← Book details Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 85

Sashe 13

Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ruÉ—e ta juyo tana kallon yanda Junaid yake a kwance ido a lumshe ko motsi baya yi tace "Ogah Junaid na binciko komai wallahi wannan video da aka turo maka ba gaskiya bane,
domin bayan Ayush ta bar gurin taron baikon ku kai tsaye ɗakinta ta nufa, bayan wasu mintuna kuma saiga wannan matar mai liƙab wanda babu san ko ita wacece ba ta shiga ɗakin Ayush, daga baya kuma bayan wasu mintuna na shiga ɗakin Ayush amma saidai matar nan bata fito ba, amma kuma ban sameta a cikin ɗakin Ayush ba toh amma abun ya ɗaure mun kai kenam jin shugowata matar ta ɓuya kenam?
to ni bayan na fito matar bata fito ba har waran awa 3 lokacin kenam muna asibiti,
Laylah ta shiga É—akin bata fito ba sai bayan wasu mintuna kuma sai ga wannan mutumin shima ya shiga ciki,
Ni abun yayi mungun É—aure mun kai! mutane uku ne suke cikin É—akin Ayush
toh idan hakane Ayush batada masaniya akan abunda ya faru da ita, mata biyu acikin ɗakin namiji ɗaya sunyi amfani da wannan namiji ne domin su ɓata mata suna, amma kuma daga baya namijin ne ya fara fitowa sai kuma Lailah ta fito itama,
gashi camerar kuma ta nuna da mangariba Ayush ta fito sanye da dogon hijab ɗinta ta fice a lokacin hospital ta nufa nasani domin a wannan lokacin taje asibiti, to kuma ina matar nan mai liƙab najira fitowarta amma shuru har yanzu har kuma yau duk shige da fice da ake yi bata fito ba, to kodai Aljana ce?...."

Bayan ta gama surutanta ta kuma cewa "Ogah Junaid kaji fah yanda ake ciki.."

taji shuru bai bata amsa ba still ta sake ƙiran sunansa "Ogah Junaid! Ogah Junaid!! My Man lafiya kuwa kodai bacci ne ya ɗauke ku..."

ta tashi taje gurin da suke a ƙwance tana bubbugar kafaɗarsa tareda ƙiran sunansa amma ko motsi babu itama Ayush ko motsi, tasa hannunta a saitin hancinsu basa numfashi a ruɗe Angel ta miƙe tsaye tana faɗin "innalillahi me kuma ya faru, nashiga uku mommy.." ta fice a ɗakin da gudu tana ƙwalla ƙiran mommy....

Ogah Junaid shima numfashin sa ne ya É—age cak a sume yake...

*********

Maimoon ce take zaune a kan gadon Ammynta sai faman rera kuka take,
Mahaifiyarta ta sakata a gaba tanata mata tambayoyi acikin damuwa,
"Maimoon magana nake miki kin kasa bani amsa shin ina kika je tsawon kwanakin nan? baki taɓa tafiya wani waje ba tareda kin sanar mun ba, kuma baki taɓa yin wannan kwanaki a wani waje ba Maimoon so kike ki jawo mana abun magana?..."

Girgiza kai Maimoon kawai tayi ta kasa cewa komai,
suna cikin wannan halin saiga mahaifinta ya shugo shima yace wa Ammy "ta gaya miki yanda taje ta?..."

Ammy tace "a'ah tin jiya naketa binta akan ta sanar mun amma taƙi..."
Daddy yace "Okay.." ya fice a gigice, ba jumawa ya shugo hannunsa riƙe da wayar wuta yana zuwa ya fara zabga mata ajiki,
Maimoon ihu take tana kuka tanata sose-sosai har saida ya faffasa mata jiki abunka da farar mace, dakatawa yayi da dukanta yana zazzaro mata eyes yace "zaki faÉ—a mun yanda kika je ko kuma na cigaba da dukanki?..."

tana kuka tace "wallahi Daddy nima bansan yanda nake ba, wasu mutane ne suka kama ni suka ajiyeni awaransu, bana fita ko ina yanzun ma guduwa nayi basu sani ba..."

