← Book details Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 85

Sashe 16

Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kafin su rufe baki saiga motar Sojoji sun kai uku suka diddirƙo da manya-manyan bindigoginsu suka tsattsaya saiga Ogah Junaid shima ya fito yana sanye da wandon Soja da kuma farar riga t-shirt yaje gaban Angel ya yi mata ɗaukar luɗa yana ɗauke da ita yace wa D.P.O "she's a commander of soldiers, California Army..." yana kaiwa ƙarshe maganar sa yayi gaba da ita ya buɗe cikin mota ya kwantar da ita a back seat,
duk abunda ya faru akwai wani abokin Junaid wanda yake wajen yayi video ya turawa Junaid,
shiga cikin motar yayi shima yaja motar ya tafi da ita gida, har wannan lokacin cikin Angel bai daina ciwo ba,
saiji tayi yace "nace miki ki tafi da wasu Soja ku kamo mutumin amma kin tafo ke É—aya ai dole ya raina ki..."

Sauran Sojojin kuma jawo Sauro sukayi daga cikin motar police suka sakashi a cikin motarsu suka tafi,
Ƴan sandar dake wajen basuyi mamaki ba saboda yanda sukaga Angel tana faɗa har cakawa Ogansu wuƙa tayi a ƙafa daman sunyi zargin tanada wani muƙami...

*******

Ayush sauƙowa falo tayi ta samu Mommy tana jera kuloli akan dinning daman yunwa take ji kuma saita fito a daidai,
Mommy tana ganinta tace "ha'a Ayushert kin fito ne, gashi kuwa na kammala girkin zo ki zauna ki ci ko.."
Ayush kasa magana tayi sai dai ta nufi dinnig ta zauna a kujera, ga tabo a goshi yanda Junaid ya buga mata shi ajikin bango, Mommy cikin tausayawa take kallon Ayush tana maganar zuci "kin kusa ki huta Ayush gobe Junaid zai tafi kafin ya dawo kuwa zan gama saita komai.."
ta zuba wa Ayush a plate tace "gashi nan Yarinyar kirki kici kisha magani ko saboda ciwon goshinki..."
Ayush É—aga mata kai kawai tayi tareda É—ago da spoon zata sa abinci a baki,
Dai dai lokacin da Junaid ya shugo falo yana É—auke da Angel,
Mommy na ganinsu a haka tace "subhanallahi meya faru da ita?.."

Kwantar da ita Junaid yayi akan doguwar sofa yace "rigima tayi da wani yayi mata duka.."
ya ƙarasa maganar tareda nufar gurin dinning domin yunwa yake ji,
har saida ya zauna zai zuba abinci ya lura da Ayush, É—agowa yayi yana kallonta,
itama kallonsa take cike da fargaba da tsananin tsoronsa domin ta tabbatar yanzu Junaid ba ƙaunarta yake ba tinda har ya furta da bakinsa...

Kawar da kansa yayi gefe yana ɗan ƙwala spoon akan glass table sai yake ɗan bada sound yana ɗan cije maroon lips ɗinsa ya ambaci sunanta a hankali "Yushert..."

kallonsa kawai take domin tin zuwansa gurin ta dakatar da cin abincin,
yace "wacece ke?.."

wani irin tambaya yayi mata wanda ita kanta saida ta É—an razana, still kallonsa take ta kasa buÉ—ar bakinta,
yace "Yushert abunda banaso kenam idan nayi wa mutum magana ɗaya inaso ya amsa mun ne akan lokacin, ki kwantar da hankalinki magana nake so nayi dake ta fahimtar juna, ki faɗa mun gaskiya bana son ƙarya da salon yaudara..."

Ayush hawaye ta fara zubar wa domin tasan maganar bazai wuce akan video nan ba,
tana cikin wannan tunanin taji yace "wacece wannan matar mai niƙab wacce tazo a ranar shagali na??"

Gaban Ayush ne yayi matuƙar bugawa da ƙarfin gaske sai wani daram-daramm kake ji, sauran kaɗan ya hana zuciyarta bugawa, ta zaro ido waje ta kafe shi da kallo..

