← Book details Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 85

Sashe 50

Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ayush tana zaune acikin ɗakin da aka ajiyeta, ɗakin sun kai su goma aciki kowa da shimfiɗarsa kamar boading skull, ga an sauya mata kayan jikinta ya koma irin na sauran ƴan matan prison riga da wando iri ɗaya kowa da number a jikin rigarsa, kowa yana ƙwakkwance amma banda Ayush wacce take zaune a shimfiɗarta sai rera kuka take sakamakon yanzu dare ne misalin ƙarfe 12Am, duk ta cika musu kunne da kuka wata mata ce ta taso a zabure tayo kan Ayush tana masifar cewa "ke duk kin hanamu bacci, bama son sakalci fa kowa ma ba son zaman nan yake ba, dan haka ki rufe mana baki ko kisha mazga yanzun nan...."
Ayush ko sauraronta batayi ba saima ƙara volume ɗin kukan take, matar ce ta ɗagota tareda zabga mata mari har sau biyu tana faɗin "wallahi tallahi zan fitarki waje kika ƙara mana kuka .."
Ita kuwa Ayush tinin ta haɗiye kukan ta sai hawayen dake zubo mata ba ƙaƙƙautawa,
ɗaya ce daga cikin prisoner girl tace "haba Mimi ki ƙyaleta mana bakiga tanata juna biyu bane, kiyi mata uzuri dan Allah, kowa ma farkon zuwansa haka yayi..."
Mimi tace "bazan ƙyaleta ba Hafiza, idan kina mun shishshigi kema saina ci jatuminki, kina nam ƙarama dake sai iyeyin banza, ita kuma wannan idan na sake jin kukanta saina fasa mata baki wannan alƙawari nane babu ruwana na cikinta..."
tana kaiwa nan ta ƙwanta a wajenta tana surutan ta har bacci ya kwasheta,
Itama Ayush ƙwanciya tayi data ga ba wani sarki sai Allah duk da sauron dake ɗakin bai dameta ba saboda ta saba da zaman daji, batayi tsammanin zata zauna a prisoner ba.
Washe gari duk matan prisoner kowa ya fito da kwanonsa suna zuwa yin layin karɓan abinci, banda Ayush dake ƙwance a ɗaki ta kasa motsawa sai kuka, wata yarinya ce tazo kusa da ita takai hannu tana tattaɓata da sauri Ayush ta ɗago tana kallonta, yarinyar tace "kina ƙwance ki taso muje mu karɓi abun breakfast..."
daƙer Ayush take motsi da bakinta tace "bana buƙatar cin komai..."
yarinyar tace "idan bakije ba babu wanda zai saurareki balle ya kawo miki har yunwa tayi miki illa, ni idan naje da kwano biyu bazasu bani ba ki daure ki tashi muje kodan jaririn dake cikin ki..."
Ayush haka take bin yarinyar da kallo tana mamakin yanda akayi yarinya ƙarama tazo prison, gashi shekarunta bazata wuce 17 zuwa 18 ba, jinjina kai Ayush tayi tace "shikenam zanci ne saboda yarona..." haka ta tashi suka tafi tare da yarinyar har gurin karɓan abinci ga kayansu iri ɗaya mai launin sky blue..
Bayan sun karɓi abinci zama sukayi a wani waje su kaɗai yarinyar a hankali take feeding Ayush sakamakon yanayin abincin bazata iya ci ba saida dabara,
Bayan sun kammala breakfast yarinyar ce ta soma magana tana bawa Ayush labarinta tace "Ni sunana Hafiza asalin ƴar Kano ce, iyayena talakawa ne futuk sai nayi tallah muke samun abinda zamu ci, ƙwatsam wani saurayi ɗan gidan attajirai ya ganni yace yana sona, ni kuma a lokacin inada wanda nakeso shima talaka ne amma saidai yanada ƙwalin degree ɗinsa amma babu aikin yi, ni kuma a iya sacondary na tsaya, iyayena suka tilasta mun akan saina Auri ɗan masu kuɗi bana sonsa haka akayi mun Auren dole dashi, ƴan uwansa basa son mu ƙyamatar mu suke suna ƙiran mu da ƙazamai, da haka akayi auren aka kawoni nan garin Abuja, a daren farko na dashi ban yadda masa ba, haka nake gudunsa, a cikin daren nan na fito daga cikin ɗakin dake upstairs ne ina sauƙowa ƙasi shima yana biyoni a baya kwatsam tsautsayi ya rubta dashi ƙafarsa ta zame daga saman beni ya buga kansa da tiles, lokaci guda kayinsa ya fashe bama iya fashewa bama tsagewa kayin yayi daga lokacin bai ƙara motsi ba rai yayi halinsa...."
ta ƙarasa maganar tareda fashewa da kuka ta cigaba da cewa "shine ƴan uwansa sukai ta cewa ni na kashe shi wai, wallahi bani na kashe mijina ba, sun fimu arziƙi nesa ba kusa ba hakan yasa aka yanke mun hukuncin zaman gidan prison har tsawon ƙarshen rayuwata....". kuka ne yaci ranta sosai, Ayush itama kukan take domin ba ƙaramin tausaya mata tayi ba, gata ƙaramar yarinya, haka Ayush ta jawota jikinta tana rarrashinta, ita yanzu tama daina damuwa da kanta tinda a cikin prisoner har da ƙananun yara...

