Sashe 71
Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
A part É—in su Mommy kuwa suma sun gama shirinsu sauran tafiya ne ya rage musu, Abbah kamar bazai mutu ba tsabar murna da farin cikin mallakar mommy a matsayin matarsa ta sunna, kuma gashi yana É—aukin komawa masarautarsa da matarsa,
Mommy kuma ba'a son ranta za'ayi wannan tafiyar da ita ba saboda tana tunanin wahalar da Ayush zata sha waran rainon triplets, twins ma ya ake ƙarewa dasu balle har triplets, saidai dake Junaid yace mata akwai waɗanda zasu na rainon yaran, anan hankalinta ya kwanta....
A ranar kuwa aka kawo wasu mata su huÉ—u, É—aya zata na aikin girki da sauran Ayyukan gida, É—aya kuma zatana gyaran É—akuna da goge-goge da wanke-wanke da wanki kayan yara dana uwar....
sauran biyun kuma sune masu rainon yara da sauran Ayyukan gida suma,
Bayan sallar asuba su Mommy ne suka fiffito da kayayyakin su, duk suka saka su a booth ɗin motar kai tsaye suka shiga falon su Ayush, zasu musu sallama Ayush tana kuka haka suka sauƙo falo ita da Junaid tana riƙe da hannunsa, kowa ya hallara a falon mommy taje gaban Ayush tana goge mata hawaye tace "kiyi haƙuri Daughter kema ba jumawa zaki iso mu, Addu'a muke buƙata daga wajenki..."
Ayush tana kuka haka ta rungumi mommy tana faɗin "Allah ya kiyaye hanya mommy amma zanyi kewarku sosai..." itama mommy kuka take ji take kamar ta haƙura da tafiyar..
Daƙer suka raba jikinsu Ayush ta nufi gurin Abbah shima ta rungume shi tace "Abbbaaahhh..." anan ta ƙara fashewa da kuka, daƙer Abbah ya rarrasheta tayi shuru...
Itama Hafzat kuka take na rashin ganin Mommy da Judan É—inta,
Judan sai faman rarrashinta yake amma taƙi yin shuru, saida mommy tazo itama ta rungumeta tana rarrashinta tukun ta haƙura, kafin su bar falon saida suka sanyawa triplets Addu'o'i tukun, suna fita suka tarar da Uncle Artaff shima yazo yin rakiya zuwa Airport domin shi tin jiya sukayi sallama, Junaid bai samu fitowa harabar gidan ba yana can falo shi da Ayush ya rungumeta sosai a jikinsa kamar zai mayarta cikin cikinsa shima har da ƙwallarsa domin ba ƙaramin kewar ta zaiyi ba,
Bayan sun gama rungume² suka fito kowa a cikinsu jiki ba ƙwari, duk sun shiga motar shi kawai ake jira, kafin ya shiga motar saida ya rabawa Ƴan Aikin da aka kawo kuɗi kowa saida ya bata dubu ɗari bibbiyu sannan yaja musu kunne akan baya son ƙazanta da nuna rashin gaskiya, saboda haka ne yasa akaje har ƙauyen suleja aka ɗauko su domin sunfi ƴan gari riƙon Amana kuma su basu fiye zalontoma kamar ƴan cikin gari ba, itama Hafzat saida ya bata kuɗi dubu ɗari biyar yace "kuɗin kashewarta ne idan tana buƙatar wani abu, kuɗin school fees kuma idan an buƙaci hakan tayi magana za'a turo mata...". Hafzat karɓa tayi tana godiya banda kuɗin da Judan ya bata Dollars goma, ko wani guda ɗaya dubu ɗari ne idan ta canza su sun zama one million kenam, mommy da Abbah suma suka bata two millions...
Ayush kuma shi kansa Junaid baisan adadin kuɗin daya ajiye mata ba, domin suna nan jaka guda a cike da kuɗi banda wanda mommy ta bata nan ma sunfi millions goma, ga Abbah yazo ya ƙara mata da Dollars domin shi baya amfani da Naira, waɗannan sun bata ne saboda idan madarar babies suka ƙare ta siya musu, sun faɗa mata hakane saboda sun san Ayush sam bata iya kashe kuɗi ba, yanzu dubu ɗari sai tayi shekara bata kashe su ba, madarar babies suna nan kamar ruwan randa, ba'a tunanin zasu ƙare a watanni kusa ba,
Da haka sukayi sallama suka tafi, juyawa Ayush tayi da gudu tana rera kuka bata tsaya ako ina ba sai a cikin É—akinta, domin tasan bada wuri Junaid zai dawo ba, su Mommy kuwa sun tafi kenam...
