← Book details Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 85

Sashe 34

Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mommy ta sauƙar da ajiyar zuciya tana kallon sarki Raamud tace "toh kenam kai baza kayi Aure ba? naga akwai part-part ɗin ɗakuna acikin masarautar nan sun kai 10 kuma manya-manya..."

Murmushi sarki Raamud yayi sannan yace "ehhh acikin part ɗin ɗakunan zan zaɓi ɗaya na zauna a ciki kafin rai yayi halinsa ba tareda matar Aure ba, domin ni na rigada na yanke cewar bazanyi Aure ba har ƙarshen rayuwata..."
ya ƙarasa maganar yana kallon mommy, itama ya tambayeta cewar "ina kema a cikin masarautar nan zaki cigaba da zama da yaranki?.."
Murmushi tasau tace "eh kamar yanda kaima kace haka nima zan zaɓi ɗaki ɗaya na zauna ni kaɗai, daman tinda mijina ya rasu na yanke cewa ba wanda zan Aura..."

Narasimha duk tattaunawar da sukeyi a junansu yana jinsu, yayi gyaran murya sannan yace "idan kun gama shiriritar takun ni zan koma yanda na fito kafin na sake dawowa..."

Sarki Raamud ne yayi saurin miƙewa sannan ya durƙusa ƙasi tareda haɗe hannayensa biyu yana roƙan Narasimha akan ya zauna dasu,
"Dan Allah Baba Narasimha kayi haƙuri ka cigaba da zama a tare da mu, inason ka kasance tareda mu domin zakana bamu duk wata kariya kuma zaka warkar mana da jinyar da ya gagare mu indai bana ajali ba, dan Allah..."
Narasimha yace "a'ah Raamud bazan iya zaman duniya ba, tafiya zanyi can wajen da nake zaune.."
Sarki Raamud hawaye ne suka cicciko masa yace "Baba Narasimha ka tuna fa mahaifina ya baka amanar mu, kar ka tafi ka barmu tinda yanzu ruhinka ya komo jikinka da temakon Damusa..."

Jikin Narasimha ne yayi sanyi yace "toh shikenam zan zauna daku...."
Daman akwai É—akin Narasimha da ban wanda aka tanadar masa, É—akin da ba kowa ne yake shigansa ba...

Sarki Raamud yayi farin cikin jin abunda Narasimha ya faÉ—a yace "Nagode Narasimha amma yanzu inaso kayi mun wata alfarma É—aya..."
Narasimha yace "meye matsalar?.."
Sarki Raamud yace "Damusa nake so ya zauna dani, na tabbata a can Nigeria duk wanda yaga Damusa zaiyi ƙoƙarin tserewa ne, kuma kaga Damusan daman na masarauta ne, bazaiji daɗin zama a wajen Junaid ba.."
Narasimha yace "wannan gaskiya ne, zaman Damusa Sujjur a cikin masarauta shine zaman lafiyansa domin shi ba kamar sauran Damusa bane, abincinsa da ban ne, don haka yanzu zanje na É—auko Damusa Sujjur..."
Narasimha yana kaiwa nan ya ɓace ɓatt...

********

Lailah tana zaune a harabar gidansu akan kujerar roba tana waya tana faÉ—in "kinga Maimoon ya zaki cemun kinada ciki? bayan sau É—aya akayi amfani dake..."
Ata ɓangaren Maimoon kuwa cewa tayi "Laila nidai na gaya miki shi Allah babu ruwansa da sau ɗaya akayi, ciki ne Allah ya bani bansan ya zanyi ba, kuma muddin Daddy nah yaji wallahi saiya ɗauki ƙwakkwaran hukunci, gashi yanzu cikin har ya soma fitowa amma ban yadda an gane ba har yanzu..."

Lailah tace "yanzu cikin zaije wata nawa?.."
Maimoon tana kuka tace "yanzu fah yana shirin shiga wata na Bakwai.."
Lailah ta zabura tace "innalillahi wa inna ilaihi raju'un, Maimoon ciki ai ya girma, kin kusan haihuwa, toh yanzu ya za'ayi? wallahi kinyi sakaci Maimoon meyasa tin da baki sanar mun ba sai yanzu, ai da an zubar yanzu kuwa babu halin zubar wa..."
Maimoon tana kuka tace "toh yazanyi, meye mafita.."

