← Book details Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 85

Sashe 7

Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

daƙer Angel ta samu ta kuɓuce a hannun Aditi ta fito tana maida numfashi ta nufi gurin da Rumana take a zaune ta hankaɗata ƙasi ita da kujerar,
Aditi ce itama ta fito daga cikin ruwan da gudu ta nufo yanda Angel take ta kamata da kokuwa suka fara kirɓawa juna naushi, Rumana itama tasowa tayi ta shiga suka fara faɗa kowa wanda yake jin haushi yake daka,
a wannan lokacin Aditi tayi nasarar gurɗa ƙafar Angel sakamakon kwantar da ita datayi ƙasa ta kama ƙafarta ta murɗe mata shi, har saida Angel ta saka ƙara sosai tana kwance ta kasa motsa ƙafar,
Aditi ganin Rumana tana ƙoƙarin cakumo ta yasa ta zari ƙwalbar lemo ta rausawa Rumana a goshi, nan da nan jini ya fara kwararowa daga goshin Rumana, baturen mutum da baya son ganin ciwo a jikinsa hakan yasa Rumana faɗuwa ta sume a gurin...

Aditi tashi tayi tana huci tareda faɗin "ku taso mana inadai kun raina ni ko? toh zan nuna muku ni mahaukaciyar soja ce, ku taso..." tana haki da ƙarfi-ƙarfi tana fitar da maganar daƙer kamar wacce tayi aikin ƙarfi..

Junaid ne yazo gurin yana faɗin "ku kuma kunzo nan duk kun tare guri ɗaya kun bar falo babu kowa....." bai kai ƙarshen maganarsa ba yaci karo da Rumana kwance ko motsi babu ga kuma jini ya wanke mata fuska, yakai idonsa kan Angel sai juye-juye take tana riƙe da ƙafarta tana kuka,
kallon yanda Aditi take a tsaye tana huci yayi bakinsa na kakkarwa tsabar ɓacin rai yace "meya faru dasu?..."
juyowa tayi tana fuskantarsa hannu a dunƙule tace "nine nam nayi aiki akansu, idan kuma kaima kana son tabbatar da aikina kazo ka ga..." tana tsalle irin na ƴan dambe...

da sauri yayo kan Rumana ganin tafi jikkata, da gudu Aditi ta shige gabansa tana faɗin "babu wacce zaka taɓa" tureta yayi gefe sannan yasa hannu zai ɗauki Rumana sai ji yayi Aditi ta kirɓa masa naushi a baya, cikin ɓacin rai ya juyo tareda zabga mata mari, zata kawo masa naushi kuma du ya riƙe hannayenta biyu da hannu ɗaya ya zaro ƙafafunta da ɗayan hannun ya cillata cikin ruwan swimming pool,
ya juyo ya ɗauki Rumana a kafaɗarsa, sannan ya miƙawa Angel hannu ta tashi daƙer ya riƙe kunkuminta da ɗayan hannunsa, ɗayan kuma yana riƙe da Rumana yanda ya saɓata a kafaɗa haka suka nufi falon gidan, Ańgel tana ɗingishi daƙer take takawa..

suna shiga cikin falon mommy da Ayush duk suka miƙe tsaye daga zaune,
Mommy cike da mamaki tace "subhanallah ya haka kuma?..." ganin yanda suke ba kaya a jikinsu ko wacce daga pant sai breziya, Ayush kam rufe idanuwanta tayi da hannayenta biyu,

Junaid ne yace "mom please ki biyo mu can medicine room kiyi treat É—insu, sunji rauni sosai...."
Mommy ce ta taɓa Ayush tana faɗin "kije ɗakunansu ki dubo musu kayan sakawa yanzun nan.." tana kaiwa karshe tabi bayan Junaid da sauri...

Bayan Ayush ta jido musu kayan sakawa tana fitowa falo saiga Aditi ta shugo falon ita da kayanta a jikinta domin tin acan ta sanya su, tana zuwa ta wuce É—akinta tana jan zuciya ga idonta yanda sukayi jaa.....

𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️

𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔

the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅

𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️

𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871

*💫💫{{N W A}}💫💫*

Book two

C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 009 ➡️ 10

Junaid da sauri ya fito falo ya nufi yanda frig yake ya buÉ—e tareda É—aukar ruwan faro mai sanyin gaske ya koma yanda ya fito,
ita kuma Ayush bayan ta kai musu kayan komowa tayi falon ta nemi guri ta zauna tayi tagumi kamar wata marainiya,
bayan wasu mintuna saiga mommy ta fito hannunta riƙe dana Angel tana ɗingishi, sai Rumana dake tafe duk goshinta an zagaye da bandeji, shi kuma Junaid yana biye dasu a baya, Ayush ganinsu yasa ta miƙe da sauri tana kallonsu tareda faɗin "sannunku ya jikin nakun?.." Angel ce ta amsa murya ciki-ciki, ita kuma Rumana ko ƙala batace ba haka ta wuce ɗakinta,
mommy da Angel da kuma Junaid neman guri sukayi suka zazzauna, itama Ayush É—in zama tayi idonta akan Junaid domin bata gajiya da kallonsa, shima yana lura da kallon da take masa saidai baya bari su haÉ—a ido,

gaba É—aya wajen yayi tsitt ba wanda ya kula kowa acikin su sai Angel ce data kalli yanda Junaid yake ta faman press phone É—insa tayi gyaran murya, murya a sanyaye tace "my Man ya batun sarki Raamud ne?.."
É—agowa yayi yana kallonta yace "baki sanar mun komai akansa ba har yanzu.."
kallon yanda mommy take Angel tayi sannan tace "munyi bincike sosai akansa sannan mun gano cewa matar data zauna daku a matsayin Æ´ar aikinku matarsa ce, wato Bara'atu..."

a zabure Junaid ya miƙe tsaye tareda faɗin "whatttt...?"
itama mommy saida ta girgiza dajin wannan batun,
Ayush ido ta zaro waje tana binsu da kallo, zuciyarta kuwa haka yake bugun uku-uku,
Angel tana bin Junaid da kallo tace "ba abun mamaki bane dan ance matarsa ce, saboda bakinsu É—aya kuma shi ya turo ta nan gidan domin ta shiga cikin rayuwarku ta misguna muku"
ta kuma cewa "ka zauna mana mu ƙarasa maganar..."
jiki a sanyaye ya zauna yana cewa "ina jinki Angel.."

ta kuma cewa "yarinyar da Bara'at tabar gidan nan da ita ƴarsu ce kuma sunanta Mayushat, a yanzu dai basa tareda yarinyar kuma gaskiya bamu gano a yanda take ba, amma guaranty Sarkin matsafa yana tareda matarsa Bara'atu a halin yanzu, sannan bincike ya nuna cewa yanzu babu wani tasirin da suke dashi na tsafi, zamu iya kai musu farmaki a koda yaushe, tawagar mu tana kan shirinta domin zuwa farmakar su, an sanar wa sojojin nan nigeria da kuma na pakistan da sojojin china da na UK da US duk akan su shirya ranar 5 ga watan November 2023, next week kenam, jirgin land army da kuma airpos na Nigeria zai tashi a ranar Monday, zamu fara shirin mu daga yau friday zuwa monday domin damu za'ayi wannan tafiyar, sai kuma mu dage da addu'a domin a tafiyar yaƙin namun bamu san mai zamu tarar ba, bamu san waye zai mutu ba waye kuma zai rayu..."

Junaid kallon Angel yake cike da baƙin cikin sarki Raamud a cikin zuciyarsa,
buɗe baki yayi yace "a shirye nake dana yaƙe shi, kuma ni zan zamo ajalinsa..."

