Sashe 57
Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ata ɓangaren Lailah kuwa ta samu sauƙi sosai domin yanzu tana cikin hayyacinta amma saidai bata iya gane kowa,
yanzu waɗanda ta sani sun dawo mata tamkar sababbin fuskoki, amma zata zauna tayi hira da mutum, a yanzu dai iya Doctor Mansur kawai ta sani domin a koda yaushe shine a jikinta, koda wasa bai taɓa gajiyawa da ɗawainiya da ita ba, kuma wani ƙakƙarfar alaƙa ne ya shiga tsakaninsu wanda idan Lailah bata ga Doctor Mansur ba hankalinta tashi yake, shi kuwa baya ƙaunar tashin hankalinta shiyasa baya barin yanda take saidai idan tana bacci,
Doctor Mansur yana iya ƙoƙarinsa akan Lailah tasan tana da ƴan uwa musamman Doctor Hasheem da yake prison, koda yaushe yakan bata labarinsa har tasa a ranta cewa tana da Yayanta a prison kuma ana yawan nuna mata photonsa hakan yasa take muradin ganinsa,
yau ma kamar kullum tana zaune a saman gado shi kuma Doctor Mansur yana kusa da ita a zaune a bakin gado yana ɓare mata wasu maganinnuwa da bottle na ruwa akan table,
ta ƙura masa ido sai kallonsa take ko ƙibtawa bata yi tana motsa baki a hankali cikin sassanyar murya tace "JAAN..."
É—agowa yayi da kyawawan idanuwansa yana kallon cikin taurarin eyes É—inta da murmushi a fuskarsa ya amsa mata da "Na'am Baby..."
cikin kasalalliyar murya tace "kai kyakkyawa ne.." suna cikin kallon juna ya ƙibta mata ido ɗaya tareda kai hannunsa saitin bakinta yace "HAAAA buɗe bakin ki kisha magani.."
a hankali ta buÉ—e ya saka mata su tareda kafa mata bakin gorar ruwa, haka take shan ruwan tana lumshe ido,
shi kuwa hakan ba ƙaramin burgeshi take yi ba, shima haka ya ƙura mata ido da kyawawan sex eyes ɗinsa,
a cikin zuciyarsa kuwa cewa yake "Masha Allah! tabarakallah Godiya ta tabbata ga sarkin halittun duniya wanda ya halitta mun wannan kyakkyawar É—awisu, Yaa Allah ka mallaka mun wannan halittar ka a mazannin matata ta Aure..."
duk Abunda yake so a game da mace gaba É—aya Lailah ta tara su,
Lailah she is a black beauty, amma saidai baƙinta na haske ne domin babu mai cemata baƙar fata, chaculate colour sannan ta haɗa da ido da kuma ƙaramin baki sai dogon hanci,
itama tanada sumar gashi babu laifi bugu da ƙari kuma tanada ƙyakykyawar surar jiki, domin a dire take Lailah tafi Ayush da Maimoon dirin jiki,
Lailah ganin kallon da Doctor Mansur yake mata babu ƙarshensa yasa ta matso daf dashi takai bakinta saitin fuskarsa tana hura masa iskar bakinta, a ruɗe yayi firgit ya dawo hayyacinsa yana sauƙe numfashi da smile a fuskarsa, ita kuwa komawa tayi ta zauna a yanda take tana binsa da kallo,
wani irin yanayi yaji ya shiga lokaci guda daman hakane indai ya zauna a kusa da Lailah ya ɗan juma to saiya shiga cikin wani hali na feeling, ba shiri ya miƙe tsaye tareda faɗin "Baby zanje na ƙarasa Ayyukana amma zan dawo ba jumawa..."
yana kaiwa nan ya nufi hanyar fita har ya buɗe ƙofa zai fita ta katse shi da cewa "JAAN..."
juyowa yayi yana kallonta haɗe da sau mata ƙayataccen murmushi yace "My Baby..."