Lailah juyowa tayi zatayi magana kwatsam sai taga Junaid yana tsaye ata bayanta, shi kuma Malam Lawan yana cikin motarsa bai sauƙo ba,
Gaban Lailah ne ya yanke ta dafa ƙirjinta tace "innalillahi wa inna ilaihi raju'un nashiga uku.."
Junaid yace "kinga babu ruwana da tattaunawar da kikeyi da munafukan ƙawayenki, shin ina Yushert?.."
Lailah hannunta na rawa ta nuna cikin falo tace "tana ciki.." juyawa yayi ya nufi ciki,
Lailah ce ta kara wayarta a kunne tace "kinga Maimoon zamuyi magana daga baya..." ta katse ƙiran tabi bayan Junaid da gudu...

A ɓangaren Maimoon kuma bayan ta sauƙe wayarta tana kuka sai ji tayi an turo ƙofa, da sauri ta ɗago tana kallon Ammy wacce ta shugo da hawaye shaɓe-shaɓe akan fuskarta,
Maimoon a tsorace tace "Ammy meyasa kike kuka?.."
Ammy ta taho gurin Maimoon tana kuka tasa hannu ta cire dogon hijab É—in Maimoon, saiga tumbin ciki har ya fito sosai,
Bazaka taɓa gane Maimoon tanada ciki ba indai ba lura kayi sosai ba, saboda kullum a cikin ɗakinta take, bata yadda taje falo saidai Ammy ta kawo mata abinci kuma kullum da hijabi a jikinta,
Anyi Anyi da ita amma taƙi fitowa cikin mutane, hatta mahaifinta shima yayi har ya gaji sun ƙyaleta..
Ammy ganin ciki a jikin Maimoon yasa taja baya da sauri tareda dafe ƙirjinta tace "nashiga uku Maimoonnn? yanzu abunda yake tare dake kenam? kike ɓoye mana? yanzun ma ji nayi kina waya da Lailah shiyasa na sani amma inbadan haka ba saidai idan naƙuda ne ya tarar dake, nashiga uku nah, yanzu har ciki yayi wata bakwai a jikinki ban saniba Maimoon?..."

Maimoon tana kuka tareda faɗin "dan Allah Ammy kuyi haƙuri ku gafarce ni, nasan nayi kuskure da ban sanar muku ba, inajin tsoron Daddy, bansan ya zanyi ba Ammy..."

Ammy itama kukan take tace "Maimoon waye ne ya miki ciki?..."
Shuru tayi Maimoon ta gagara bada amsa sai kuka,
Ammy ta sake yin magana tace "magana nake miki Maimoon ki ban amsa mana.."
Maimoon murya na kakkarwa tace "nima ban saniba Ammy, bansan inada ciki ba sai da naga ya fito.."
Ammy tace "kodai mutanen da suka sace ki ne suka É—irka miki cikin?..". Maimoon tana kuka tace "ehh sune.."
Ammy cikin damuwa tace "Insha Allahu za'a É—auki mataki akansu"
daganan Ammy tayi waje cikin ɓacin rai..

******

Junaid yana shiga cikin falo ya tarar da Ayush zaune tana fuskantar plasman ita kaɗai, juyowa tayi ta kalli wanda ya shugo ganin Junaid yasa ta miƙe tsaye da sauri tana kallonsa,
saiga Lailah itama ta shugo, kalle kalle suke yiwa junansu ba wanda ya kula kowa acikinsu, daga baya saiga malam lawan shima ya shugo ganin Ayush yasa shi faÉ—in "Ayshert daman kina nan a raye? taya kika bar gidan nan?.."

Ayush fashewa tayi da kuka ba tareda tace musu komai ba,
Junaid ne yazo gabanta ya tsaya suna facing juna yace "ki gaya mun gaskiya taya akayi gidan mu ya kama da wuta kuma mahaifiyata tana ciki?.."
wani irin kallo Ayush ta watsawa Junaid tace "wannan wani irin tambaya ne? shin inda nima na ƙone a ciki zaka samu kayi mun irin wannan tambaya ne?.."
Junaid kallonta yake cike da mamaki bai taɓa tunanin Ayush zata iya bashi wannan amsar ba, yace "shin kina farin cikin mutuwar mahaifiyata?."
kallon cikin eyes É—insa take ta maida masa amsa da cewa "kamar yadda kaima kayi farin cikin kashe mun mahaifiyata ba..."