Daddynta yace "su waye ai dai kinsansu, kuma miye alaƙar ki dasu?.."
tana shessheƙar kuka tace "nima ban sansu ba, ina cikin tafiya taji an sakani a mota daga nan na nemi hankalina narasa..."

Daddy a fusace yace "ƙarya kike kice anyi kidnapped ɗinki domin da sun nemi kuɗi a waran mu..."

Ammy ta taso itama tana kuka tsabar tausayin ɗiyarta tazo gaban Daddy tace "Abul Bintu ka dubi wannan al'amarin Maimoon bata taɓa wannan dogon zango ba kuma ba tareda sanin mu ba, kaima dai kasan munada maƙiya zasuyi hakane domin su ƙuntata maka, fatan mu tinda Allah ya kuɓuto mana da ita mugode wa Allah kawai, amma ni na yadda da ɗiyata ɗari bisa ɗari..."

Dogon numfashi Daddy yaja idonsa akan Maimoon wacce kanta ke sunkuye yace "su nawa ne mutanen? kuma zaki iya gane fuskokinsu? sannan akwai abunda sukayi miki ne?..."

Maimoon ɗagowa tayi tana faɗin "gaskiya Daddy bazan iya ganesu ba saboda koda yaushe da baƙin hula a fuskokinsu, sun kai su goma amma babu abunda sukayi mun kawai dai acikin wani ɗan ɗaki suka kulle ni.."

Daddy ya kuma cewa "zaki iya gane gidan da suka kai ki?.."

Dasauri ta girgiza kai tace "a'a bansan lokacin da aka kaini gidan ba kuma lokacin dana fito ban tsaya dubawa ba saboda ina tsoron kar su fito su kamani..."

Daddy goya hannayensa yayi ta saman ƙirjinsa yace "inason shugo da hukuma cikin wannan al'amarin su binciko mun su waye ne waɗannan mutanen..."

Ammy tace "a'a Abul Bintu kar ka fara domin wannan maganar ba kowane ya sani ba, idan aka shugo da hukuma ai kowa zai san da maganar kuma akwai masu zargi da yawa, nidai a shawarce mu bar maganar nan a iya cikin gidan nan, ƴata da mutuncinta a idon jama'a kuma mahaddaciyar alƙur'ani, bazaiyu azo ana mata mummunar fassara ba..."

Daddy yace "toh shikenam tinda kince haka..."
yayi ficewarsa acikin É—akin,
Da gudu Maimoon ta tashi ta rungumi Ammy tana kuka mai cin rai...

Duk tattaunawar da sukayi kuwa Laylah tazo ta laɓe musu taji duk maganganun da sukayi tin daga lokacin da aka fara dukan Maimoon,
jin fitowar Daddy ne yasa tayi gudu ta koma falo ta zauna,

Daddy yana fitowa Laylah ta durƙusa har ƙasi ta gaishe shi ya amsa mata tareda cewa "ki tashi kice gurinsu suna cikin ɗaki, kinzo ganin ƙawarki ko.." ya ƙarisa maganar yana murmushin yaƙe domin bayaso ta fahimci wani abu...

Itama tashi tayi tana dariya ta shige ciki, tana shiga kuwa ta samesu suna zaune asaman gado Maimoon ta É—ora kayinta akan cinyar Ammy.

Da sallama Laylah ta shiga, Ammy ta amsa mata cikin nuna damuwa,
Samun guri Laylah tayi ta zauna suka gaisa da Ammy ta juyo tana kallon Maimoon tace "ashe Besty nah ta dawo.."

Ammy tace "wallahi kuwa Laylah wai ashe gidan kawunta taje ta toh sai matarsa ta riƙeta! sunyi ta ƙiran wayata basu samu ba, kuma yanzu basu da number Daddyn ta, dake ba'a Nigeria suke ba suna ƙasar Iran..."

Laylah tace "too har ƙasar Iran taje ta kuma bata sanar ba?.."

Ammy tace "cewa tayi baƙin cikin yayanki Hasheem ne yasa ta yanke hukuncin barin Nigeria, yanzun nan Daddynta ya gama yimata faɗa ai, ta tsoritar damu sosai wallahi..."

Laylah ta jinjina kai suna kallon kallo itada Maimoon tace "gaskiya Besty baki kyauta mana ba, kin hana mu bacci kullum acikin tunaninki muke..."

