Sashe 68
Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Around 12 0'clock na dare Ayush tana zaune akan sallaya bayan ta idar da sallar dare tana jan carbi, shi kuma Ogah Junaid yayi shame-shame akan gado sai shan baccinsa yake, bai ma san Ayush ta tashi ba har tayi sallah daman kullum saita tashi cikin dare tayi sallah,
tana zaune kwatsam sai taji cikinta yanata juyawa da ƙarfin gaske, wani irin ƙara tayi game da kama cikin tana hura iskar bakinta a wahalce, wani ruwa taji yana ƙoƙarin zubo mata kamar meyin fitsari dasauri ta janye sallayar da take kai ta wurga gefe, nan danan rigarta ta ɓaci da jini, ga paya ta fashe wani irin murɗa take ji ga raɗaɗin ciwon ciki, gaba ɗaya ta fara fita hayyacinta, daƙer ta rarrafo bakin gado tasa hannu tana bubbugan Junaid dake ta shan baccinsa, shuru ko motsawa beyi ba, haka take kuka tana ta faman jijjigansa saidai yeyi juyi ya sake komawa bacci, ƙiran sunansa take a wahalce tana faɗin "Yaya Junaid ka tashi mana, cikina ciwo wayyo Allah, Yaya Junaid zan mutu ka tashi dan Allah, ka temaka mun cikinaaa..."
Junaid kuwa baima san tana yi ba, wani irin nannauyar bacci ne ya É—auke shi,
Kuka take tana shure-shure, bata san lokacin data ƙwanta tana birgima ba, haka ta sake tashi daƙer ta kamo hannunsa tana jansa amma saidai ya tureta sannan ya juya ya cigaba da baccinsa, ga duk ta ɓaci da jini!
Ganin bashi da niyar tashi yasa ta kama gadon daƙer ta tashi taje saitin kayinsa ta kafa bakinta akan kunnensa da ƙarfi ta garzaya masa cizo,
A firgice ya juyo a rashin sani ya zabga mata mari har saida ta faɗi ƙasi yana kame da kunnensa ya juya ya cigaba da baccinsa, shi a tunaninsa duk mafarki yake yi, a cikin mafarkin yake jin shessheƙar kuka amma ya kasa farkawa, saima jan pillow da yayi ya runguma a madadin Ayush, ya ɗauka ita ya runguma,
Ayush tana kuka ta soma rarrafe ta nufi hanyar fita daga ɗakin, ta kasa miƙe wa tsaye sakamakon cikinta da mararta sun riƙe babu halin tashi ita kaɗai, haka ta rarrafa daƙer ta buɗe ƙofar ta fice,
A zaune take jan mazauninta tana sauƙa daga kan beni duk yanda taja sai wajen ya ɓaci da jini, da haka tayi nasarar sauƙa daga beni na uku, saida ta huta tukun ta cigaba daja tana ƙoƙarin sauƙa a beni na biyu, in cikinta ya juya saita ɗanyi ƙara ta jinkirta kafin ta cigaba da ja da gindi, tana kaiwa ƙarshen beni na biyun ta ƙwata a wajen saida ta gama juye-juyenta bayan ya ɗan lufa kuma du ta soma ƙoƙarin sauƙa daga beni na ɗaya shine na ƙarshe wanda zai sadata da babban falo, daƙer tana kuka da muzurai ta ƙarasa sauƙa falon tana ja a zaune,
saida tazo tsakiyar falo zata nufi ɗakin mommy cikinta yayi wani irin juyi da ƙarfin gaske, taji wani abu kamar dutsi ya sauƙa mata ƙasin marar ta kamar zai fito ta farjinta a gigice ta saki wani irin ihuu sai a dodon kunnen mommy tayi sujjada kenam, ƙirjin mommy ne yayi wani irin bugawa a rikice take karanto addu'o'i acikin sujjadar amma ta kasa ɗagowa,
Hafzat itama idar da sallar ta kenam don ko addu'a bata fara yi ba taji wannan ihun, a ruɗe ta miƙe tsaye tareda addu'a,
kafin ta motsa ta ƙara jin wani ihun ana ƙwalla ƙiran sunan mommy,
a tsorace Hafzat tace "Innalillahi kamar Aunty Ayusher..." tayi hanyar fita da gudu, kai tsaye cikin falo ta nufa tana zuwa ta tarar da Ayush ƙwance ta naɗe sawayenta jin abu yana shirin faɗowa,
kuka take tana faÉ—in "wayyo Allah nah kayan cikina zasu zubo, kuzo ku temake niiii, mommy kayan cikina zasu zubooo..."
Hafzat itama ta tsorita sosai haka ta rinƙa zarya acikin falon ta kasa aiwatar da komai sai yarfe hannayenta take tareda faɗin "wayyo Allah mun shiga uku Aunty Ayusher ɗinmu zata mutu, wayyo Allah jini ta ko ina Aunty Ayusher zuba yake, dan Allah kar ki mutu..."
sai kuka itama take tayi kuma ta kasa taɓa Ayushert, suna cikin wannan halin saiga Mommy ta tafo da gudu kamar zata kife haka ta nufi gurin Ayush ta ɗagota tareda faɗin "Kiyi haƙuri haihuwa ne, ki ware sawayenki..."