*BAYAN WATA 3*

Ayushert ta rigada ta sabarwa rayuwarta a cikin prisoner, yanzu ta daina damun kanta da yawan kuka, ga sun shaƙu sosai da Hafizat ta mayarta tamkar ƙanwarta ta jini komai tare suke yinsa, akwai abunda Hafiza bata barin Ayush tayi shine irin su wanki da ɗaukar abu mai nauyi duk Hafiza ke yinsu sakamakon cikin Ayush ya girma sosai, domin cikin yanzu watansa takwas, duk wasu ayyukan bauta da ake sakawa an bada umarnin kada a saka Ayush a ciki, yanzu hankalinta a ƙwance yake ba kamar farko-farkon zuwanta ba, kowa sai yace zai hantareta ita da Hafizat..
Damuwarta shine abu ɗaya wato Junaid tana mamakin yanda tsawon watannin nan amma baizo ya dubata ba, kuma sai take zargin anya lafiyarsa ƙalau, shine kawai damuwarta, amma malam Lawan yakan zo mata wasu lokuta, tana tambayarsa Junaid amma sai ya sanar mata cewa yana nan lafiya ƙalau, a yau ne daya zo yake sanar mata cewar tin lokacin da aka kawo ta prison Junaid yake kulle a gurin mutanensa sojoji,
Ayush tasha kuka sosai jin haka....

******

Duk tsawon wata ukun nan Junaid yana kulle a ɗakin dake quarters, Marshal yaƙi bari a fito dashi wai sai matarsa ta haihu a prison tukun, Abinci kuwa sai an daideci yana bacci tukun a buɗe a hankali a ajiye masa tukun a sake kulle ɗakin, shima haka rayuwarsa yake tafiya shi kaɗai a cikin ɗaki, zaman kaɗaici ya dameshi ga wayarsa tana hannunsu, yayi masifar! yayi barazana!! yayi magiyar!!! yayi kukan har ya gaji, ga yanaso ya sanya Yushert ɗinsa a ido amma babu hali, yayi matuƙar kewar matarsa Yushert, shi kaɗai yasan kalar raɗaɗin da yake ji a cikin zuciyarsa, sannan ya ƙudurta a ransa cewar da zarar ya fito duk saiya ƙona headquarters ɗin gaba ɗaya, babu abunda zai rage a cikinta tinda har zasu masa wannan wulaƙanci da tozarci...

Malam Lawan yayi zirga-zirga wajen sojojin nan akan subar masa Junaid ya tafi dashi amma sun ƙi da haka har ya gaji ya daina zuwa,

******

Ata ɓangaren mommy da sarki Raamud sunata shirye shiryen dawowa Nigeria, duk da basu san abubuwan dake faruwa ba, Mommy murna kamar bazata mutu ba tana son dawowa gurin yaranta, ga tayi missing ɗin Junaid ɗinta, sun yanki Visa gobe da safe jirginsu zai tashi...

*TEAM ƊIN JUNAID DA TEAM ƊIN AYUSH NACE BAA HOW MARKET 🤪🤪🤪🤪🤪🤪🤪*

𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️

𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔

the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅

𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️

𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871

*💫💫{{N W A}}💫💫*

Book two

C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 57 ➡️ 58

Today is Monday Around 2pm jirgin su Mommy suka sauƙa a Nigeria,
Mommy murna kamar bazata mutu ba har ɗaukin ganin yaranta take kamar zata fura, Allah! Allah take ta isa gida, sarki Raamud ya fahimceta duk wannan saurin so take taje gida murmushi kawai yayi ba tareda yace komai ba, shima kansa mamakin kansa yake yana maganar zuci "wai yau nine a Nigeria? Allahu Akbar Aure mai haɗa zumunta...". suna tafe a motar haya domin babu motar a hannunsu, har suka ƙariso ƙofar gida, ganin yanda gidan ya rurrushe yayi baƙi ƙirin yasa mommy cewa "Yaa Salam haka gidana ya koma? kuma Junaid baiyi ƙoƙarin gyarawa ba? toh yanzun acikin gidajensa wanne ɗaya ya koma sai Allah...."
Sarki Raamud shima kansa abun ya bashi mamaki ganin yanda gidan ya ƙoƙƙone, baiyi tunanin har abun yakai haka ba yana jinjina kai yace "yanzu ya za'ayi mu samu Junaid?.."
Mommy ta juyo tana kallonsa cikin nuna damuwa tace "yanzu haka idan nace zan sauƙa nayi tambaya sai suce zasu firgita domin a tunaninsu na mutu ne, ni kuma nafison nabi abu a sannu har su gane cewar ba mutuwa nayi ba..."
Sarki Raamud shima idonsa akanta yace "hakane toh amma yanzu meye abun yi?.." da sauri mommy tace "ahh! muje gidan malam Lawan..". cikin rashin fahimta yace "waye malam Lawan kuma?..." Mommy tace "idan muka je zaka ganshi, daga nan sai in baka labarinsa"
murmushi yayi sannan yace "okay..."
suka sa mai motar ya juya mommy tana masa ƙwatance har suka isa gidan malam lawan...
Chapter 50 · 0% Book details