Wani irin harara Maimoon ta wurga mata ta juyar da kansa gefe guda..
Ammy tace "Maimoon baki ga Aminiyarki tazo bane?..."

𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️

𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔

the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅

𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️

𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871

*💫💫{{N W A}}💫💫*

Book two

C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 17 ➡️ 18

Mommy ta shugo É—akin Junaid da gudu kamar wacce zata kifu, Angel na biye da ita a baya haka suka shugo har secret room a yanda Angel ta barsu ahaka ta dawo ta tarar dasu,
Mommy jawo Ayush tayi daga saman Junaid zata faɗi ƙasi sukayi saurin tareta su biyu suka haɗu suka ɗauki Ayush sukayi ɗakinta da ita suna shiga suka kwantar da ita akan gadonta
tace "kInsan wani abu Angel ke zaki zauna da Ayusher ki yayyafa mata ruwa, ni kuma zanje naji da Junaid,
Angel tace "toh shikenam Mom..."
dasauri ta nufi toilet zata É—ebo ruwa,
ita kuwa mommy har ta fice,
da sauri ta shiga ɗakin Junaid ta samoshi a ɗayan room ɗin da bottle a hannunta na ruwan sanyi, tana zuwa ta fara watsa masa ruwan akan face ɗinsa, a hankali yake buɗe eyes ɗinsa ba tareda ya firgita ba! dishi-dishi yake kallon ceilling, ya ƙara lumshe idonsa tareda sauƙe numfashi,

Mommy ce ta É—aga kansa tukun ta zauna tareda kwantar da kansa kan cinyarta tana faÉ—in "Babana kana lafiya?..."

buÉ—e eyes É—insa yayi yana motsa bakinsa a hankali ya furta "Mom my heart zai fashe.."
ya riƙo hannun mommy ya ajiye asaitin zuciyarsa..

Mommy tace "My son ka kwantar da hankalinka ba abunda zai samu zuciyarka, ka daina saka abu a ranka kaji ko Babana..."
ya ɗago ƙwayar idonsa yana kallon Mommy yace "mom kin daina fushi dani?.."
Momy tace "daman ba fushi nake dakai ba, kaine idan ranka ya ɓaci baka iya control kanka, yanzu meye amfanin dukan Ayush? banaso ka mayar mun da yarinya jaka, yanzu ma naga naji rauni akan goshinta kuma nasan kaine! shiyasa take tsoron Aurenka ai...".
ta sauƙe numfashi tareda kallon gefe tana shafar sumar kayinsa,
yana kallon ceilling yace "tayi mun laifi babba Mom, meyasa zata kwanta da wani namiji daban wanda bani ba? bazan iya juran haka ba..."
Shuru Mommy tayi bata ce masa komai ba...

Ayush ce take zaune asaman gadonta sai faman rera kuka take bayan Angel ta farfaÉ—o da ita,
hakuri Angel take bata tana rarrashinta tareda cewa "Ayush kema bakya jin magana wallahi, bayan kinsan a halin da ake ciki yanzu Junaid ba'a cikin nutsuwarsa yake ba, mai zai kaiki É—akinsa har ma ki shiga yanda ba'a lamunce miki ba haba dan Allah, gashi yanzu kin jawo ya fasa miki goshi bayan baki gama warkewa da dukan da yayi miki ba..."

Share hawayenta Ayush tayi sannan tace "kenam ni an mayarni dabba kullum acikin dukana ake, nifa ba yarinya bace! na mallaki hankalin kaina, saboda Yaya Junaid gaba ɗaya zaman gidan ya isheni, ni tafiya zanyi bazan iya rayuwa acikin wannan ƙuncin ba kullum ina cikin zubda hawaye, ina zaune a cikin gidan masu kuɗi amma ba kwanciyar hankali a cikin gidan kamar wacce nake cikin prison..." ta ƙarisa maganar tana kuka.

Angel tace. "a'ah ki kwantar da hankalinki gobe ma Junaid zai bar Nigeria kuma kafin ya dawo komai zai daidaita, idan kikace zaki tafi Mommy bazataji daÉ—i ba..."
Chapter 13 · 0% Book details