Angel ce ta katse shi da cewa "a'a shuwagabannin mu basu bada umarnin a kashe shi ba, da ransa suke son ganinsa.."
Junaid miƙewa tsaye yayi yana darara wa Angel tsawa tareda faɗin " i will kill him with his wife, babu wanda ya isa ya dakatar dani, sai dai nayi sanadiyar rasa aikina da kuma rayuwata, amma saina kashe mutumin daya azabtar da rayuwata, saina kashe matar da tayi sanadiyar mutuwar mahaifina, sannan kuma bazan taɓa ƙyale ɗiyarsu ba, saina nemo ta a duk yanda suka ɓoyeta..." yana kaiwa haka ya bar falon ya haura upstairs...

Ayush tana zaune jikinta ne ya hau ɓari tana rawar sanyi, wani irin zazzaɓi ne mai zafin gaske ya rufeta, tinin hawaye har ya cicciko mata, zuciyarta yana bugu da ƙarfin gaske,
ganin kuka yana shirin kuɓuto mata yasa ta tashi da sauri itama ta haura upstair zata koma ɗakinta, tana shiga kuwa ta danna sakata a ɗakin ta faɗa saman katafaren gadonta tana rera kuka na gaske..

Junaid kuwa toilet ya shige, ruwa ya kwara a kansa yayi wanka shap-shap ya fito ya shirya cikin wandon soja da farar t-shirt, ya zura takalminsa sahu ciki irin na sojoji, ya feffesa turare sannan ya fice da sauri ya sauƙa down stairs,

Mommy da Angel ne suka miƙe tsaye a zabure ganin Junaid yana shirin ficewa,
Mommy tace "ina zaka je Junaid?..."
juyowa yayi yace "zanje headquarters ne domin na tantance ƙarfafan sojojin da za'ayi tafiyar dasu ba lusarai ba..."
yana kaiwa haka yayi ficewarsa, a gigice yaje ya shige motarsa ya fizgeta da gudun gaske,
maigadi daman tin fitowar Junaid yayi saurin buÉ—e masa gate...

Mommy tana daga tsaye ta kalli Angel da damuwa a fuskarta tace "wallahi Angel ina tsoro kar wani abu ya cutar mun da yarona, har ina ne ƙasar da zakuje?..."

Angel ta sauƙe ajiyar zuciya tana hura iskar bakinta tace "ki kwantar da hankalinki mom insha Allahu ba abunda zai faru da Junaid, ai jarumin namiji ne ba'a yaƙarsa sai dai ya yaƙi mutum, kuma ƙasar da za'a hallaru acan domin gudanar da yaƙin can ƙasar California ne, toh masarautar babu kowa yanzu haka sai su, babu mutane ko ata gefensu ne, waran dai ya kasance daji ne..."

Mommy tace "toh shikenam Allah dai yasa aci nasara akan su, a kamosu dumu-dumu..."
Angel tana murmushi tace "ai zamu ci nasara tinda sojojin da zasu hallara ba kaɗan bane, sojoji ƙasashe daban daban ne zasu zo domin gudanar da farmaki...

Ayush tashi tayi daga kwance tana zazzagaya cikin room É—inta tareda faÉ—in "innalillahi wa inna'ilahi raju'un, shikenam iyayena nashiga uku nah, Allah ka karemun iyayena, taya zan sanar musu cewar su tafi? ta ina zan sanar musu cewar su gudu kafin ranar? ga yanzu babu tsafin da zanyi magana dasu ta cikin madubi, meye ake shirin aikata wa iyaye nane?..."
tana magana tana kuka sosai gaba É—aya ta susuce..

Around 6 o'clock bayan anyi sallar mangrib
Angel ce ta fito ta gama shirya musu dinner na kayan abinci, sai data kammala tsab tukun taje É—akin mommy ta tarar da ita akan sallaya ta idar da sallah,
Angel ta mata magana akan ta fito su ci abinci, mommy ta amsa mata da "toh"
Chapter 7 · 0% Book details