← Book details Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 85

Sashe 61

Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hafzat tana ƙwance asaman katafaren gadonta tana lumshe da ido kamar mai yin bacci ƙwatsam taji bugun ƙofa a hankali, tana son tambayar ko waye amma hakan ya gagara daƙer ta tashi jiki a mace tana jan ƙafa taje ta buɗe ƙofar,
ganin Junaid yasa ƙirjinta yayi wani rass dasauri taja da baya domin tinda tazo gidan nan bai taɓa zuwa koda bakin ƙofar ɗakinta ba sai yau,
Junaid tsayawa yayi yana kallonta cike da mamakin irin tsoron da take masa, baisan dalilin da yasa take jin tsoronsa ba,
nafarko shi ba wani haÉ—e mata rai yake yi ba, har yanzu bai nuna mata asalin kansa ba amma duk da hakan tana nuna tsoronta akansa, hakan kuma yana shirin sosa masa zuciya,
ƙarasa shugowa yayi ya nemi guri ya zauna a bakin gadonta idonsa akanta yace "zo ki zauna"
jiki na ɓari ta soma girgiza masa kai alamar a'ah,
ƙara maimaita mata yayi kuma du ta sake girgiza masa kai, ransa ne yayi matuƙar ɓaci yakai hannunsa saitin goshinsa yana murzawa cikin zafin nama ya zaburo ya cabko hannunta sannan ya janyo ta dab dashi yana zaro mata ido yace "zauna nace..."
ba shiri ta É—osana É—uwawunta a bakin gadon tana ajiyar zuciya,
ba tareda ya kalleta ba yace "me kike tunani akaina ne?..."
shuru tayi masa ba tareda ta bashi amsa ba, ya kuma cewa "nayi miki kama da dodo ne ko kuma kina tunanin zan cutar dake ne?...."
kanta a sunkuye ta kasa É—agowa balle ta iya bashi amsa,
ransa ne yayi matuƙar ɓaci a fusace ya daka mata tsawa tareda faɗin "I hate dis nonsense, idan ina miki magana kina sharar dani wata rana zanyi ball dake ..."
Hafzat a gigice ta É—ago tana kallonsa lips É—inta na kakkarwa tama rasa mai zata ce masa,
. haka kawai Junaid yake mata ƙwarjini tin daga lokacin data fara ganinsa ta soma jin shakkarsa domin ta juma bataga namiji dirarre ƙarfaffa mai faffaɗar ƙirji irin na Junaid ba, gashi asalin kyakykyawa ne ga lips ɗinsa kamar na mace ƙarami dashi ga yaci launin maroon colour, ga sumar kayi baƙi ƙirin lallausa a ƙwance luf² har zuwa sajensa zuwa gemun, haƙiƙa duk macen data haɗa ido da Junaid bazata taɓa sanin Lokacin da zata shiga wani hali ba,
Hafzat ko kaɗan bata ƙaunar Junaid yazo yanda take domin bazata iya juran ganinsa ba, shiyasa idan tana gabansa kanta yake ƙasi bata son ɗagowa ta kalleshi,
a yanzun ma bata san lokacin da idonta suka kafu akansa ba, ko ƙibtasu bata yi, wani dogon tunani ta faɗa ciki still idonta akansa,
ganin kallon da take masa ne yasa shi mamaki yana tunanin meye dalilin da yasa ta zuba masa na mujiya har haka, hannu yakai saitin idonta yana karkaÉ—asu yanason ganin shin a hayyacinta take ko sumar zaune tayi,
firgit tayi a tsorace ta soma faÉ—in "innalillahi wayyo Allah mijin Aljanna..."
kallonta yayi cikin rashin fahimta yace "kin haukace ne?..." girgiza masa kai tayi tareda cewa "a'ah..."
jinjina kai yayi sannan yace "kin iya shayin na'a-na'a?..." dasauri ta É—aga masa kai alamar ehh, yace "aina kika iya?.." cikin sanyin murya tace "agurin Mommy.." jinjina kai yayi yace "ok kizo ki haÉ—a mana yanzu" yana kaiwa nan ya tashi yayi ficewarsa, ita kuwa bin bayansa tayi da kallo cikin wani irin yanayi data tsinci kanta a ciki...

