← Book details Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 85

Sashe 69

Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Bayan su Junaid sun koma gani yayi babu Ayush, saida ya ƙarashi dubata bai ganta ba tukun ya lura da jinin data ɓata, gabansa ne yayi wani irin bugawa a tsorace ya ƙwalla ƙiran ta "Yushertttt!!!!
da gudu ya sauƙa down stairs ya nufi ɗakin mommy, itama ya tarar bata nan, ya fito falo nan ma yaga jini duk ya ɓata carpet ɗin, a ruɗe ya wuce part ɗin Abba, nan ya sanar masa halinda ake ciki, nan danan Abba ya shiga ƙiran wayan mommy amma saidai wayar ta barshi a gida,
Abba yace "ina tunanin fah suna hospital ko haihuwa Ayush zatayi .."
Junaid kamar ya nitse ƙasi haka yake jin kansa na rashin ganin Ayush kuma ga jini ta ko ina, a gigice yace "Abba muje hospital ɗin banaso na rasa Yushert..."
Suma haka suka nufi hospital,
Kafin ka ƙirga mintuna har sun isa hospital dake Junaid shi yake driving gudu yake bana wasa ba..
suna sauƙa ya rufa cikin facility ɗin hospital da gudu, yana zuwa ya tarar da Judan da Hafzat zaune babu wanda yayi magana acikin su, Hafzat sai faman kuka take ta gagara yin shuru, ganin halinda ya tarar dasu yasa gabansa ya ƙara yankewa gaba ɗaya ya gama tsorita, a gigice ya dafa kafaɗar Judan yana faɗin "Ina Yushert? Meya faru da ita?..."
Judan yace "tana cikin can É—akin..."
Da gudu Junaid zai nufi ɗakin Judan yayi saurin riƙo shi yana faɗin "Ah ahhh ka kwantar da hankalinka Ogah, can ɗin labour room ne haihuwa ne ya tashi mata..."
wani irin haÉ—iyar yawu yayi tareda faÉ—in "Allah yasa dai karta mutu..."
Judan yace "insha Allah zata haihu cikin ƙoshi lafiya .."
Shima Abban ƙarasowa wajen yayi dasauri yana addu'a Allah ya sauƙeta lafiya,
Suna cikin wannan halin saiga wata Nurse ta fito daga cikin É—akin tana sauri zata É—auko abu, Junaid yayi saurin tareda yana faÉ—in "Ina Yushert É—ina?..."
Nurse murmushi tayi tace "ta haihu..."
Junaid yace "toh Amma ita fah??..". bata samu damar bashi amsa ba ta wuce saboda saurin da take yi,
Can bayan wasu mintuna saiga Mommy ta fito tana kuka,
Ganin tana kuka yasa duk suka tsorata, gaba É—ayansu nufo gurinta sukayi suna tambayanta Ayush,
Mommy taƙi yin magana sai hawaye,
Junaid cikin firgici da tashin hankali ya mannu da jikin gini, jikinsa gaba ɗaya ya mutu idanuwansa sun kaɗa sunyi jawur yana shirin zubda ƙwallah yaji mommy ta tintsire da dariya, lokaci guda ta fara tsalle tana faɗin "Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Alhamdulillah Masha Allah!!!! Allah mun gode makaaa..."
taje gaban Junaid tana murna tace "wannan kukan farin ciki nake yi Ayush ɗita ta Haifi triplets ƴan uku kuma tana cikin ƙoshin lafiya...."
Zaro ido Junaid yayi cike da mamaki yace "Mommmm are sure? Triplets fahh?..."
Mommy tace "yesss my son..."
Tsabar farin ciki Junaid baisan lokacin da ya rungumi mommy ba ya É—agata sama yana juyi da ita..."
Momy buɗe baki tayi tana faɗin "kai kai kaiiii sauƙe ni dallah ni ɗin dai ba ƴar tsana bace, kaji mun wawan yaro..." ta ƙarasa maganar tana dariya, sauƙeta yayi ya nufi cikin ɗakin da gudu, daman an rigada an shirya ɗakin da yaran gaba ɗaya anyi musu wanka an sanya musu kayan sanyi na jarirai daman an tanadar dasu, ita kuma Ayush tana kwance an gyara ta itama tana rufe da mayafi zuwa ƙirjinta har yanzu bata farfaɗo ba,
ganan ledar jinin da aka É—aura mata yana É—iga a hankali saboda ta zubda jini sosai kafin azo asibitin ma....

Junaid yana shiga gurin Ayush ya fara nufa ya zauna a bakin gado yana shafar kyakykyawar fuskarta, ido a lumshe sai yaga ta ƙara masa kyau sosai ta ƙara fari daman gatanan kamar tsohuwar Aljana tsabar farin fata da kyau, yanzu kuma saita ƙara farin akan na baya,
Daga baya suma su Abba da mommy da Hafzat da Judan suma suka shugo fuskarsu a washe kowa bakinsa a buÉ—e an kasa rufe shi,
zama sukayi akan kujerun É—akin kowa yana É—aukin a bashi jariri,
Mommy ta ɗauki jaririn namiji ta miƙawa Abba, ta ɗauƙi ɗayan mace ta miƙawa Judan ɗayar kuma ta bawa Hafzat,
Shi kuma Junaid yana ta Yushert É—insa bai tsaya duba Jariran ba,
Kowa a cikinsu saida ya tottofawa jariran Addu'o'in neman tsari, kafin shima Junaid ya karɓesu ɗaya bayan ɗaya yana musu ƙiran sallah a cikin kunnensu tareda Addu'o'i....

