← Book details Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 85

Sashe 2

Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

daga ƙarshe Laylah ta bashi umarnin ya sauƙa haka, tayi saved video tana cije leɓɓenta,
saka kayansa yayi sannan yace "Æ´anmata ni zan tafi saina ji alart, É—aga masa kai kawai tayi sannan tace "yanzu ma kuwa.."
yana tafiya tayi masa transfer 50,000,
Ayush kuwa nan danan wani irin mungun bacci ya ɗauketa, dariya Laylah tayi tace "wooo ni Laylah Amaryar Ogah Junaid, Ayush kenam daga yau soyayyarki bazata ƙara zama a cikin zuciyar Ogah Junaid ba, nasan dai bayan kin farfaɗo bazaki tuna abunda ya faru ba, sai dai ki ganki acikin wannan yanayinda kike ciki, na barki lafiya..."

Laylah ce itama tayi ficewar ta a É—akin, cike da farin ciki ta bar gidan gaba É—aya....

Ayush bata farfaɗo ba sai ana ƙiran sallar mangarib ta tashi jikinta yana mata ciwo, ga ta tashi da ciwon kai tana lumshe manya-manyan eyes ɗinta waɗanda suka shanye kamar wacce tayi maye, kallon kanta tayi a zabure ta tashi tana faɗin "subhanallahi ya na ganni a haka?.." kallon yanda kayanta suke a saman gado tayi tana mamakin yanda akayi ta cire kayan ta, can bayan ta zurfafa tunani tace "waɗannan kayan masu uban zafi daman taya zan iya kwanciya dasu, mantawa kawai nayi ina buƙatar shan iska.." ta sauƙa daga saman gadon taje gaban madubi ta tsaya tana kallon kanta, ita bata kawo komai a ranta ba saima tuno da Mommy datayi a asibiti tareda Junaid, hawaye ne suka fara mata go slow asaman fuskar ta, taga bisani ta goge hawayen ta shige cikin toilet tayi wanka da ruwan zafi sakamakon ciwon da jikinta ke mata, ta fito ta shirya tsab ta zura ƙatoton hijab har ƙasi tayi sallah kafin ta tashi ta fice daga cikin ɗakin, tunani tayi gwara kawai taje asibitin taga meyake faruwa duk da tasan zata fuskanci wulaƙanci ga kuma yunwar da take ji amma bata buƙatar cin komai a halin yanzu...

tana fito wa harabar gidan kai tsaye hanyar da zai sadata da gate ta nufa, sai da tayi tafiya mai ɗan nisa kafin ta iso bakin gate hijab ɗinta na jan ƙasa,
Baba maigadi ne ya fito yana faÉ—in "ke! ke ina zakije kina ganin duhu ya gabato?.."
tace "zanje dubowa mommy a asibiti.."
Baba maigadi yace "amma yarinya idan dare yayi ba'a samun abun hawa a wannan yanki fa.." tace "karka damu zanje bakin hanya.." ya ce "la la laaa da ƙafarki? amma yayi miki nisa daga nan ai.."
Ganin zai ɓata mata lokaci yasa tace "Baba buɗe mun gate ɗin nan zan tafi a haka, Yaya Junaid yana can yana jirana shi yace naje ni yanzu"
Baba maigadi yace "ayyo ai saiki mun bayani tin farko, zo ki wuce.." ya buÉ—e mata ta fice,
tafiya take da sauri- sauri saboda unguwar shuru ba kowa sai hasken nepa ta ko ina amma gidaje a ƙarƙame da gate, unguwar GRA kenam, da haka ta isa bakin hanya a tsorace, tana zuwa ta tari mai adaideta sahu ta hau sai asibitin Doctor Fateema..

suna isowa da sauri Ayush ta sauƙa zata shige cikin hospital saboda secuirity bakin gate sun hana shiga da abun ƙarfe ciki saidai idan ma'aikatan asibitin ne,
mai keke napep ne ya kwalla mata ƙira yana faɗin "Hajiya kin manta baki ban kuɗina ba.." jin haka yasa Ayush tsayawa ta juyo tace "nawa ne kuɗin?" yace "ɗari biyar ne, kinsan da daddare ba'a ɗauka sosai..."
Ayush dai tsayawa tayi tana kallon mutumin, ga ba sisi a hannunta, sai cewa tayi "malam dan Allah kayi hakuri banida kuÉ—i wallahi...." kafin ta rufe baki ya katse ta da cewa "a'ahh wallahi ba wannan maganar kawai dai ki ban kuÉ—ina yawwa.." Ayush cikin sassanyar murya tace "toh shikenam jirani zan kawo maka kuÉ—in ka yanzu.."
yace "toh ina jiranki yanzu"
ta shige ciki tana gudu ita burinta taga majinyatan a wani hali suke.
tana shiga can cikin compound na asibitin ta tarar da Angel tana tsaye ta jingina da jikin gini kai a sama,
Aditi da Rumana kuma suna a zaune, har Aditi ta fara gyangyaÉ—i domin so suke suga farfaÉ—owar Junaid kafin su wuce gida, Mommy kuwa sun san wannan sai anyi da gaske tukun..
jin shugowar Ayush yasa suka juyo suna kallonta, Rumana kam kallo É—aya tayi mata taja dogon tsuka sannan ta kawar da kanta gefe, itama Aditi tana kallo Ayush ta maida kanta tana cigaba da baccinta, Angel kuwa kanta a sama tana kallon ceilling ko kallon Ayush batayi ba sakamakon dogon tunani data zurfafa bata ma san Ayush ta shugo ba...
itama Ayush tsayawa tayi bata ce musu ƙala ba ta samu ɗaya daga cikin kujerun wajen ta zauna, ƙirjinta kuwa na bugun uku-uku a tsorace take gaba ɗaya, tunanin kalar wulaƙancin da Junaid zaiyi mata take yi, ta saddaƙar ƙarshen barinta gidan kenam, bazai cigaba da zama da ita ba, itama zufafa tunaninta tayi suna cikin wannan halin suka ji ance "hajiya ya zaki shanya ni a waje kince zaki karɓo mun kuɗina..." Ayush firgitt tayi har ta tsorita da jin maganar mutumin mai keke napep, kamar zata yi kuka tace "haba bawan Allah ba'a temako ne?.." yace "dakata hajia nifa ba temako na fito yiba yauwa neman kuɗina na fito yi, ina zaune ba mai temaka mun nima..."
Aditi da Rumana kam ko kallon wajen basuyi ba saboda ba jin abunda suke faÉ—a sukeyi ba, kwata-kwata basu iya hausa ba,
Angel ce kawai ta iya hausa sosai saboda ta zauna a cikin hausawa,
ta kalli yanda suke tace "meyake faruwa ne?"
kafin Ayush ta buÉ—e baki har mutumin ya kora mata jawabai, Angel bata ce musu komai haka ta buÉ—e handbag É—inta ta ciro 1k ta bawa mutumin tace "gashi nan kaje kawai..."
mai napep washe baki yayi yana godiya ya kalli Ayush yace "hajiya saida safe koh..." ko kula shi batayi, ta kalli Angel tace "nagode..." bata kai ƙarshe ba suka jiyo likita yana cewa "zaku iya shugo wa Ogah Junaid ya farfaɗo tin ɗazu ya samu hutu ne yasa ba'a ƙira ku ba.."