Around 10 O'clock pm.
Sarki Raamud yana nan yanata kai kawo a falo ya kasa zama gaba É—aya yana cikin damuwa na rashin ganin mommy, sai tambaya yaketa yi "wai shin har yanzu bata dawo bane? kuzo ku kaini asibitin nan naje na dubo ko lafiya tinda safe har zuwa yanzu dare.."

Shima Junaid yana zaune akan hannun kujera sai faman ƙiran wayan Ayush yake amma ba'a picking, gaba ɗaya ransa a ɓace yake domin basuyi akan zata kai wannan lokacin bata dawo ba, sai tsaki yake ta ja shi kaɗai..

Ita kuwa Hafzat da Judan suna saman dinnig suna night lunch su biyu, sai jan hankalinta yake da hirar masoya ita kuwa hankalinta yana kan su Junaid, shi yana damuwa akan rashin dawowar Yushert ɗinsa shi kuma Sarki Raamud yana damuwa akan Mommy toh abunda yafi bata mamaki shine "shin meye alaƙar Abbah da Mommy? Bayan ance su ba ma'aurata bane, gaskiya akwai ƙaƙƙarfar alaƙar soyayya a tsakanin mommy da Abbah..." a cewar Hafzat da take ta maganar zuci,
duk gidan nan ita kaɗai ta fahimci akwai soyayya a tsakaninsu domin ita take kusa da mommy akoda yaushe inhar tana gida, kuma suna yawan waya, yana daga part ɗinsa itama tana part ɗinta amma haka zasu ɗau lokuta suna waya, wani lokacin kuma sukan haɗu a guest room dake can wani part na gidan, tsararren waje na baƙi idan za'ayi wani ɗan taro! acan suke haɗuwa su sha lovayya, kuma Mommy takan tashi cikin dare misalin ƙarfe 12 ko 1 taje kitchen ta haɗo shayin na'a-na'a takai part ɗin sarki Raamud, saboda shi indai bai tashi yasa wani abu a cikinsa dadaddare ba akwai matsala, hakan yasa mommy take ɗauka masa wannan ɗawainiyar, soyayyarsu suke sha ba tareda kowa yasani ba a cikin gidan, amma ita Hafzat tana bibiye dasu itace CCT ɗinsu, kuma tana yawan ɗaukar wayar mommy da cewar zatayi Game ko kallo haka zata shiga gurin saƙonni taga duk saƙon soyayyar da sarki yake turo mata itama tamayar masa da reply na soyayya, wayan yana hannunta sarki yasha ƙiran mommy amma bata ɗauka saboda bata son su gane cewar ita tasan alaƙar dake tsakaninsu har sai sune suka bayyanar da kansu, tsabar yawan ƙiran da sarki yake yiwa mommy a waya Hafzat har ta riƙe numbersa daman dake number a saved yake an rubuta KING OF KINGS akan numbersa....

Hafzat kallonsu kawai take tana murmushi daga Junaid É—in har Abbah, kawar da kai tayi ta maida hankalinta kan Judan wanda tin É—azu yake ta zuba kamar kurna...
Bayan wasu mintuna suka ji an turo ƙofar falo da sallama a bakinsu suka shugo, mommy da Ayush a zabure sarki yayo kan mommy yana faɗin "Sarauniya ina kika shiga ne haka gaba ɗaya na shiga damuwa, sauran kaɗan na fita nemanki..."
Mommy tayi murmushi tana kallonsa cikin yanayin shagwaɓa tace "kayi haƙuri My king wallahi Ayyuka ne suka riƙeni..."
Yace "toh Sarauniya please ki dena kaiwa dare a waje kinji koh?..."
tace "Insha Allahu my king zan kiyaye..."
cikin farin ciki da annushuwa ya ƙibta mata ido ɗaya, tayi saurin kawar da kanta tana dariya ...."

