← Book details Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 85

Sashe 49

Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ayush ce a gaban General da Marshal da sauran sojoji masu manyan miƙami da kuma ƙananun sojaji duk suna tsaye bayan sanar musu da abunda Ayush tayiwa ɗaya daga cikin sojoji, a tsawace General yake tambayarta dalilin da yasa tayi haka, amma Ayush tayi shuru babu bakin magana kai a sunkuye sai faman kuka take, daiden lokacin da Junaid ya shugo da motarsa da gudu, da sauri yayi parking ya fito ganin yanda aka taru ga kuma Ayush a durƙushe a rana, da gudu ya iso gurin baiyi magana wa kowa ba sai nufan gurin da Ayush take yayi, yana zuwa yasa hannu ya ɗagota tsaye yana goge mata hawayen fuskarta da hannu,
ji yayi Marshal ya darara masa tsawa tareda faɗin "umarnin wa kabi ka ɗago da ita? shin meye matsayinka a yanzu da har zakayi mana wannan shishshigin...". Junaid bai kulashi ba yana kallon Ayush yace "Yushert what happened to you?.." kuka ne yaci ranta sosai tasa hannu ta rungume shi, shima rungumarta yayi rai a ɓace domin baiji daɗin ganin Ayush a wannan yanayin ba, General ne ya katse shi da cewa "Junaid mai kakeyi haka, waya baka izinin shugowa wannan quarters?..."
kallonsa Junaid yayi sannan yace "sorry Sir but what happen to my wife? meyasa zakuyi mata wannan hukunci? ku bari kotu ta yanke mata hukunci ba ku ba..." Marshal yayi saurin katseshi da cewa "kaii ka kama bakinka, kasan da wanda kake yiwa magana, General ne a gabanka..."
Junaid cikin fushi ya dakawa marshal tsawa da cewa "and so whattt? banda Allah babu wanda nake jin tsoro saidai nayi biyayya nabi dokar aiki." ya ƙarasa maganar tareda kallon yanda canal yake yace "tell me what's going on?..."
Canal nuna naseer yayi da yatsa yace "matarka ce ta yanke masa yatsu guda huÉ—u..." Junaid ya kalli Naseer yace "whatt? amma me yayi mata?.."
Canal yace "muma bamu saniba yaƙi yin magana kuma itama taƙi cewa komai" Junaid ɗago da Ayush yayi daga jikinsa yana kallonta yace "Yushert!.." ɗagowa tayi tana kallonsa itama ya kuma cewa "meya haɗaki dashi? kar kiji tsoron kowa ki buɗe baki kiyi magana babu abunda zai faru dake, ko waye bai isa yayi miki abunda Allah baiyi niyar miki ba..."
Ayush murmushi tayi ta ɗanyi nisa da Junaid kaɗan kafin ta ɗaga murya tana faɗin "Yaya Junaid ba wai tsoron su ne ya hanani yin magana ba, kawai dai inaso nayi magana ne a gabanka ka duba mun shin Abunda na aikata daidai ne ko kuskure...." ta kalli sojan ta nuna shi da yatsa tace "wannan mutumin idan shine zai riƙe ƙasa toh tabbas duniya bazata zauna lafiya ba, idan yasu ne zasu kare ƙasa toh kuwa saidai ayita mutuwa domin basu da wani daraja da kima, sannan basu san mutuncin mace ba, idan kuwa zasu iya lalata rayuwar mace to kuwa zasu iya yin lalata da mahaifiyarsu,
idan kuwa haka sojoji suke Allah ya wadaran su, idan haka soja yake bashida imanin da zai tausayawa mace ko yaro ko tsoho toh Allah ya tsine masa aikinsa bashida wani amfani, sai gadarar riƙe bindiga..."
Marshal ne ya katseta da cewa "kee ba'a ce kici mana mutunci ba don kina gaban mijinki to karki manta shima mijin nakin ai soja ne..".
Ayush tana fuskantar Marshal tace "ehh mijina soja ne amma ba irin lalatattun sojojin nan ba kamar waÉ—anda suka tsargu..."
Marshal ne zai nufo gurinta cikin zafin nama yana cewa "ke karfa kimun rashin kunya domin mijinki ma da kike gadara dashi a ƙasana yake yanzu kuwa an sallame shi gaba ɗaya bakuda bakin magana..."
General ne ya dafa kafaɗansa yana masa alamar sauƙowa..."
Junaid murmushi yayi yana kallon Ayush domin ba ƙaramin burgeshi tayi ba, yanzu babu wannan tsoron natan, zata iya tsayawa a gaban kowa tayi magana, yace "Yushert colm down kije kan maganarki kai tsaye..."
alamar voting tayi masa sannan ta cigaba da cewa "ina zaune yazo yana mun magana cikin rashin ɗa'a da daraja, a matsayina na mace kuma matar Aure shin ya kamata yayi mun maganar fasiƙanci? a'ah abun ya wuce fatar baki har hannu ya kawo yana shafa mun jiki da sunan saina biye masa yayi lalata dani, hakan yasa na yanke masa yatsun hannu saboda na koya masa darasin rayuwa...."
Junaid a zabure yace "whattt?..." zuwa yanda take yayi yasa hannu ya zabga mata mari ya riƙe mata kafaɗu da hannayensa biyu yana fuskantar ta rai a ɓace cikin ɗaga murya yace "hakan shine abun burgewa?..."
sauran sojojin da suke wajen abun ya ɗaure musu kai ganin yanda Junaid yake ganin laifinta, suna cikin wannan tunanin suka ji yace "amma kin cuceni Yushert, naso ace wuƙar da kika zara caka masa kikayi a maƙogaro, meyasa zaki tsaya a iya hannu? meyasa baki yanke masa wuya ba?..." kamar zaiyi kuka haka yake jijjiganta...
wanda aka yankewa yatsu ne ya soma magana cikin kakkarwar murya yace "wallahi ƙarya take...." kafin ya rufe baki Junaid yayo sufa kamar Damisa ya cabke masa wuya, da iya ƙarfinsa yake matse masa maƙogaro har saida yakai shi ƙasi, duk sojojin wajen ne suka rufu akan Junaid suka ƙoƙarin janye shi amma sun kasa, wani irin ƙarfin bala'i ne da Junaid, ko girgiza bayayi tsabar ƙarfinsa daya danna akan wuyan Naseer,
haka yake kakakin mutuwa ido sun fito waje, sai shure-shure yake numfashinsa a ɗage cakk, Junaid yana ƙoƙarin murɗe masa wuya akayi saurin kawo Alluran macewar jiki da sauri aka caka masa, daga nan ne akayi nasarar janye shi daga kansa, shi kuwa Naseer tinin ya suma kaɗan ne ya haka ya mutu domin inda anyi kuskuren jinkirin kawowa Alluran nan da Junaid ya karya masa wuya...
Junaid gaba ɗaya ya fita hayyacinsa sai cewa yake "ku barni na kashe shi, ku ƙyaleni nace, gaba ɗayanku zan kashe ku idan baku sakeni ba, zan kashe ku! zan kashe ku!! zan kashe kuuu!!!..." da haka shima ya sume a wajen sakamakon temporary da jikinsa ya ɗau ga kuma Allurar da aka masa,
sai a lokacin sojojin suka sake shi tareda É—aukarsa suka nufi cikin É—akunan quarters dashi...