da sauri suka miƙe cikin room ɗin da Junaid yake ciki, Ayush kawai aka bari zaune a gurin ta kasa tashi ma, gabanta sai yanke wa yake,

bayan sun shiga Aditi da Rumana ne suka zauna a bakin gadon da yake, Angel kuma tana tsaye sai murmushi take ta zubawa, tana farin cikin tashin Junaid,
shima yana zaune har an cire masa ledar ruwan da aka É—aura masa, kwata-kwata ba annuri a fuskarsa, su kuma sai masa sannu suke suna gaishe shi da jiki, baya iya ce musu komai sai kawai É—aga musu kai yake, ya kalli yanda Angel take a tsaye yace "ina mamana?.."
Angel tace "tana other room ta samu yin bacci ne, amma da zarar ta tashi za'a sanar maka.." tayi masa wannan dabarar ne saboda kar yace zaije ya dubata, gashi ba'a barin kowa ya shiga sai likitoci..

kaɗa kansa kawai yayi, gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi, yana zaune ya kasa cewa komai, suma duk cikinsu ba wacce ta ƙara yin magana, sake ɗagowa yayi ya kalli Angel yace "ke bakya gajiya da tsayuwa ne? ko sojoji basa gajiya ne.." murmushi tayi tana kallonsa cike da mamakin yanda ya canza lokaci guda, tace "ina zuwa..." ta juya ta fice daga cikin ɗakin..
shi kuwa binta yayi da kallo har ta ƙule masa kafin ya kawar da kansa ya maida kallonsa kan su Rumana da Aditi waɗanda suke zaune daf dashi a bakin gadon..

bayan wasu seconni sai ga Angel ta shugo tana riƙe da hannun Ayush,
har suka iso gaban gadon da Junaid yake a zaune,
tin shugowarsu Junaid ya kafa idonsa akan Ayush kamar zaiyi kuka haka yake kallonta, itama Ayush fuska yayi jaga-jaga da hawaye ga idonta ya kumbura sosai tsabar kuka haka suka tsaya suna kallon juna ido cikin ido.

Aditi da Rumana kamar zasu haÉ—iyi ransu tsabar takaici sai suka tsaya suna kallonsu,
Angel kuma ba abunda take sai murmushi,
sarkin murmushi kenam bata fushi......

𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️

𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔

the wife of a tiger🐅🐅🐅

𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️

𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871

*💫💫{{N W A}}💫💫*

Book two

C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 003 ➡️ 004

Kawar da kansa gefe Junaid yayi daga kallon Ayush,
Angel ce tayi wa su Aditi magana ta turanci tace "ku taso to suna son yin magana.." Rumana ce ta juyo tana watsawa Angel harara da waɗannan blue eyes ɗinta, itama Aditi ƙara curɓune fuska tayi tana faɗin "ba yanda zanje ni, ayi komai a gaban mu" ajiyar zuciya Angel tayi tana kallon Junaid ko zaiyi musu magana, amma ko juyowa baiyi ba yana kallon gefensa,
Angel ce tayi wa Ayush raÉ—a a kunne tace "ki zagaya ta gefen da yake kallo.." Ayush kallon Angel tayi da sauri tana girgiza kai tace "ina tsoro kar ya mareni.." turata Angel tayi tana faÉ—in "jeki ba abunda zaiyi miki"
gaba ɗaya jikin Ayush a mace yake batada wani ƙwari haka take jan sawayenta daƙer kamar mai tambayar ƙasi,
Rumana ƙara juyowa tayi ta harari Angel tareda faɗin "munafuka kawai kinason haɗa abunda bazaiyu ba" murmushi kawai Angel tayi bata tanka mata ba..
Chapter 2 · 0% Book details