a gaban ta yana jinjina kai yace "shikenam tinda kin dage akan saina kaiki toh amma ki sani duk wanda yayi kokarin cutar mun dake wallahi wallahi saina ɗauki ƙwaƙwaran hukunci wanda kare ma bazai shanshana ba...". yana kaiwa nan ya riƙo hannunta ya kuma cewa "muje mu." yana janta a haka suka sauƙa falo shi kuwa yana sanye da baƙar jallabiya a jikinsa, suna fita out side na gidan suka shiga motar a hankali ya karya ƙwana sannan ya miƙi hanyar gate, kafin ya iso mai gadin ya buɗe musu suka fice da gudu..."
*****
A sashin mommy Kuma kulawa iya kulawa tana samu agurin sarki Raamud, ga mata zaƙa² dake mata ayyuka, ko ƙwaƙƙwaran motsi mommy tayi sai sun tambayeta ko akwai abunda take so, ga ta ɓangaren sarki Raamud shima babu abunda zata nema ta rasa, wani ƙyakykyawar alaƙa ne a tsakaninsu duk da har yanzu babu maganar soyayya a tsakaninsu amma kana ganinsu kasan akwai ƙauna, yauma kamar kullum tana zaune akan dadduma dake wajen lambu a bayan masarauta ta ɗan shigingiɗa kaɗan tana riƙe da apple a hannunta har ta ci rabi, a gabanta kuma ƙaton paranty ne yana ɗauke da kayan fruits a ciki duk anyi slaces ɗinsu, ga kuma kuyange a wajen su biyar suna taya mommy hira, wasu suna mata tausa wasu kuma suna zazzaune kawai, dake suma ƴan aikin suna son kasancewa da mommy domin tanada son mutane, bata son zama ita kaɗai, suna cikin hira saiga mai martaba sarki Raamud ya shugo filin lambu dake fakaice guri guda, yana zuwa ƴan aikin suka tashi suna gaishe shi tareda ficewa daga wajen, shima zama yayi akan daddumar yana fuskantar mommy da murmushi a fuskarsa yace "Rankiya daɗe sarauniya na gaisheki..." murmushi tayi itama ta tashi zaune tace "haba mai martaba nifa ban zama sarauniya ba..." dariya yayi yace "ai kin zama mah" ta ɗago tana kallonsa tace "taya kenam?..". yace "saboda kema jinin masarauta ce..". zaro kyakkyawar idanuwanta tayi tace "o-oh o-oh! yara nane jinin sarauta bani ba, ban haɗu da masarauta ba" sarki Raamud ido kawai ya kafa mata da ƙyakykyawan murmushinsa yace "gashi kuwa yanzu ta dalilin yaranki kin zamo ƴar sarauta..."
dariya tayi tana kawar da fuskarta gefe, yace "amma fah kinyi kyau sarauniya, alkebbar tayi miki kyau.." da sauri ta jawo mayafinta tana rufe fuskar, hannu yasa yana ƙoƙarin buɗe fuskar har yayi nasarar janye mayafin, ta sunkuyar da kanta ƙasi cikin jin kunya tace "dan Allah ka daina, mu ba yara ba..."
yace "yaran to me suka iya in banda shirme, ai iya soyayya sai tsofi.."
zaro ido mommy tayi tace "soyayya kuma?.." shima jin abunda tace ne yasa shi sosa ƙeyarshi yana faɗin "a'ah badai soyayya ba, wasa nake miki" tace "ohooo yanzu naji batu..."
daga nan kowa yayi shuru babu wanda ya ƙara ce wa kowa komai, shi sarki Raamud tunaninsa ya zai fara sanar wa mommy cewa yana sonta, kuma gashi yana da burin Auranta, shi ason ransa ko yanzu ta amince masa zai iya sawa a ɗaura masa Aure a gobe domin har sauran masarantu sun fara complain akan wai sarki Raamud yana zaune akan mulki ba mata, su a tsarinsu duk wanda zai zauna akan mulki sai yanada matar Aure, ansha kawo masa ƴaƴan sarakuna akan ya zaɓi matar Aure amma yaƙi zaɓa shi idonsa nakan mommy Kuma ya kasa sanar mata, a tunaninsa bazata yadda bane,
itama mommy gaba É—aya hankalinta yana kan sarki Raamud, ganinsa take kamar mijinta, a duk lokacin da suka fake guri É—aya kamar yanzu sai tayi tunanin kamar da mijinta take tare, har mantawa take da mijinta ya mutu saboda ganin sarki Raamud take kamar shi, domin kamar su É—aya sakk kamar an tsaga kara, a duk lokacin da take kallon sarki Raamud bata sanin Lokacin da murmushi ke zo mata, kuma saita tsinci kanta a cikin farin ciki, ga kulawar da take samu a wajensa,
amma wasu lokuta idan ta tuno da yaranta saita ji ba daɗi a ranta, yanzu ma Junaid da Ayush ne suka faɗo mata arai, sarki Raamud ganin hawaye a fuskar mommy ne yasa shi firgita da sauri yasa hannu ya tallafo kanta yana faɗin "sarauniya lafiya kuwa? meya faru dake kodai na ɓata miki ne, dan Allah kiyi haƙuri! ki sanar mun abubuwan da bakyaso da kuma abunda kike so, ni kuwa insha Allahu zanyi ƙoƙarin ganin na faranta miki.."
murmushi tayi ganin yanda ya rikice akan ta, ta ɗago tana kallonsa tace " a'ah ba abunda kayi mun, kawai dai ina tunawa da yarana ne, bansan a wani hali suke ciki ba, dan Allah inaso naje garesu..." Sarki girgiza kai kawai yayi ba tareda yace komai ba, sai bayan ya ɗanyi jinkiri tukun yayi ajiyar zuciya yace "kuyi haƙuri sarauniya, insha Allahu zaki gana dasu! inaji ajikina suna nan cikin ƙoshin lafiya.."
mommy ɗagowa tayi kamar zata fashe da ihu tace "ni kawai inason sanya su a cikin idanuwana" murmushi yayi yace "shikenam ki ƙwantar da hankalinki zuwa end of the month zamu tafi Nigeria tare...". sai a wannan lokacin mommy tasau ƙayataccen murmushi ta ɗago suna kallon juna...