Shima kallonta yake yi yace "ina jinki..."
Girgiza masa kai kawai tayi babu bakin magana,
ya kuma cewa "Yushert wacece matar nan da kike ƙiranta da Uma?..."
nan ma shuru tayi mishi girgiza masa kai kawai take,

Jinjina kai yayi ya kawar da kansa gefe cike da takaici domin ya tsani yayi wa mutum magana ya tsaya yana kallonsa, still juyowa yayi idonsa akan nata ya kuma cewa " Yushert wacece matar da ta ɓace bayan ta fito daga ɗakin ki?.."
wannan lokacin kam Ayush har da sakin fitsari tana zaune bata ma san tanayi ba,
sai ƙarar zubar fitsarin kake ji yana sauƙa akan tiles tsuuuuuu🤣🤣🤣

Ogah Junaid kam jin sauƙar fitsarin ne yasa ya leƙa ƙasan kujerar da take zaune yaga fitsari yana zuba, shi yayi tunanin kofin ruwane ya zuba daga saman table, ɗagowa yayi yana kallonta cike da mamaki yace "Yushert bakida gaskiya kenam? meye manufarki na zama tareda mu? kinyi ƙaryar cewa bakida kowa ashe ke ba mutum bace, ashe ke ahalin Aljanu ce?, toh meyake tafe dake? inaso in sani yanzun nan.."

lokaci guda hawaye duk ya wanke mata fuska, idonta yayi jawur tana lumshe su a hankali domin ita kaÉ—ai tasan irin tashin hankalin da take ciki...
ya kuma cewa "Yushert magana fah nake miki.."
Ayush ko ƙwakkwaran motsi ta kasa yi..
Ran Junaid ne yayi matuƙar ɓaci ganin tinda ya fara magana ko amsa ɗaya bata bashi ba,

Cikin zafin nama Junaid ya ɗaga hannayensa biyu da ƙarfin gaske ya doka a tsakiyar glass table na cin abinci
Glass dinning ne yayi wani irin ƙara ya dagargaje,
tsabar firgici da tashin hankali da kuma tsoro haka kujerar Ayush ya faɗi ta baya ta doku a ƙasi nan take ta fara wani irin shaƙuwa tana fitar da jini daga bakinta, ta zazzaro ido waje tana kallon sama tana shaƙuwa da ƙarfin gaske ga yanda taketa ambaliyar aman jini...

Mommy tana zaune a kujerar da Angel take a kwance duk saida suka razana da jin ƙarar fashewar glass table, a gigice Angel ta miƙe tsaye alokacin ma taji babu ciwon cikin,
zuciyar Mommy ne yake bugawa da ƙarfin gaske tsabar tsoritar da tayi duk suka nufi gurin da gudu!
Mommy tana faÉ—in "nashiga uku meya faru kuma du Junaiddd..."
Angel ganin yanda Ayush take kwance ido a ƙafe ga shaƙuwarta yanda yake dukan dodon kunnuwansu,. da sauri ta durƙusa tasa hannu ta tallafo kayinta tana ƙiran sunanta "Ayush! Ayush!! Ayushert!!! meya faru da ita haka..."

Mommy kam tsayawa tayi tana kallon yanda Ayush take tayi tama rasa yanda zatayi gaba É—aya ta ruÉ—e, ta rasa mai zatayi É—aya...

Shi kuwa Junaid yana zaune idonsa akan Ayush ya kasa motsawa shima jikinsa duk yayi weak, ga hannayensa duk sun faffashe sai jinin da yaketa zubarwa, ba ƙaramin ciwo yaji ba...

Angel ce tace "Mommy mu gaggauta kaita hospital dan Allah, zata iya mutuwa fah..."
agigice Mommy tasa hannu zasu É—auki Ayush! Junaid ya katse su da cewa "kar ku yadda kuje hospital, ku kaimun ita room É—ina..."