turo ƙaramin bakinta tayi a shagwaɓe tace "yau ɗin ba chaculaty ne?..". Dariya yayi har saida fararen haƙwaransa suka fito yace "waya gaya miki ana fashin kawo wa Baby chaculate ne? na yau ma yafi na kullum..."
sumbatar tafin hannunta tayi sannan ta hura masa iskar, yayi saurin dunƙule hannunsa kamar ya karɓi saƙon sannan ya ɗora hannun akan saitin zuciyarsa yana shafar wajen,
Lailah cikin jin kunya takai hannayenta biyu ta rufe fuskarta tana dariya,
shima da dariya yabar cikin ɗakin tareda rufe mata ƙofa....
Bayan fitarsa da awa ɗaya saiga Mommy ta turo ƙofar ɗakin Lailah da sallama a bakinta, lokacin Lailah har tayi nisa a baccin ta, zuwa tayi dab da gadonta ta zauna akan kujerar da yake fuskantar Lailah! zuba mata ido tayi tana tausaya mata a halin da take ciki, ga ta rasa tunaninta ga kuma Babban Yayanta a prison ga babu iyaye, tana cikin wannan tunanin taji ana faɗin "wacece ke? mezaki mu? kada ki cutar dani dan Allah, wayyo Doctor! Doctorr!! JAAN kazo ka temake niiii...." ta ƙarisa maganar tareda fashewa da kuka,
ita kuwa Mommy kaÉ—a mata hannu take tareda cewa "A'ah Lailah ki saurare ni, nasan kin manta ni amma Ni ba cutar dake zanyi ba, ki kwantar da hankalinki..."
Lailah girgiza mata kai take alamar bata gamsu da jawabanta ba, suna cikin wannan halin saiga Doctor ya shugo yana riƙe da baƙar leda, ya ƙarisa shugowa da sauri ganin yanda Lailah take ta kururuwa, zama yayi a bakin gadon ya kamo hannunta yana matsa mata a hankali, yace "colm down Baby, ki daina jin tsoron mutane domin sun zo duba lafiyarki ne bawai cutar dake ba, idan kikayi musu haka baki musu adalci ba, a yanzu kin mance komai but kina buƙatar ƙwanciyar hankali yanda zaki sake sabunta rayuwarki, waɗanda kika mance a baya yakamata ki dawo dasu cikin rayuwarki kinji koh Baby..."
Lailah fashewa tayi da matsanancin kuka tana faɗin "kenam wannan mah inada alaƙa da ita? wacece ita a gurina ina buƙatar sani domin na karɓeta da hannu bibbiyu..."
Doctor ya kalli mommy sannan yace "Hajia saidai kiyi mata bayani da kanki tinda har zata saurareki.."
Mommy hawaye ne ya kuɓuto mata tasa hannu tana gogewa tareda matso da kujerar ta kusa da ita tace "Lailah ki ƙwantar da hankalinki wannan ƙaddarar daya afku dake Allah Ubangiji yasa shine mafi Alkhairi agareki, Allah yasa canjin rayuwarki shine silar shiryuwarki akan komai duk da bana shedar ki akan aikata laifi amma na sanki da yawan faɗa da masifa...". Mommy ta ƙarasa maganar cikin zolaya tareda ja mata hanci, itama Lailah saida ta murmusa jin yanda mommy taso da nishaɗartar da ita,
Mommy ta cigaba da cewa "Ni Abokiyar mahaifiyarki ce wacce ta rigamu gidan gaskiya, ni nake yawan kula da al'amuranku ke da ƴan uwanki tin kuna yara da iyayenku suka rasu, kuna ƙirana da suna Mommy kasancewar kunbi bakin ɗana wato Junaid domin shi kawai na haifa..."