Junaid wani irin zuciya ne dashi wanda lokaci guda hankalinsa zai bar jikinsa da zaran ransa ya ɓaci matuƙa, kuma ƙarfinsa ƙaruwa yake a lokacin,
dake Jinn sun shafeshi tin lokacin da sarki Raamud yake turo masa su, bayan hakan jinin tiger ya rigada ya gudana da jininsa dole da zaran ransa ya ɓaci abun zai ɗan motsa masa, amma ba kamar baya ba...
shiyasa General baya shiga sabgarsa sosai saboda gudun ɓacin ransa, iya marshal ne kawai yake fafatawa da Junaid dake shima yanada zafin rai amma bai kamo ƙafar Junaid ba...

Bayan shigar da Junaid cikin room marshal ne ya damƙi damtsen Ayush ya shigar da ita cikin mota shima ya zagaya ya shiga da gudu ya finciki motar suka tafi kai tsaye kotu suka nufa, sai kuma wasu motocin sojoji da suka biyo bayansu,
Naseer kuma hospital aka kai shi.

Bayan 10hours an gama Shari'a! malam Lawan ma ya halacci kotun, ba'a yanke hukunci ba amma an bada horo É—aya, Ayush zata zauna a gidan gyaran hali har ta haihu, bayan ta haihu ne za'a sake zama a kotu anan za'a yanke hukunci,
Bayan an fito da Ayush za'a tafi da ita prisoner faɗuwa tayi ta fara burburwa a ƙasi tana juyi tareda zunduma ihu, wasu mata ne suka rirriƙeta suna shirin ɗagota amma sam taƙi shiga cikin mota, kamar wata mai Aljanu haka take ihu tana faɗin "wallahi bazanje prison ba! wallahi bazanje prison ba, wayyo Allah nah Yaya Junaid, nashiga uku ku temake ni wayyo Abbanaaa, Ummanaaa..."
kokuwa take dasu tana kai musu duka suma haka suke janta, ganin matan bazasu iya shigar da ita cikin motar ba yasa soja ɗaya yazo ya kimkimeta, shima haka take yakushinsa tana cizonsa tana kurma masa ihu da haka ya sakata a cikin motar aka rufe da ƙarfi, har aka tada motar suka tafi da ita tana wannan ihun, har muryarta yana shirin dishewa, fuskarta duk ya yi jawur tsabar kuka,
Malam Lawan yana tsaye a gurin saita yayi hawaye shima rai a jagwalgwale ya shiga motarsa ya tafi...

Acan ɓangaren Junaid kuma farfaɗowa yayi yana ambaton sunan Yusherttt gani yayi babu kowa a cikin ɗakin da aka ƙwantar dashi, tsararren ɗaki ne na hutawar manya-manyan sojoji ga sanyin A.C yanda yake ratsa shi ga kuma mashigar toilet ta gefe guda, da saurinsa ya tashi ya nufi bakin ƙofa zai buɗe ya fita, cike da mamaki yake bin ƙofar da kallo ganin an kulle ta waje, babu hanyar fita, da ƙarfi yasa hannu ya naushi ƙofar tareda yin ihu a fusace, ganin ƙofar bazai buɗu ba yaje ya samu guri a bakin gado ya zauna tareda dafe kayinsa da hannayensa biyu yana kallon ƙasi....
yana nan a haka har dare basu zo sun buɗe masa ba, kuma suna jin yanda yake ta buga ƙofar yana ƙiraye-ƙirayen sunayensu amma babu wanda yaje ya saurare shi domin bin umarnin Marshal,
shi ya sanar musu cewar kada su kuskura su buÉ—e masa É—akin har washe gari, saboda yana tunanin zaije ya É—auko Ayush ne da zaran an barshi...

*******
Chapter 49 · 0% Book details