← Book details Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 85

Sashe 54

Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mommy tana rungume da Ayush bata san lokacin data suma ba, sai nauyinta data ji yayi over ga tilin tumbi Mommy har tana shirin faɗuwa ta tattaro iya ƙarfinta a hankali ta kai Ayush ƙasa saboda bazata iya riƙeta a tsaye ba, zaro ido waje mommy tayi tareda faɗin "nashiga uku me kuma ya faru dake Ayushert?..." tattaɓa fuskarta ta soma yi amma shuru Ayush ko motsi, fashe wa da kuka mommy tayi tana neman agaji ƙiran mutanen wajen ta soma yi, duk aka rufu akanta amma an rasa wanda zai taɓata suna cikin wannan halin saiga su Junaid da malam Lawan sun shugo da sauri sakamakon sanar musu da akayi a waje, a ruɗe Junaid yasa hannu ya ɗagota yayi hanyar waje da ita, masu tsaron prison ne suka bi bayansa suna son dakatar dashi, har zai buɗe murfin motar suka dakatar da shi da faɗin "ba'a bada umarni a fitar da mai laifi a cikin wannan prison ba, wannan kuskure ne..." Junaid ya juyo yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya sannan yace "baku ga a halin da take ciki bane?..." suka ce duk da haka sai an bada umarni tukun, su Mommy ne suma suka ƙaraso wajen da sauri cikin damuwa take faɗin "dan Allah kuyi haƙuri mu kaita asibiti idan baku yadda damu ba saiku biyo mu muje tareda.." wani ne daga cikinsu yace "okay amma kafin nan sai kun bada information nakun.." a lokacin suka bada sannan suka shiga motar kai tsaye hospital suka nufa da ita tareda security guda biyu... Ranar a hospital suka kwana, iya malam Lawan ne kawai ya koma gida amma Junaid da Mommy da kuma sarki Raamud duk a asibiti suka wayi gari, a lokacin da Ayush ta farfaɗo su Mommy basa nan sunje shigar da report akan Ayush na anason fitar da ita daga prison, an karɓi ƙorafinsu amma sai an sake zama a kotu an nunawa duniya cewar Doctor Fateema ba mutuwa tayi ba sannan kuma a wanke Ayush a kotu.... Bayan farfaɗowarta Junaid kawai ta tarar a kusa da ita yana zaune ya zuba mata ido, itama kallonsa take a hankali take motsi da leɓɓenta tace " mafarki nayi ko? nasan mommy bazata taɓa dawowa ba, na tamka babban kuskure a rayuwata, da hannuna na kashe mommy nima rayuwata batada wani amfani..." kuka ne yaci ranta sosai dasauri Junaid yasa hannu yana rufe mata baki tareda girgiza mata kai yace "kar na sake jin wannan batun, mommy bata mutu ba ta samu tsira ne.." hannu tasa ta zamar masa hannunsa dake kan bakinta tana ƙoƙarin ɗagowa zaune daƙer har saida ya tallafa mata tana kallonsa cike da mamaki take cewa "tayaya hakan zata faru? taya zakace mommy bata mutu ba shin ɓacewa tayi ne ko meye?..." murmushi yayi sannan yace " Narasimha..." da sauri Ayush ta ɗago tana kallonsa baki na kakkarwa ta maimaita sunan "Narasimha?..." shima idonsa akanta yace "yes ko kin sanshi ne?.." idonta akansa ko ƙibtawa batayi ta jinjina a cikin ranta take cewa "na sanshi shine yayi mun magani lokacin da na cire zobe a jikin cibiyata, kenam shine yazo ya ɗauketa..." tana cikin wannan tunanin taji Junaid yana faɗin "tunanin mai kike yi ko kin sanshi ne?..." a ruɗe tace "kenam masarauta aka kaita ta ɗebi tsawon watannin nan?.." jinjina kai Junaid yayi yana kallonta, a lokacin jikinta yayi sanyi kamar wacce