← Book details Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 85

Sashe 75

Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Doctor Hasheem ba karamin razana yayi ba jin abunda ya faru da Lailah, daman yana hospital yana duba majinyata yazo zai fita da gudu yaga ashe itama Lailah har an iso da ita, a rikice ya karɓeta sai cikin emergency room,
Shima Doctor Mansur ba karamin ruɗewa yayi ba jin Lailah tana asibiti, ba shiri shima ya nufi hospital ɗin Doctor Hasheem ba abunda yake furtawa sai "innalillahi wa inna ilaihi raju'un ².."
da haka har ya isa.
kafin a ankara Daddy da Ammy da Maimoon har sunji labari suma ba shiri suka nufi asibitin,
Lailah saida tayi ƙwana biyu tana kwance tukun Allah yasa ta farfaɗo, kafin ta gama buɗe ido bakinta ya fara motsi tareda faɗin "Yaya ka dena dukan Ogah Junaid dan Allah, meya maka hakane, zaka kashe shi fah...". Jin haka yasa Doctor Hasheem nufan gurin dasauri yana ambatar sunanta, Lailah ƙoƙarin tashi zaune take, Doct Hasheem ne ya ɗagota zaune yana kallon ta tareda cewa "Lailah kin gane ni?..."
bugan ƙirjinsa tayi tana murmushi tace "haba Yaya idan ban tuna dakai ba shin wazan tuna, nifa ban manta komai ba..."
Doct Hasheem yace "amma naji kina ambatar sunan Ogah Junaid shin kin sanshi ne?..."
Lailah cike da mamaki take kallon Doct Hasheem tace "Haba Yaya taya zan manta Ogah Junaid, tsohon saurayina ne fah, shine mutum na farko dana so a rayuwata, amma Yaya nayi mamaki taya abubuwan baya suka dawo mun ƙwaƙwalwata? yanzu ina iya tuna komai abunda ya faru a baya, tayaya Yaya? shin ina Ogah Junaid fatan ya samu lafiya koh? amma Yaya inadai baka illata shi ba dukan da kayi masa, naji tausayinsa sosai, toh ina kuma Ayushert take kodai ta gudu kashe mommy datayi ta hanyar gobara, naje na bayar da dukkan rahotannin ta agidan rediyo, an kamata ne?..."
Doctor Hasheem tsayawa yayi yana kallonta cike da farin ciki memory sense É—in Lailah ya dawo mata, amma abun fargaba shine kar Lailah ta dawo da soyayyar Junaid cikin zuciyarta,
Lailah murya na kakkarwa tace "Aunty Maimoon.." tana kallon wajen da Maimoon take zaune itama Maimoon tasowa tayi tazo har wajen gadon Lailah tace "Lailah your welcome..". Lailah tana kuka tace "Aunty Maimoon kiyi haƙuri da laifin da muka aikata miki..." kafin ta ƙarasa Maimoon tayi saurin toshe mata baki tareda cewa "abunda ya wuce ya wuce kenam, ki cigaba da tsara rayuwarki na yanzu, Ogah Junaid ki manta dashi kawai yanzu Aure zakiyi..."
Lailah dariya tayi tace "daman ai kawai na tuno ne amma rayuwata ta yanzu tafi mun, a baya abubuwa marasa kyau na rinƙa aikatawa yanzu kuma Insha Allahu zan zamo uwa ta gari wa ƴaƴanta...." Duk sunyi farin cikin jin abunda Lailah ta faɗa, shima Doctor Mansur yana daga gefe har jikinsa yayi sanyi amma jin har yanzu Lailah tana tare dashi yasa ya sauƙar da doguwar ajiyar numfashi, shima ya nufi wajenta yana murmushi itama ganinsa yasa tace "mijina na kaina, kayi haƙuri lokacin da mota ta bugeni ina sauri ne zan koma gida shiyasa ban jira kazo ka ɗauke ni ba...". shafar gefen fuskarta yayi ba tareda yace komai ba sai murmushin farin ciki...
Suma su Daddy da Ammy sunyi farin cikin dawowar sense É—in Lailah....

