← Book details Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 85

Sashe 36

Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lailah bata koma gida ba sai waran ƙarfe 10 na dare saboda ta wuce gidansu Maimoon domin jin wasu matsalolinta, ta shiga damuwa sosai ganin halin da Maimoon take ciki ga kuma cikinta ya fito sosai, tana kuma tausayawa Yayanta idan maganar nan ta fito...
shugowa cikin falo tayi ta tarar da Ayush zaune a one seater tana kallon tv sai kuma Doctor Hasheem a 3 seater, zuwa tayi zata wuce É—akinta da sauri Doctor Hasheem ya katse mata hanzari tareda faÉ—in "baki iya sallama ba koh?.."
tsayawa Lailah tayi ba tareda ta juyo ba tace "nayi mana sai dai baku jini ba.." tana wani kumbura domin ta tsani ta tashi taga Ayush a cikin gidan nan, gaba É—aya bata da wargi..

Doctor Hasheem ya kuma cewa "ina kika je?.."
Lailah tana turo baki tace "gidansu Maimoon" ƙirjin Doctor Hasheem ne ya buga an fame masa ciwon dake zuciyarsa, cije leɓɓen bakinsa yayi yana jinjina kai tareda kallon Ayush wacce idonta akan tv, yace "Okay kije kitchen ki haɗowa Ayushert tea mai kauri ki kawo mata tana jin yunwa..."
Juyowa Lailah tayi tana faɗin "Yaya kafin nabar gidan nan fah nayi girki, ai bai kamata ace abincin har ya ƙare ba saboda nasan ba baƙi akayi ba.."
Doctor Hasheem yace "ehh ta cinye yanzu kuma tana buƙatar ruwan tea kafin ta kwanta idan kuma bazaki yi ba, Ni zan shiga kitchen na haɗo mata.."
Lailah kamar zata rausa ihu tana jumping da ƙafafuwanta tana gunaguni tace "wannan matar akwai shegen ci kamar mayya, tinda tazo gidan nan girki sau biyu zuwa uku nakeyi tsabar cinta yayi yawa, munafuka kawai..."
haka ta nufi kitchen tana wannan maganganun ba tareda Doctor Hasheem ya jiyota ba, amma saidai Ayush duk taji abunda ta ce,
Doctor Hasheem jin gunagunin da takeyi ne yasa shi faÉ—in "Lailah kina magana ne?.."
tace "a'ahh..."
Bayan minti talatin saiga Lailah ta fito hannunta ɗauke da cup na ruwan shayi da haɗin madara, tana zuwa gaban Ayush ta miƙa mata,
a cikin zuciyarta kuwa cewa tayi "Æ´ar buro uba na watsa miki dai akan fuska, acici mala'ikun tauna.."

Ayush tana murmushi tasa hannu ta karɓa tareda cewa "yauwa ƴar ƙanwata godiya nake.."
Lailah wani irin harara ta watsa mata ba tareda ta ganta ba sannan tayi wucewar ta É—akinta tana kumbura kamar filfila,..

******

Around 11:00pm Junaid yana ƙwance a saman gadonsa yana kallon ceilling sai murmushin yake shi kaɗai ga kuma katin Auren su a saman ƙirjinsa, fuskan Ayush ce take masa gizo, sai kuma yake tunowa da abunda ya faru a tsakanin su kafin ya tafi yaƙi,
lokaci guda kuma ya tuno da Mommynsa saiga wani irin zazzafan hawaye yana faman gangaro masa, yana cikin wannan tunani-tunanin har bacci yayi awon gaba da shi...