Triplets kuma suna can waran masu rainon su, itama Hafzat É—akinta ta shige tana kuka,
Gidan kuwa an zuba masu tsaro kam ba laifi dake iya mata ne kawai aciki, Bodyguards saida aka zuba guda goma, baƙaƙe da fararen fata kowa yana riƙe da manya-manyan bindigu, suna toshe da baƙaƙen glass, sunci boom kai kace tinda aka halicce su basu taɓa yin dariya ba,
Ga wasu karnuka na turawa da aka zuba suma sun kai biyar, waÉ—annan manya manyan karnukan Aikinsu zagaye duk faÉ—in gidan ne, daga sunji motsi su hau haushi, sai kuma wasu daga cikin Bodyguards su yo gurin....
Hafzat da direbanta mai kaita school, fitarta a gidan sai in za'a kaita skull idan kuma ta dawo shikenam ba sake fita sai washe gari kuma du, shiyasa duk tilin kuÉ—in da aka basu suna nan a ajiye basa kashewa saboda ba'a barin kowa ya fita haka kawai, kuma duk abunda zasu siya akwai shi a gidan, duk abunda suke so akwai a gida, saidai ita Hafzat dake tana da waya ta aika kuÉ—inta bank duk aka zube mata su acikin account duk sanda ta tashi takan turawa iyayenta kuÉ—i ta hanyar transfer...
(Tabb nikam duk kuɗin da aka ajiye mun bazan iya zama ba yawo ba yaciin🙄🙄🙄 anya kuma zaku iya kuwa Reader's?....)
Rayuwa tana tafiya yanda ya kamata, abubuwa suna chanzawa zuwa hanya mai kyau, akwana a tashi yau wata biyar da tafiyar su Mommy, kullum Ayush sai tayi waya dasu ta video call acikin computer, wani sa'in kuma a cikin ƙatuwar wayarta Iphone take waya dasu, especially Ogah Junaid kusan kwana suke suna waya ta video call, hakan yana rage mata kewa sosai, yanzu Ayush saita jera sati guda bata sauƙo falo ba, abinci saidai akai mata can upstairs, daga bacci sai kuma waya da Junaid ɗinta sai idan lokacin sallah yayi ta tashi tayi acikin ɗakinta, takan motsa jiki wajen gyara cikin ɗakinta domin bata yadda ƴan aiki su shugo mata bedroom sai iya Hafzat ce kawai ta lamince mata, itama sai idan zata zo ɗaukan yara takai su wajen raino, ba'a maiso mata dasu sai idan dare yayi, tin suna wata uku ta yayesu bata basu nono sai madara, ai kuwa yaran gwanin burgewa gasu ƴan ɓulɓul dasu duk da basa shan nono...
Itama Hafzat tin da safe idan ta tafi school bata dawowa Sai ƙarfe shida na yamma dake makarantar haɗe take da Boko da islamiyya, idan ta dawo tayi wanka taci abinci sai tayi waya da Judan tukun take ƙwanciya bacci bayan nan tayi sallar mangarib...
Kuma sa'in-sa'in Uncle Artaff yakan zo gidan dubasu ko akwai wacce bata da lafiya ko kuma akwai wata matsala.....
★★★ *AFTER 3 YEARS AGO* ★★★
Ogah Junaid aikinsa ya kankama a ƙasar California, yanzu aiki yake tuƙuru na aikin General, bai tashi dawowa Nigeria ba saida yayi shekara uku kafin, domin dayaje riƙeshi akayi aka hanashi dawowa, yanzu saidai ya rinƙa zuwa hutun ƙwana biyu saiya koma,
Dawowarsa ba ƙaramin farin ciki Ayush ta shiga ba, harda kukan farin ciki, Ogah Junaid ya ƙara kyau sosai yayi fari duk wanda ya ganshi yasan ya samu kyakkyawar kulawa da jin daɗin rayuwa, shima ba ƙaramin farin ciki yayi ba ganin iyalansa cikin ƙoshin lafiya, ga yaransa sun girma sosai yanzu duk sun wuce shekara uku² da haihuwa, Ayush itama ta ƙara kyau sosai ta samu hutu tayi ƙiba, jiki ya murmure....
Hafzat tayi candy ta samu result mai kyau, dake yanzu school of Nursing ta kammala ta karanci Pharmacy na shekara biyu...
Gaba ɗayansu suna zazzaune a falo suna kallon India Film na yaƙi Ayush tana zaune a kusa da Junaid ɗinta ga yaransu ɗaya tana can ƙwance saman cinyar Hafzat, ɗaya kuma tana kan cinyar Daddynta..