A wannan ranar farin ciki saida mommy ta ƙira ƴan uwa da abokan arziƙi duk ta sassanar musu, Uncle Artaff kam shine first ɗin ƙira,
Kafin azozzo duba Ayush saida aka canza mata É—aki zuwa wani katafaren É—aki na alhurma ya gama haÉ—uwa kamar É—akin ba'a cikin hospital yake ba,
harda plasman da frig ga A.C amma saide an kashe A.C an kunna abunda yake bada É—umi a É—akin saboda jarirai basu son sanyi,
(Nidai na manta sunan abun dake babu a house 🤣🤣)...

Ga labulaye masu tsada, carpet kuma kana takawa yana nutsewa dakai, ga wasu kujeru masu kyan tsada guda bakwai,
Cikin toilet kuma akwai shawer na ruwan sanyi da zafi, akwai kuma bahon wanka, anyi sa'a zuwa wannan lokacin Ayush ta farfaɗo saidai bata jin daɗin jikinta, ba jumawa saiga su Uncle Artaff da iyalansa shima sunzo hospital, a ranar anyi baƙi kam duk abokan arziƙi ne da masoya, banda ƴan uwansu mommy dake su ba'a gari suke ba, wasu suna Kaduna wasu Kano wasu Bauchi wasu kuma ba'a cikin Nigeria suke ba akwai waɗanda suke Camaroon da London da Sudan...
Mommy tanada ƴan uwa sosai, saboda Junaid ne basa zuwa don idan sukazo bakinsu baya mutuwa sun rinƙa tambayar ƴan uwan mahaifin Junaid shi kuwa yaita musu rashin mutunci har koransu yake daga gidansu, kuma yayi musu warning akan kar su sake zuwa yanda suke dalilin da yasa basa zuwa kenam, amma yanzu tinda komai yayi normal duk zasu zo amma sai ana gobe suna, kuma a ranar suna za'a ɗaura Auren mommy da sarki Raamud...

★★★★★

Ranar Suna, ranar daya kama ranar Jumma'at kenam, gidan mommy ya cika da mutane, ƴan uwan mommy su sukafi yawa dake gidan babban gida ne, akwai ɗakuna part to part, kuma an ƙara tsara gidan yayi kyau sosai, an chancanza furniture's ɗin ɗakunan, sunyi bala'in kyau sosai,
Ko wani ɗaki ƴan gari ɗaya ne aciki, ɗakin ƴan Bauchi daban, ɗakin ƴan Kano daban, ɗankin ƴan Kaduna daban, ɗakin ƴan Katsina daban, ɗakin ƴan Adamawa daban, ɗakin ƴan ƙasar London daban, ɗakin ƴan ƙasar Camaroon daban, ɗakin ƴan ƙasar Sudan daban, waɗannan duk ƴan uwan mommy ne sun samu wadatattun ɗakuna!!!!
Sai kuma iyayen su Hafzat suma sunzo hidimar tareda Æ´an uwanta kusan su goma, daga Kano suma...

Ga Mutanen ƙasar Iran wato ƴan uwan mahaifiyar Uncle Artaff suma kusan su goma sun zo aciki harda mahaifiyarsa ta fara samun sauƙi Alhamdulillah ita kam ɗakinta daban aka tanadar ita kaɗai dake bata son hayaniya,
Duk ƴan uwan mommy an nuna musu cewa itace mahaifiyar Máahmud Baban Junaid kuma an nunnuna musu sarki Raamud da Uncle Artaff cewa sune ƴan uwansa kuma sun gamsu sosai har suna cewa "ai kuwa suna kama da Máahmud sakk especially sarki Raamud kamar an tsaga kara..."
Sai yanzu hankulansu suka kwanta ganin Æ´an uwan mahaifin Junaid,
Gasu Lailah suma sunzo hidimar ita da Maimoon dasu Ammy,
Daga ƙasar China Aunty Adity itama tazo jin labarin ƙaruwar da Ogah Junaid ya samu,

A masallacin da aka É—aura Auren mommy da Abbah anan aka raÉ—a sunan Æ´an ukun Junaid da Ayushert,
An sanya musu sunaaa!!!

Namijin yaci sunan mahaifin Junaid wato
MÁAHMUD *(AREEPH)*
Ita kuma É—aya daga cikin macen ta samu sunan Mommy wato.
FATEEMA *(AMREESH)*
ita kuma ɗayar Junaid yayi alƙawarin indai ya samu ɗiya mace zai yiwa jarumarsa mai suna, toh wannan alƙawarin yana nan tafe an sanya mata sunaaa..
MARYAM *(ANGEL)*.....
Chapter 69 · 0% Book details