Dasauri Ayush ta waiwayo tana kallonsu cikin mamaki ido kamar zasu faɗo ƙasi jin yanda mommy take ƙiran Abbanta! cikin rashin fahimta ta maimaita sunan da ƙarfi tace
"My King kuma?...."

a zabure mommy ta É—ago tana kallonta ita sam ta manta cewa akwai mutane a wajen, ganin sarki Raamud yakan sa ta manta da abunda take yi,
shima tsabar hankalinsa yana kan mommy kwata-kwata ya sha'afa da cewar akwai mutane a falon, cikin jin kunya yayi saurin barin falon ya koma part É—insa,
itama mommy bata tsaya bawa Ayush amsa ba ta ratsa ta gefenta ta wuce É—akinta jiki duk a sanyaye...
Gaba ɗaya hankalin Ayush ba ƙaramin tashi yayi ba jin irin maganganun da sukayi irin na masoya, a hankali ta furta "Whatttt can't believe..."

Shi kuwa Junaid tin shugowar Ayush yake ta jifanta da wani irin kallo na takaici, sunyi akan idan taje hospital zuwa azahar ko la'asar zata dawo sai gashi har 10 na dare, kuma ba yau ta saba masa haka ba, sai gadarar idan tayi laifi ta soma kuka tana bada haƙuri da magiya amma hakan bashi zaisa gobe ma ta ƙara yin laifin ba,
yana cikin huci tazo ta wuce shi ko kallon yanda yake batayi ba haka ta wuce da ƙaton tumbin cikinta kamar zatayi ihu haka take ji tana mamakin yanda mommy da Abbah suka shaƙu har haka...

Haka take taka matakalar Benin kamar babu jini a jikinta da haka harta shige bedroom É—inta,
shima Junaid a fusace ya haura yabi bayanta, sai iya Hafzat kawai aka bari ita da Judan har ta fara sakin jikinta dashi...

★★★★★★★ "Yushert! Yushert!! Yushertttt!!! tsabar iskanci kinaji ina ƙiranki amma ko ki kulani bayan laifin da kika yi?.."
Ayush tana zaune a bakin gado tana jinsa yanata surutansa amma ko kallonsa batayi ba, kawai maganganun su Mommy ne yake mata yawo aka, dogon tunani ta faɗa ga kuma hawaye shaɓe-shaɓe akan fuskarta,
ganin haka yasa Junaid zama a kusa da ita yana faÉ—in "ke kuma fah? me akayi miki kike kuka?..."
murya ciki-ciki tace "Babu komai"
Yace "a'a akwai banason ɓoye-ɓoye a lamarina ki fito ki faɗa mun gaskiyar abunda yake faruwa..."
cikin nuna rashin son hayaniya da damuwa kamar zata rausa ihu tace "haba Yaya Junaid mekake so nace maka, nace babu komai ba dole ne saika ji ba, please ka ƙyaleni da abunda ke damuna banson hayaniya da damuwa..."
cike da mamaki yake binta da wani irin bahagon kallo yace "whattt! Yushert Ni ne hayaniya da damuwa? okay thanks..."
cikin takaici ya miƙe tsaye tareda cire jallabiyan jikinsa ya faɗa cikin toilet yayi wanka shaf-shaf sannan ya fito yana ƙamshin sabulu mai daɗin gaske, ya shirya cikin ƙananun kaya three quarter da singlet sannan yazo gaban Ayush kamar bazaiyi magana ba cikin ƙarfin hali yace "tashi mun zan ƙwanta..."
tashi tayi tana haɗe rai ta koma kan wata doguwar sofa ta zauna tareda kifa kanta akan gwiwowinta tana rera kuka ciki²
Shi kuwa hannu ya miƙa ya kashe hasken ɗakin sannan ya kunna green lamp sai ɗakin ya bada green light mai kyan gaske, ya kwanta tareda jawa kansa mayafi ya lumshe idonsa kamar meyin bacci sai dai yana jinjina maganganun Ayush data yi masa cikin rashin ɗa'a da biyayya sannan yana tunanin shin meya sameta ta shiga damuwa har haka,
yana cikin wannan tunanin da haka har bacci ɓarawo yayi awun gaba dashi....
Chapter 61 · 0% Book details