aka zuba masa ruwan sanyi kai a ƙasi, daiden lokacin da su Mommy suka dawo da wasu takardu a hannunta, Ayush tana ganinsu tayi saurin ƙwanciya ta kifa kanta acikin filo domin a halin yanzu bazata iya haɗa ido da mommy ba, mommy zama tayi a bakin gadon ta ɗora hannunta akanta tana faɗin "ya hakane Ayushert ki ɗago mata na ganki nayi kewar ki, Alhamdulillah da Allah yasa kika farfaɗo lafiya duk da nasan saboda ni kika suma, kiyi haƙuri kinji ni ɗin ce mommy ba wata ba ...." Ayush tana jinta amma ta kasa ɗagowa, har saida sarki Raamud ya matso kusa da ita ya kawo kansa saitin kunnenta yana mata raɗa da cewa "Ɓingel karki nuna rashin wayo ki tashi ki nemi yafiyar ta akan abinda kika aikata mata, zata ji daɗi domin in baki kasheta bama kin tafka mata babban asara...." yana ɗagowa itama ta tashi tareda fashewa da matsanancin kuka ta sauƙa daga kan gadon ta ɗayan ɓangaren ta zagayo tareda durƙusawa ƙasi agaban mommy tana kuka tana faɗin "mommy dan Allah kiyi haƙuri akan abunda na aikata miki wallahi nima nasan banyi miki adalci ba, haƙiƙa nayi miki butulci a rayuwa domin ko mahaifiyata bata nuna mun kulawar da kika nuna mun ba, kin nuna mun soyayyar gaskiya tamkar uwar da take matuƙar son ɗiyarta, ..." kuka ne yaci ranta sosai har ta kasa ƙarisa maganar, itama mommy kuka take tana kallon Ayush cikin tausayawa tasa hannu ta ɗagota tareda rungumarta a jiki tace "kiyi shuru my daughter banson jin kukan ki, wallahi baki mun komai ba abunda kika aikata ko kaɗan banji tsanarki ba domin na ɗaukeki tamkar ƴar dana haifa a cikina, karfa ki manta ciki na fa kika ƙi sannan kika fito a cikin ƴar uwa Bara'at, saboda haka ki ƙwantar da hankalinki komai yazo ƙarshe, insha Allahu daga yau baza ki sake kwanan prison ba, my daughter na yafe miki duniya da lahira..." Ayush itama rungumar Mommy tayi tana rera kuka mai ratsa zuciya, sun shafi mintuna a haka kafin mommy ta samu nasarar rarrashinta sannan tayi mata albishir da cewa daga nan ba komawa prison, ba ƙaramin farin ciki Ayush tayi ba tana cikin murna lokaci guda ta maida fuskarta kalar tausayi a shagwaɓe tace "Mommy.." kallonta mommy take cikin kulawa ta amsa mata da cewa "na'am ƴar mommy ya akayi ne?.." tana zubda hawaye tace "missing someone very close to my heart..." Junaid cikin rashin fahimta yake kallonta fuska a ɗaure, sarki Raamud shima yana zaune akan kujera baiyi tunanin komai ba ya ɗauka ta tuno da mahaifiyarta ne, shima ba ƙaramin tausayawa ɗiyarsa yake ba amma saidai ta wani ɓangare hankalinsa a ƙwance yake tinda har Allah ya haɗasu da mommy mai ƙyakykyawar zuciya. Mommy kallon Ayush tayi sannan ta kalli yanda Junaid yake a zaune still ta maido da eyes ɗinta kanta tareda faɗin "amma waye wannan wanda kika yi missing ɗinsa haka?..." girgiza kai Ayush tayi sannan tace "ba namiji ba, mace ce na haɗu da ita ne a prison, yarinya ce ƙarama tana buƙatar temako..." Junaid ne ya sauƙe wata nannauyar numfashi a bayyane yace "thank God..." Daga Ayush har mommy tsaya kallonsa suka yi daga bisani mommy tace "lafiya kuwa Junaid?...". ɗaga musu hannu yayi tareda faɗin "no ku cigaba da hirarku..." daiden lokacin da Malam Lawan ya shugo da sallama a bakinsa suka gaggaisa sannan ya nemi guri ya zauna, ya sanar musu cewa "ranar 10 ga