← Book details Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 85

Sashe 31

Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Junaid mafarkin da yake yi ne yasa baiji ƙiran da akeyi a wayarsa ba,
yana cikin bacci bakinsa yana motsi a hankali yake furta "Yushert! Yushert!! Yushert!!! Please kar ki tsaneni, har yanzu ina kan sonki kuma bazan daina sonki ba har abada...."
Ayush tana tsaye a gaban Junaid wanda bayansa wani ƙaton rami ne mai zurfin gaske, tana ta kwashewa da dariya haɗe da tafa hannayenta biyu tana shewa ga bindiga a hannunta, lokaci guda ta tsayar da dariyan tana wani irin kallo na ƙasƙanci tace "kayi kaɗan Junaid kai babban maƙiyi nane kuma bazan taɓa yafe maka akan laifin da ka aikata mun ba, rayuwarka a tafin hannuna yake, idan kaga na yafe maka toh kasheka nayi, kar kayi tunanin zan ƙyaleka, saina ɗau fansar jinin mahaifiyata da kuma abunda ke cikinta...."
Junaid durƙusa wa yayi a gabanta yace "indai haka shine daidai agareki to Bismillah zaki iya kasheni yanzu, amma inaso ki sani soyayyarki bazata taɓa zamowa ƙiyayya ba acikin zuciyata inasonki Yaushert..."
Kafin ya rufe baki ta harbeshi a kafaɗarsa ta kuma saita kayinsa ta harba cikin rashin sa'a iya bullet ɗaya ne a cikin bindigar, cikin takaici ta wurgar da bindigar gefe tana faɗin "kash naso ace na dagargaza maka ƙwaƙwalwa wallahi, idan ka furta mun kalmar so ji nake kamar ana ƙara rura mun wuta a cikin zuciyata, ganin kalmar nake tamkar mutuwata, na tsani kalmar soyayya sannan na tsani mai yin soyayya, Junaid mutuwarka hutu ne a gareni kuma samun nutsuwa ne a gareni..."
Junaid yana riƙe da gurin da ta harbeshi yana kukan zuci idonsa akan Ayush wacce take tsaye akansa ko Annuri babu a fuskarta, idonta tsantsar ƙiyayya ne acikinsu buɗe baki tayi tace "kayi haƙuri ka gaida mun mahaifiyata da kuma ɗan uwana dake cikinta...." tana kaiwa nan tasa ƙafarta ta cankeshi yayi baya ya faɗa cikin wannan ƙaton rami mai zurfin gaske....

A ruɗe Junaid ya farka yana ihu tareda ambatar sunan "Yushertttt..." yana maida numfashi sama-sama ga gumin da ya wanke masa fuska, wani irin haɗiyar yawu yayi ga zazzaɓin da ya rufeshi ya ƙanƙame sai rawar sanyi yake tayi....

******

A wannan daren misalin ƙarfe 2 da rabi Ayush tana tsaye a bakin gate ɗin gidan Doctor Hasheem tana ta faman bubbugawa tana kuka, jin motsin mutum yasa tayi shuru da yin kukan, ji tayi an tambaya cewa "waye ne?.."
cikin sassanyar murya tace "Ni ce..."
maigadi yace "ke wa?.." tace "Ayushert.."
yace "ok ki jira toh mai gidan ya fito ya buÉ—e miki domin bazan mutu ni kaÉ—ai ba wollah.."
maigadi ne ya fara hura wusir da ƙarfi, cikin lokaci ƙalilan sai ga Doctor Hasheem ya fito cikin rigar bacci yace "wai meyake faruwa ne?.." cikin muryar jin bacci yake magana,
Maigadi yace "daman Ogah wata mata ce take jiranka a waje..." cikin mamaki yace "wata mata kuma? a wannan daren? shin daga ina take?..."
maigadi yace "a'ahhhh ban saniba aradu..."
tafowa Doctor Hasheem yayi yazo ya buɗe gate baisha wahala waran ganeta ba saboda akwai hasken nepa ta wajen, gabansa ne yayi matuƙar faɗuwa cike da mamaki yake binta da kallo, baki na kakkarwa yace "Ayushert! ke daga ina?.."
Fashewa tayi da matsanancin kuka..."
girgiza kai yayi sannan yace "Junaid ko?.."
yasa hannu ya jawota ciki sannan ya karɓi akwatin hannunta yajata suka nufi cikin gidan...