Ba Junaid ba hatta malam lawan dake tsaye shima ya girgiza da jin kalaman Ayush, cikin ɓacin rai Malam Lawan yace "ke Ayshert wani irin magana kike yi haka ne?..."
Ayush ta kalli Malam Lawan sannan tace "malam wannan Junaid shine wanda ya kashe mun mahaifiyata da tsohon cikinta, kuma bazan taɓa yafe maka ba, mungu azzalumin bawa..."
Junaid idonsa ne sukayi jawur tsabar baƙin ciki ga duk ya fita hayyacinsa yace "Yushert a lokacin da nake tambayarki shin wacece ke, kasa bani amsa kika yi, shin meyasa kika ɓoye mun kanki? duk da baki gaya mun ba naji kuma an sanar mun ko ke wacece a guri na, ko ba komai nasan tushen mahaifina kuma na gano su waye ƴan uwana, Yushert ko ba soyayya zanyi alfahari dake a matsayin ƴar uwata kuma jinina, mahaifiyarki kuma bani na kasheta ba, ta ceci rayuwata ne...."
Kafin ya ƙarasa maganar Ayush ta kai hannu ta zabga masa mari asaman fuskarsa,
Lailah ce tayi wani irin firgita tasa hannu biyu ta toshe bakinta tana zaro ido waje,
Shima Doctor Hasheem dake bakin ƙofar ɗakinsa a tsaye saida ƙirjinsa ya buga,
Malam ne yayo kan Ayush yana faÉ—in "kin haukace ne Ayshert, shin kinada hankali kuwa?..."
Junaid haka yake bin Ayush da kallo cike da mamaki ya kasa aikata komai,

tana kuka tace "Ni ba abunda zaka gaya mun Junaid, ka riƙe ɗan uwantakar ka domin ni yanzu babu wata alaƙa dake tsakanin mu, na tsaneka wallahi bana ƙaunar ganin fuskarka, ka kashe mun mahaifiyata sannan kazo kana mun wani banzan shirmen maganarka,
zan gaya maka gaskiyar magana shine kamar yanda ka hallaka mun mahaifiyata toh haka nima na dasa gobara a cikin gidanku munyi two zero kenam, nima saidai ka kashe ni..."
tana ƙarasa maganar ta rufa da gudun gaske ta shige ɗakin da take tasa sakata...

Junaid jin furucin Ayush yasa yayi baya zai faɗi yana dafe da goshinsa Malam Lawan yayi saurin riƙoshi ya rungume shi sosai a jikinsa, haka jikin Junaid yake ɓari yana kakkarwa sosai ga duk gumi ya wanke masa ilahirin jikinsa, haka ƙirjinsa yake ta faman bugawa da ƙarfin gaske,
Malam Lawan shima kamar a mafarki yake jin kalaman Ayush domin yayi matuƙar tsorata sosai da abunda Ayush ta aikata kuma bata ji fargaban faɗa ba...
wani irin ihu Junaid ya rausa ya durƙusa ƙasi da gwiwowinsa yana dukan ƙasa da hannayensa biyu da ƙarfin gaske, yana ihu kamar ransa zai fita..

haka Malam Lawan yake rungume dashi a ƙasi yana rarrashinsa, kamar zaiyi kuka haka yake ji,
Doctor Hasheem shima yana tsaye yayi matuƙar tausayawa Junaid, Lokaci guda kuwa yaji Ayush ta fita masa arai kwata-kwata, a wannan lokacin ba ƙaramin haushi ta bashi ba,
Lailah itama fashewa tayi da kuka ta nufi É—akinta da gudu,
tana zuwa ta zauna a bakin gado tayi dialing call number wata mutumiyarta ƴar jarida, bugu ɗaya kuwa ta ɗauki ƙiran,
Da sauri Lailah ta kara a kunne tana faÉ—in "Hello Sumaiya kina inane?..."
A ɓangaren Sumaiya kuwa cewa tayi "ina wajen aiki mana.."
Lailah tace "toh kar ki bar wajen gani nan zuwa akwai tattaunawar da zamuyi, kuma hanyar samun kuÉ—in ki.."
Sumaiya tace "Allah yasa rahotanni zaki kawo mun tsararru.."
Lailah tace "maganar akan Doctor Fateema ne, gobarar da ya tashi da ita ba haka kawai bane, yarinyar gidan ce ta ƙoneta, yanzu haka tana gidan mu.."
Chapter 34 · 0% Book details