suna cikin hirarsu sai sukaji an turo ƙofar ɗakin gaba ɗayansu kallon bakin ƙofar sukayi ganin yaro ya shugo,
Doctor Hasheem yace. "kaii zo mana..". yaron yazo har gabansa ya riƙe hannunsa yana cewa "daga ina kake, meye sunanka?..."
Rapeekh dake zaune saman cinyar Ammy yace "Laaaa Daddy shine Abokina wanda nake baka labarinsa class É—in mu É—aya dashi kuma kullum sai munyi faÉ—a...."
Doctor Hasheem ya kalli yaron yace "kaine Areeph?.." Areeph dasauri ya É—aga masa kai alamar ehh,
ya tambaye shi meye full name ɗinsa, Areeph kamar bazaiyi magana ba daƙer ya iya cewa "Máahmud Junaid Khan..."
Jin sunan abunda ya ɗaure wa Doctor Hasheem kai, cike da mamaki yace "sunan Babanka Junaid Khan Máahmud?...". dasauri Areeph ya ɗaga masa kai,
Doctor Hasheem kallon Lailah yayi yace "wannan yaron Ogah Junaid ne..."
A zabure Lailah tace "yaron Ogah Junaid kuma? Innalillahi haka yaran suka girma, yaushe ne mukaje hidimar sunansu...."
suna cikin tattaunawarsu saiga Ayush ta shigo É—akin kamar zata kife tayi sallama, duk suka juyo suna kallonta bayan sun gaisa tace "Areeph inata nemanka ban ganka ba...".
Doctor Hasheem ne yace "Malama Ayushert your welcome...". cike da mamaki Ayush take kallon Doctor tace "Doct Hasheem kaine? Daman kana ƙasar?..."
yace "wallahi kuwa ina Nam tsawon shekaru bamu sake haÉ—uwa ba"
Zama tayi suka fara tattaunawa akan yanda rayuwa ta juya dasu, Doctor Hasheem ya kwashe labarin abunda ya faru dashi har zamansa a prison ya sanar mata, tayi matuƙar tausaya masa sosai, itama ta bashi labarin tafiyarta bayan tabar gidansa ta koma daji da zama har tayi zaman prison itama,
Zaro ido Doct Hasheem yayi yace "kema kinyi zaman prison ne?...". tace "ehh amma zaman wata uku nayi kai kuma gashi har tsawon shekara huÉ—u...".
Lailah tace "Aunty Ayusher..." Ayush ta kalli Lailah tace "Lailah ashe abunda ya faru dake kenam?..." ta amsa mata tace "toh Allah ya tsare gaba..." Duk suka amsa da Ameen...
Doctor Hasheem yace "amma Ayush meya kawo ku hospital..."
tace "wallahi satin mu guda a asibitin nan, na kawo Areeph bashida lafiya...". yace "Allah Sarki kinga kuma ina zuwa nima amma ban lura daku ba, nadai ga Ogah Junaid jiya shida Malam Lawan amma iya gaisuwa mukayi ban tambayesu abunda ya kawo su ba saboda naga suma sunada iko da asibitin ....". ya kuma cewa "toh amma meya same shi ne?..."
Tace "Babansa ne yayi masa dukan mutuwa don har saida ya suma..." ta buÉ—e ma Areeph riga duk ta nunnuna musu yanda ya faffasa masa jiki...
Girgiza kai Doctor Hasheem yayi sannan yace "innalillahi wa inna ilaihi raju'un irin wannan dukan ai yayi tsari a yaro ƙarami irin wannan, gaskiya Ogah Junaid bazai taɓa canzawa ba, har yanzu yana nan da wannan zafin ran nashin..."
Lailah wani irin ƙololuwar baƙin cikine ya ziyarci cikin zuciyarta ganin yanda Ogah Junaid yayi wa yaronsa, ko kaɗan bataso taga ana dukan yaro, sam ba ƙaramin haushin shi taji ba...
Kowa a wajen saida ya tofa albarkacin bakinsa....
Rapeekh yaron Doctor Hasheem yace "shiyasa bana ganinsa a makaranta yanzu, kuma a ajinmu an bamu result É—in jarabawar mu na canjin aji, Ni nayo na É—aya..."
Ayush tace "kai kayo na ɗaya? shima Areeph an karɓo result ɗinsa shima na ɗayan yayo kuma abin ku ɗaya?..."
Doctor Hasheem yace "ehh ajinsu ɗaya mana akwai wani malamin su yana gaya mun cewa dole sai an sake musu jarabawa a iya tsakaninsu domin kowannen su yanada ƙoƙari sosai sai anyi musu inter biyu..."

Areeph ya kalli Ayush yace "mommy aini bazan taɓa faɗuwa a exam ba..."
Shima Rapeekh yace "nima bazan taɓa faɗuwa ba..."
A haka sukayi wasa da dariyarsu suka fice a É—akin,
A ranar aka sallami su Ayush suka koma gida,
Masha Allah Areeph duk ya rage abubuwanda yake yi a baya, kuma tsoron Daddynsa ya ziyarci cikin zuciyar shi, duk abunda aka ce masa yayi da hanzarinsa zaiyi, Amma saidai har yanzu akwai wannan zuciyar da kuma idan aka masa magana baya saurin bada amsa wannan ajininsa yake amma akwai ladabi da biyayya yanzu kam....
Chapter 75 · 0% Book details