A falo suka zauna tana kuka duk ta kwashe labarin ta gayawa Doctor Hasheem,
jinjina kai Doctor Hasheem yayi sannan yace "kiyi haƙuri Ayushert haƙiƙa Junaid bai kyauta miki ba, bai kamata ya kashe miki iyaye ba, amma kema inaso ki sani komai ana binsa ne akan tsari duba da yanda kema iyayenki sukayi masa, shi wannan fansa ya ɗauka kema kinsan Junaid baya yafiya, amma duk da hakan yayi rashin imani gaskiya yasa hannu ya kashe mata mai ciki haihuwa yau ko gobe innalillahi wa inna ilaihi raju'un, dole kema bazaki yafe masa ba, banga laifinki ba Ayushert, ki ɗauki duk hukuncin daya dace ki ɗauka ina goyon bayanki, sannan zaki cigaba da zama damu acikin gidan nan..."

Ayush tana kuka tace "a yanzu na ɗauki fansata akan mahaifiyarsa shima ya ɗanɗani raɗaɗin dana ɗanɗana..." ta ƙarasa maganar fuska a haɗe...

Doctor Hasheem yana kallonta cikin rashin fahimta yace "ban gane mai kike nufi ba? kar kiyi kuskuren É—aukan fansarki akan Mahaifiyarsa domin tayi miki halacci sosai a rayuwa kuma ita batada wata matsala..."
Ayush juyowa tayi tana kallon Doctor Hasheem a fusace tace "kenam niɗin mahaifiyata matsala take dashi yasa ya ɗauki rayuwarta? mahaifiyata batada wani masoyi daya wuce Junaid, kullum maganar ta akan Junaid ne, mahaifiyata bata taɓa sa hannu ta mareni ba sai akan Junaid, shin sakayyar da zai mata kenam? uwa bata fi uwa ba, haka uba baifi uba ba, kamar yadda ya sheƙe mun mahaifiyata haka shima mahaifiyarsa yau za'a wayi gari itama ta sheƙa, sai mu zama marayu da gaske..."
Doctor Hasheem haka yake bin Ayush da kallo gaba É—aya ta sauya masa, ba Ayush É—in daya sani a baya bane, yana tunanin a ransa cewa "Anya kuwa wannan Ayush ce? ina tunanin Aljana ce tazo mun a suffar Ayush...." daga nan ya fara tsorita da ita domin kalamanta sun girgiza shi,
yana cikin wannan halin yaji ta ce "shin kana mamaki ko? kar ka damu ni ɗin ce Ayush, abunda akayi mun ne yasa zuciyata ƙaiƙashewa nima, kuma muje zuwa gaba shima Junaid saiya bar Duniyan nan, da hannuna zan kashe tsinanne la'ananne, ban taɓa yadda cewa soyayya takan zamo ƙiyayya ba sai yau kuma akaina..."
jikin Doctor Hasheem ne yahau rawa daƙer ya buɗe baki yace "shin mai kika aikatawa mommy?..."
kafin ya rufe bakinsa yaji wayarsa tana ring-ging a saman table É—in tsakiyar falon,
Hannunsa na kakkarwa ya ɗauki wayar ganin number hospital ne yasa ƙirjinsa bugawa da ƙarfin gaske yayi picking tareda karawa a kunne, ba tareda yayi magana ba yaji ance "Doctor Hasheem kayi saurin zuwa gidan Doctor Fateema gidanta duk ya cinye da wuta kuma mun rasata a cikin gidan, ko ina ya ƙone yayi ƙurmus, ga Oga Junaid baya ƙasan, kuma an hanamu ƙiransa mu sanar masa, dan Allah kai ɗin kazo ance mutum biyu ne a cikin gidan kuma bamu ga ko ɗaya ba acikinsu...."
yana kaiwa nan ya katse ƙiran,
Doctor Hasheem yar da wayar yayi ƙasi, idanuwansa sun ƙafe akan Ayush ji yake kansa yana juyawa, girgiza kai yayi a ruɗe ya tashi da gudu ya fice a falon,. a wannan daren yaje ya shige motarsa ya finciketa a ɗari ya nufi bakin gate,
Maigadi ne ya fito da gudu jin ƙarar motar yazo ya buɗe masa gate, ya tafi da kayan baccin a jikinsa....