Cikin kuka Ayush tace "wallahi bazan ware sawayena ba kayan cikin zubowa zasu yi, kuma mutuwa zanyiii..."
Mommy tace "ki ƙwantar da hankalinki yanzu hospital zamu kai ki, Ayush taya zan ɗagoki bayan kin tuƙwiƙwiye kamar maijin sanyi ki sake jikinki mu samu damar ɗagoki..."
"wallahi mommy kayan ciki nane zasu zubo idan na sake jikinaa..."
Mommy ganin Ayush zata iya kashe jaririn indai ba'ayi saurin kaita hospital ba yasa ta cewa Hafzat "riƙe mun hannayenta Ni kuma saina kama ƙafafuwanta mu ɗagata.."
Hafzat jiki na kakkarwa tace "wallahi mommy bazan iya ba tsoro nake ji..."
A fusace mommy ta daka mata tsawa tareda cewa "ki kama mun hannayenta mu fita da ita waran motar shine aiki?..."
fashewa Hafzat tayi da kuka ta kasa motsawa, itama Ayush kuka take sosai tana faɗin "wayyo Allah kayan cikina zasu zazzaɓoo ku temake niiii..."
Gaba ɗaya mommy ta rasa yanda zatayi ga Ayush taƙi sake jikinta balle ta ɗagota su fita, ga kuma jini yaƙi tsayuwa..
suna cikin wannan halin saiga Judan ya fito dasauri jin kururuwa yayi yawa yana sanye da baƙar jallabiya ya ƙaraso gurinsu yana faɗin "lafiya kuwa meyake faruwa ne..."
Mommy a gigice ta riƙo hannunsa tana daɗin "haihuwa ne munaso mu kaita hospital ne, temaka ka ɗauketa mu tafi dan Allah..."
Hannu Judan yasa ya ɗauketa tana ƙara tuƙwiƙwiye kanta saboda kar kayan cikinta su zubo..
da haka aka fita da ita har wajen parking, nan danan Judan ya tada motar suka miƙi hanyar gate,
Ayush tana bayan motar kanta yana kan cinyar mommy, ita kuma Hafzat tana gaban motar suna isa wajen gate security ya yi saurin buÉ—e musu suka fita da gudun gaske sai hospital....
Shi kuwa Junaid yana nan rungume da pillow bai san wainar da ake tuyawa ba, sai ana ƙiran Asuba nan ma saida ya kusan makara ana shirin shiga sallah ya yi saurin tashi yana miƙa tareda jero addu'o'i, idonsa a lumshe ya zuro zara-zaran sawayensa ƙasi yana shirin tashi, kai tsaye toilet ya miƙa ya ɗauro Alwala sannan ya fito tsabar bacci yana cin idonsa bai lura da Ayush bata nan ba haka ya ɗauki jallabiyarsa ya zura yayi hanyar fita tareda faɗin "My Yushert shine yau ɗin kikayi sallarki baki tasheni ba koh?..."
Daiden lokacin da ya buɗe ƙofa ya fice bai saurari ko za'a bashi amsa ba, yana sauri kar a shiga sallah ya rasa jam'i, dake kullum Ayush ce take tashin shi sallar Asuba, ana ƙiran farko zata tashe shi,
Duk bai lura da jinin dake É—akin ba amma ba lallai ya gane cewa akwai jini ba saboda carpet ne irin mai dark É—in nan da kuma gashi-gashi a jiki,
Amma Benin kam duk tiles ne indai ya kalli ƙasi dole zai gani...
Shima Abban duk kururuwan da akaita yi acikin daren baiji ba dake part É—insa da É—an rata kuma a lokacin ba wai bacci yake yi ba shima yana sallar daren,
A harabar gidan Abban ya haÉ—u da Junaid sai faman sauri yake zai fita a tare suka tafi masallaci...
★★★★★★★★
A lokacin da aka kai Ayush labour room ihu take tana ƙiran sunan Yaya Junaid, a lokacin yaron ya jikkata sakamakon maƙurashi da tayi har ya daina motsi, saida aka mata wani Allura wanda zaisa yaron motsawa,
Itama mommy rigar likitancinta ta sanya ta shige É—akin,
Judan da Hafzat kuwa a waje aka barsu suna zazzaune,
Ana ƙiran Asuba daƙer Ayush ta haifo santalelen yaronta, ƙato dashi fari tasss kamar balarabe,
tana haifansa kuwa ta suma, mommy farin ciki kamar bazata mutu ba, ganin Ayush bata motsi yasa suka É—auko Allurar kashe jiki zasu yi mata Operation sakamakon akwai wani yaron a ciki, kuma a halin yanzu bazata iya amfana ba,
hakan akayi saida aka ciro mata jarirai biyu bayan wanda ta haifa kafin,
An samu Æ´an uku
Namiji É—aya shine wanda ta haifa da kanta,
sai kuma mata biyu bayan an mata Operation,
Amma ba ƙaramin wahala Ayush tasha ba, bata cikin hayyacinta kwata-kwata,
haka aka shiga gyara yaran gwanin sha'awa gasu triplets rass...
★★★★★