_________________Lailah ce ta tashi cikin dare ta fito falo sanye da sleeping dress riga da wando ta nufi frig ta É—auki lemon juice kai tsaye É—akin Doctor Hasheem ta nufa tana zuwa ta fara knocking a hankali har sai da tayi sau uku tukun yayi magana tareda faÉ—in "waye?.."
Lailah tace "Ni ce dai Yaya.."
bai sake yin wata magana ba sai ji tayi ya buɗe mata ƙofa ya juya ciki, itama bin bayansa tayi ta samu ɗaya daga cikin kujerun ɗakin ta zauna tana shan lemonta,
Doctor Hasheem kallon agogon ɗakin yayi yaga kusan ƙarfe 12 na dare yace "meyasa kika tashi a cikin wannan daren?.."
Lailah tace "daman ai ina tashi shan lemo ko cin Apple saboda yunwan dare ke damuna.."
kallonta Doctor Hasheem yake cikin takaici yace "kuma sai akace kizo ki takura mun a wannan daren?..." turo baki Lailah tayi sannan tace "haba Yaya amma dai kasan bana zuwa maka a cikin dare ko? yanzun ma matsala ce ta kawo ni..."
yace "matsalar bazaki bari saida safe ba?.."
tace "yoo Yaya da safe ka tafi gurin aiki kodan yanzu an bada hutun asibitin koh? sakamakon mutuwar mai asibitin da aka kasheta, yanzu kullum kana tareda da wancan yarinyar taya zan samu lokacin zama dakai har mu tattauna akan matsalar...". ta ƙarasa maganar tana murguɗa baki tareda zuƙan lemonta,
Doctor Hasheem kallonta kawai yake yana mamakin iyeyi da kinibibi irin na Lailah ga kuma bakin mayar da magana tana yarinya ƙarama, wanda yanzu take shirin shiga 19years old,
girgiza kai kawai yayi yace "Allah ya shiryeki Lailah, yanzu dai meye matsalar daya kawo ki bacci nake ji..."

tana kora Æ´ar lemonta hankali kwance tace "Daman maganar shine akan Maimoon tana da tumbi.."
Doctor Hasheem cikin rashin fahimta yace "bangane Maimoon tanada tumbi ba, kowa ma ai yanada tumbi..."
Lailah tana lumshe ido tace "ehh amma ai ba kamar namu ba, ita nata na musamman ne..."
Doctor Hasheem yace "kinga bana son shirme fah idan bazaki gaya mun magana ba ki tashi ki tafi.."
miƙewa tayi tana faɗin "a'ah Yaya ba saika koreni ba, zan gaya maka yauwa, daman Maimoon tanada tsohon cikinka..."
zaro ido waje Doctor yayi yace "ban fahimta ba.." Lailah juyawa tayi zata fita tareda cewa "toh shikenam Yaya karka fahimta randa ta haihu kam ai zaka fahimta koh, idan nan ma baka fahimta ba saika jira isowar motar police a cikin gidan nan zakafi fahimta da kyau..."
kafin Doctor Hasheem ya ce wani abu har ta fice da sauri ta nufi ɗakinta, Doctor Hasheem yana tsaye idonsa a bakin ƙofa tin lokacin fitar Lailah yanata maimaita maganar Lailah akan Maimoon tanada tsohon ciki, nan danan kuma gumi ya fara tsirto masa yana furta "ciki! ciki kuma? Maimoon daman akwai ciki? Innalillahi wa inna ilaihi raju'un..."
A wannan lokacin kwana yayi bai rintsa ba, yanata tunanin Maimoon....