Lailah ƙura mata ido tayi har saida ta kammala sannan tace "na fahimce ki Mommy, kenam iyayena tin ina ƙarama suka mutu suka barni? niɗin marainiya ce daman? Allah Sarki mommy mun gode miki da ƙoƙarin da kikayi akan mu,
toh Amma su nawa ne Æ´an uwana?.."
Mommy tace "ku huɗu ne Lailah, Babban Yayanki shine Doctor Hasheem wanda yanzu haka yana prison, sai kuma wanda ya biyo shi shikuma yana ƙasar Egypt karatu, sai kuma haidar wanda yanzu yana can Katsina gurin kakarku, kece kawai mace acikinsu kuma Auta..."
Lailah cikin yanayin tausayi tace "toh amma meyasa su Æ´an uwan nawan basu zo sun dubani ba?.."
Mommy tace "saboda gudun tashin hankalinsu hakan yasa ba'a sanar musu rashin lafiyarki ba kuma hatta shi babban Yayan nakun basu san yana prison ba, amma da yardar Allah Yayanki ya kusan fitowa..."
Lailah tace "gwara ma da ba'a gaya musu ba saboda kar hankalinsu ya tashi, amma keÉ—in mommy ya sunan É—an nakin?.."
Mommy tayi ajiyar zuciya tana mai jinjina wannan al'amarin daya faru da Lailah, gashi wanda take mutuwar so mah ta manta dashi, cikin kasalalliyar murya tace "sunansa Junaid Khan yana da matarsa har ta kusan haihuwa..."
Lailah tayi saurin katse mommy da cewa "a'a mommy daman ba cewa zanyi inasonsa ba, ni yanzu burina shine komai nawa ya dawo mun ƙwaƙwalwata..."
Murmushi mommy tayi tana girgiza kai tace "Lailah kenam ni É—in ma kawai nasar miki nayi saboda ki fara sanin kowa.."
itama Lailah murmushi tayi tace "Allah Sarki mommy nima wasa nake miki kiyi haƙuri..."
kaiwa hannu mommy tayi tana shafar suman gashinta ba tareda tace komai ba..
suna cikin wannan halin sai suka ji sallama an turo ƙofar ɗakin, Mommy da Doctor suka amsa sallamar cikin kulawa,
Maimoon ce ta shugo da yaro a hannunta ta rufa masa farin towel a kansa, sai kuma Ammy da Daddy! Doctor ne ya nuna musu waran zama tareda musu barka da zuwa suka gaigaisa, itama mommy tana murmushi suka gaisa cikin aminci da kyautatawa juna,
Daddy ne yazo har bakin gadon Lailah ya zauna yana faÉ—in "Autar Mama da Abba yadai?..." Lailah zuba masa ido tayi tana murmushi tace "babu komai..."
Mommy tace "waÉ—annan É—in kin ganesu ne?.."
Lailah tana kallonsu tace "na ganesu mana ai suna yawan zuwa mun, kuma Doctor ya ce mun suna taka rawar ganin na samu lafiyata..."
Daddy yace "ni naso ace ma asibitin ƙasar waje aka fita da ita wata ƙila za'ayi dacen dawo mata da memory sense ɗinta..."
Lailah tayi saurin katse shi da cewa "a'a Daddy nafi jin daɗin zamana a wannan asibitin domin Doctor yana bani kulawa sosai da sosai.." ta ƙarasa maganar tana kallon Doctor Mansur wanda shima kallonta yake yana murmushi ...
Daddy yace "toh shikenam ai naga yanzu kin samu lafiya koh?.." jinjina kai Lailah tayi tareda cewa "sosai ma Daddy yanzu bana jin komai a jikina"
Daddy yace "Masha Allah haka nake son ji Autar Abba,
Daman yau nazo ne ma akan a sallameta zamu wuce gida da ita, akwai ƴan uwan mahaifiyarta cikin wannan satin zasu zo duba jikinta, ƙwanaki ƴan uwan mahaifinta ne suka zo, insha Allahu zan cigaba da riƙeta a gidana..."