watan January za'a koma kotu koh?..". Mommy tace "eh ganan takardar ma amma daga nan gida zamu wuce da Ayush..." Ayush dasauri ta katse mommy da cewa "dan girman Allah mommy ku temaki Hafiza tana cikin mawuyancin hali, gashi na baro cikin prison ba tareda ta saniba saidai ta nemeni ta rasa, yarinyar ta shiga raina du Da du mah shekarar ta 18 a duniya..." Mommy zaro ido waje tayi tana maimaita kalmar "18 years old? amma ya akayi ta shiga prison a wannan ƙarancin shekarun natan?..." anan Ayush ta kwashe komai dangane da yarinyar ta gaya musu, ba ƙaramin tausaya mata sukayi ba, mommy tace "insha Allahu baza mu barta ta ƙare rayuwarta a cikin prisoner ba, zan tsaya mata tsayin daka Allah Sarki baiwar Allah, saboda iyayenta basu da kuɗi shine akayi amfani da dukiya domin aga ta tagayyara, insha Allahu hakan bazata faru ba, nima zan zubar da ruwan kuɗi domin naga ta fito ta cigaba da rayuwarta cikin aminci..." kowa saida ya tofa albarkacin bakinsa, Ayush ba ƙaramin farin ciki tayi ba jin Hafiza zata fito daga maƙarƙama.... anan suka shiga hirar su na rayuwa, mommy kaf saida ta ƙwashe rayuwar da tayi a cikin masarauta ta sanar musu ta ƙare maganar da cewa "ai wallahi banso barin masarauta ba, kawai nazo ne saboda yarana amma banda haka babu abunda zai dawo dani Nigeria..." Sarki Raamud yace "Ni ai bazan iya zaman wannan ƙasar takun ba, duk zafi yabi ya ishi mutum ga ƙura da rana bazan iyaba, yanzu idan na tashi komawa tare zamu koma ai..." ya ƙarisa maganar yana kallon mommy, juyowa mommy tayi tana kallonsa cikin gatsine tace "waa? saidai gaba ɗayan mu zamu tafi tare da su Junaid, yauwa ga ƙafata ga ƙafarsu domin bazan iya rayuwa ba tareda su ba..." Malam Lawan ba abunda yake musu inba dariya ba, Ayush itama dariya take tace "ai masarauta ba ƙaramin haɗuwa yayi ba, Ni tinda nake ban taɓa ganin tsararren masarauta haɗaɗɗe kamar masarautar mu ba ga girma, yanzu iya Yaya Junaid da malam Lawan ne kawai basu shiga masarauta baa..." Zaro ido Junaid yayi yana kallonta yace "waya gaya miki?..." Mommy tace "kin manta yaƙin da suka je neh?..." Ayush tace "wooo hakane fah ashe! Yaya Junaid ya kaga tsaruwar masarauta?..." juyar da kai gefe yayi domin shi Junaid har yanzu akwai wannan miskilancin nasan, shi baya son irin wannan doguwar hirar.. Sarki Raamud yana kallon Ayush yace "shima Malam Lawan ai ɗan cikin masarauta ne, a cikin masarauta aka haife shi kuma ya taso a cikinta..." Ba Ayush ba hatta Junaid da Mommy abun ya ɗaure musu kai, gwara ita mommy sun sanar mata a baya amma har yanzu tana mamakin faruwar hakan, Ayush cikin rashin fahimta tace "tayaya kenam? nifa malam Lawan a daji na sanshi ya zauna damu ni da mahaifiyata daga baya ya tafi domin shine ya koya mun karatun Alkur'ani da wasu abubuwa na addinin musulunci..." Shima Junaid abun ya bashi mamaki domin malam Lawan bai taɓa sanar musu haka ba, kuma shine ya bashi labarin rayuwar Ayush a daji ita da mahaifiyarta amma bai sanar masa yayi rayuwa dasu ba... Malam Lawan ne ya kalli Junaid da murmushi a fuskarsa yace "yadai Ogah Junaid kaji abu kamar daga sama koh?..." shima Junaid ɗin shi yake kallo cikin rashin fahimta. Malam Lawan yace "kar ku damu yanzu zan warware muku komai, zaku san ko
Chapter 54 · 0% Book details