Itama Ayush tana can ɗakinta tana zaune ta kasa yin bacci, daga ta ƙwanta sai taji murɗa, gaba ɗaya ta fita hayyacinta tsabar yawan Amai, kuma komai taci saita amar tana cin abinci zata amar dashi hatta ruwa idan tasha baya zama mata a ciki, shiyasa take yawan jin yunwa har Lailah tana mata gorin yawan cin abinci,
Yunwa ne ya gama isarta haka ta tashi ta fito falo kai tsaye kitchen ta nufa taje ta haɗo kakkauran shayi da biredi ta fito ta koma ɗakinta, zama tayi a bakin gado tana cin bread ɗinta da shayi ko rabin ci batayi ba wani irin murɗa ya hautsino mata, da gudun gaske ta nufi toilet bayan ta ajiye kayan bread akan mirror, amai takeyi bana wasa ba, kamar zata amar da kayan cikinta haka take ƙwaƙulo amai,
Idanuwanta ne sukayi zuru-zuru ga wani irin hajijiyan da yake É—ibanta, fashewa tayi da wani irin matsanancin kuka tana faÉ—in "wannan wani irin masifa ne da bala'i, wai kam meyake damuna haka ne, duk abunda naci saina amar dashi, toh kenam haka zanyi rayuwata ba tareda naci komai ba, wayyo Allah nashiga uku..."
haka take magana cikin kuka duk ta rarrame ta kokkoɗe ta gama tuttujewa, haka ta wanke bakinta tana tafiya tana laluman jikin bango tsabar hajijiyan da take ji, daƙer ta shiga bedroom ta faɗa akan gado rubda ciki tana kuka, ai kuwa saiga wani aman ya tunkaro maƙogaronta, wani irin hautsinawa tayi daga saman gadon ta faɗo ƙasi tana rarrafe ta shige toilet, a wannan lokacin kam a ƙasin tiles tayi aman domin bazata iya miƙewa tsaye ba, cikin natan nan kamar wanda aka yashe komai, tsabar yunwar da take ji, ga tumbin cikinta har ya ɗan soma fitowa amma duk bata gane cewar ciki bane gashi har na tsawon 4months,
zama tayi a cikin toilet daga taji amai saita kwara shi a wajen, da haka har bacci ya É—auketa a zaunen ta jingina bayanta a jikin bango, kayinta a sama da haka take baccin,
cikin ya hanata cin abinci sannan ya hanata ƙwanciya, daga tayi ne sai Amai koda bazata amar da komai ba haka zata rinƙa kakakin Amai,
tana zaune a toilet tana bacci jikinta har wani kakkarwa yake ga wani zazzaɓin da yake damunta, jikinta duk ya ɗau zafi, har wani canza colour tayi tsabar azaba launinta ya koma yellow......

*TOH PAH 🤣🤣🤣 ALLAH SARKI AYUSH HAR KIN BAN TAUSAYI WOLLAH...*

𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️

𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔

the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅

𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️

𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871

*💫💫{{N W A}}💫💫*

Book two

C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 43 ➡️ 44

Bayan sallar Asuba da sassafe sai ga motar Junaid a ƙofar gidan Doctor Hasheem, buɗe murfin motar yayi ya fito da hanzarinsa hannunsa riƙe da katunan Aurensu, buga gate yake da ƙarfin gaske,. daga ciki ne maigadi yace "waye ne fisabilillahi da sassafen Allah" ya ƙarasa maganar yana buɗe gate ɗin! ganin Junaid ne yasa shi washe baki yana faɗin "ahoo ashe yallaɓai ne, sannu da zuwa" bai ƙarasa maganar ba Junaid ya bangaje shi tareda shige wa ciki, da gudun gaske ya ƙarasa zuwa cikin gidan yana zuwa nan ma ya fara buga musu ƙofar falo, har saida ya buga kusan sau biyar kafin yaji motsin mutum,
Doctor Hasheem ne ya buÉ—e yana yamutsa fuska yace "lafiya kuwa Junaid da sassafe kazo gidan mutane?.."
Junaid ne yake masa kallon up and down sannan yace "ina matata?.."
Doctor Hasheem cike da mamaki ya maimaita cewa "matarka kuma? aina kenam?.."
Junaid ne ya zuciyo ya cabki ƙwalar rigar baccin Dr Hasheem yana faɗin "nace ina matata Yushert? kayi kuskuren zama mun da mata a cikin gida ɗaya Doctor Hasheem, Yushert she's my wife don haka ka bani waje naje na ɗauko matata.."

Doctor Hasheem jin abunda Junaid yake faɗi ne yasa shi kwashewa da dariya yana nuna shi da yatsa, dariya kuwa yaƙi tsayuwa har wani kama ciki yake, daƙer ya tsagaita dariyar yana faɗin "shin ka haukace ne Junaid? taya Ayushert ta zamo matarka? kodai a daren jiya kayi mafarki ne toh kuwa idan mafarki kake gwara ka farka domin a halin yanzu Ayush tafi ƙarfinka, yanda ta tsaneka a rayuwa ai kana sanar mata cewa ita matarka ce zuciyarta bugawa zatayi..." ya ƙarasa maganar yana dariya yatsarsa akan Junaid yana nuna shi..
Chapter 36 · 0% Book details