Mommy tace "baza mu barta a gida ba, ciwo ba ƙaramin ciwo ba, idan baka sonta toh ni ina sonta, kar ka ƙara shiga shirgin Ayush daga yau! babu ruwanka da ita ko meye zatayi, ai ba kai ka kawota gidan ba kuma ba'ace wannan gidan naka bane gidan mahaifinka ne, idan kuma kana gadara da gidan mahaifinka ne toh zamu fita mubar maka gidan inyaso zanje na sayi gidan da zan zauna da Ayusher....."
Mommy tana kuka haka ta ƙarasa maganar tana riƙe da Ayush zasu huce Junaid ya miƙe a tsawace yake faɗin "ita ɗin ba mutum bace Aljanace, bamu san meye manufarta akan mu ba, ta ce batada iyaye ashe ƙarya take iyayenta Aljanu ne..."

Angel da jin wannan batun tayi saurin kwantar da Ayush taja da baya tana mammannewa ajikin bango,
Angel a rayuwarta bata son shiga harƙar Aljanu, tana mungun jin tsoron Aljanu, a duniyar nan ba abunda tafi jin tsoro kamar Aljanu, lokaci guda jikinta ya fara rawa tana kakkarwa! tinda tayi gamo da Aljani a asalin suffar su marasa daɗin gani daga nan take yawan mafarki mai ban tsoro na Aljanu kuma bata son taji an ambatu sunan Aljanu...

Mommy gaban Junaid taje ta tsaya tace "meye hujjarka na cewa Aljana ce? shin kofato ka gani a ƙafarta ne ko meye? toh bari na gaya maka ko ita mayyace mai cin naman mutane zan zauna da ita, saidai kabar gidan nan ko kuma ni nabar maka gidan amma Ayush ba yanda zataje a cikin gidan nan, ƙafarta ƙafata don haka karna sake jin wannan batun a bakinka,
Kuma last warning idan ka sake musguna wa rayuwar wannan yarinyar ko kuma ka sake dukanta toh wallahi wallahi saina tsine maka, kuma nabar maka gidan...."

Juyowa Mommy tayi ta kama Ayush zata É—agata tace wa Angel "zo ki tayani mu É—agata hospital za'a kaita.."
Angel tana manne da jikin bango tace "a'ah Mommy bazan iya ba..." muryar ta na kakkarwa kamar mai yin zazzaɓi,
Mommy tace "Angel kodai cikin nakin ne?.."
dasauri Angel tace "eeeeh ciki nane..."
Mommy tace "toh shikenam Allah ya yaye miki.." tayi ƙoƙarin ɗaga Ayush suna tafiya a hankali zasuyi waje...

Da gudu Angel ta wuce É—akinta taje tasa sakata..
Mommy har sun doshi ƙofar fita daga falon taga an ɗaga Ayush sama dasauri ta waiwayo taga Junaid ne ya ɗorata akan kafaɗarsa yana kallon Mommy yace "am sorry Mom banaso akaita hospital kuma du ace mun ta ɓata, ki ƙira Doctor yazo har gida yayi mata magani..."
yana kaiwa haka ya juya ya nufi upstairs da ita, kai tsaye room É—insa ya shiga..

Mommy tsabar takaici kasa cewa komai tayi sai tsaya kallonsa da tayi har ya kule mata,
zama tayi akan kujera tayi tagumi...
Lokaci guda ta zabura ta miƙe da sauri taje ta ɗauki phone ɗinta ta ƙira number Doctor Samuel emergency...

Tana katse ƙiran tajiyo jiniyar motar sojoji, zama tayi akan kujera bata bi takansu bama,
Sojoji guda uku ne suka kawo Sauro bayan sunje an cire masa bullet a ƙafarsa,
shugo dashi sukayi kai tsaye part É—in horo suka wuce dashi, suka zaunar dashi akan chair suka É—aÉ—É—aureshi da igiya a jikin kujerar,
Sai nishi yake tayi tsabar azabar daya sha a hannun sojojin kafin su kawo shi,
suna gama aikinsu sukayi tafiyarsu, daman Ogah Junaid yace musu a gidansa zai hukunta shi...

Sojojin nan suna tafiya saiga motar Doctor Samuel ya tafo da kayan aiki,
Angel ce ta fito da gudu ta wuce Mommy a falo ta fice waje,
Mommy sake baki tayi tana kallonta tace "ohhhh mai ciwon ciki..."
Chapter 16 · 0% Book details