Bayan fitarsa Ayush fashewa tayi da matsanancin kuka mai cin rai tana faɗin "ki gafarce ni Mommy Dan Allah, kiyi haƙuriiiii...."
kuka ne yaci ranta sosai, tana cikin rera kuka saiga Lailah ta fito tana sanye da rigar bacci zuwa gwiwarta, ganin Ayush yasa ta murtsuka idonta ko mafarki take ganin da gaske ne Ayush take gani ta sake baki tana kallonta....

*NACE BAAA YAU MA ZAN TAMBAYEKU HOW MARKET👋👋👋*

𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️

𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔

the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅

𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️

𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871

*💫💫{{N W A}}💫💫*

Book two

C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 37 ➡️ 38

Doctor Hasheem a ɗari ya iso da motarsa yana zuwa ya buɗe ya fito ganin gidan yanata ci da wuta ne yasa zuciyarsa bugawa baki na kakkarwa ya furta "innalillahi wa inna ilaihi raju'un..." da gudu ya shige gidan ya ɗauki robar feshin ruwa ya ƙarasa shigewa ciki, ruwa ake badawa sosai har Allah yasa wutar ta mutu, Doctor Hasheem a hanzarce ya shiga ɗakin mommy yana dubata amma bai ganta ba, ga yanda tiririn wuta yake tashi, haka suke duba wa amma ba alamun mommy ga toilet duk ya cinye da wuta, girgiza kai Doctor Hasheem yayi sannan ya furta "mu rasata, wuta ta cinye ta shikenam Mommy..." wani zazzafan hawaye ne yake zuba masa, sai ji yayi ta bayansa ance "Doctor akwai yarinyar gidan a ɗakinta fah.." Doctor Hasheem kawar da kansa gefe yayi ba tareda ya kulashi ba ya juya yayi ficewarsa...

*****

Lailah ce ta ƙaraso gurin da Ayush take tana tsaye tace "Ayushert meya kawo ki gidan nan a wannan daren?..". Ayush bata kulata ba ta cigaba da kukanta, ganin Lailah ta dameta da tambayoyi yasa Ayush miƙewa tana faɗin "idan kinaso na bar muku gida saina tafi ai koh.."
Lailah ta zaro Ido waje tace "me yayi zafi haka, cigaba da zamanki bani na kawoki ba, idan tayi tsami ma ji.." Lailah juyawa tayi ta nufi waran frig ta buÉ—e ta É—auki Apple da farro ta koma É—akinta daman yunwa ne ya fito da ita...

Ayush tayi waran awa biyu tana zaune bata rintsa ba, can saiga Doctor Hasheem ya shugo cikin damuwa yana tafiya kamar babu laka a jikinsa, zuwa gaban Ayush yayi ya tsaya yana faɗin "shin kin kyautawa kanki? yanzu kinji daɗi ko mommy ta ƙone tayi ƙurmus babu alamun gawarta, yanzu kin ji daɗi?..."
Ayush bata bashi amsa ba itama miƙewa tayi ta ɗauki akwatinta tayi hanyar fita, Doctor yace "ina zaki je kuma?.."
tace "zanje gurin da ba takurawa, na zaɓi nayi rayuwata ni kaɗai..."
Doctor Hasheem yace "amma ki sani idan Junaid yaji labarin ke kika ƙone gidansu bazai barki ba, kizo ki zauna damu anan gidan insha Allahu zan rufa miki asiri, shima Junaid zan san abunda zan gaya masa wanda bazai tuhumeki ba, amma muddin aka san cewa kece kika kashe Doctor Fateema ta hanyar wutar petur toh bakin mutane ma kaɗai ya isheki, za'ayi miki abunda akayi wa mahaifiyarki kema ki koma jeji da zama, idan kin zaɓi haka shikenam..."
Chapter 31 · 0% Book details