← Book details Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 85

Sashe 55

Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

ni wanene a yanzu, Da farko dai sunana Artaff Zaidullah Hussein Ni ɗa ne agurin Sarki Zaid mahaifin Raamud da Máahmud ni ƙaninsu ne amma mahaifiyar mu ba ɗaya bane, su alokacin da mahaifiyarsu ta haifesu ƴan biyu Allah ya karɓi rayuwarsu, kasancewar masarautar ba'ason sarki ya zauna babu mata yasa aka Aura masa ƴar Sarkin ƙasar Iran, wato mahaifiyata Gimbiya Maryama! tinda aka haifeni Máahmud yake jana a jikinsa har na fara wayo a yayinda shi kuma Raamud yake ƙina, ko inuwarsa naje yakan hantareni haɗi da duka, koda mahaifiyata baya son zuwa yanda take daga waran mahaifin mu babu waran da yake zuwa, hakan yasa ya fara jin haushi ɗan uwansa saboda ni, haka rayuwa take tafiya yanda ya kamata har muka mallaki hankalin kan mu a lokacin ne ƙiyayya ta ƙullu a tsakanina da Raamud baya ƙaunar ganina saboda wai kar a bani mulkin masarauta, Allah Sarki ga yayuna waɗanda suka rigani shan iskar duniya taya za'a ban mulki kuma, a lokacin da mahaifin mu yake shirin sauƙa ya tara mutane ya sanar cewa zai bawa Yayan mu wato Máahmud mulkin masarauta anan Raamud ya maida ƙiyayyata zuwa kan ɗan uwansa Máahmud, har yayi sanadiyar da aka kai farmaki cikin masarautar, a ranar ni kuma da mahaifiyata munje ƙasar Iran gano mahaifinta yana ƙwance ba lafiya ciwon ajali ya riskoshi, a ranar da mahaifin mahaifiyata ya rasu a ranar saƙo ya risko mu kan cewar an kai farmaki cikin masarautar mu har anyi nasarar kashe mahaifin mu sarki Zaid, Máahmud kuma an ɓatar dashi ƙwata-ƙwata, naji ba daɗi sam na kuma yi rashin mahaifina da kuma kakana na waran uwata, Mahaifiyata kuwa tinda ta suma jin mahaifinta ya rasu ga kuma saƙon mijinta shima ya rasu ga kuma Máahmud wanda ta sashi a ranta shima baya nan daga nan bata ƙara farfaɗowa ba sai bayan watanni uku nan ma saida aka dage da addu'o'i da maganganuwan Musulunci tukun Allah ya bamu nasarar ceton ta amma har zuwa wannan lokacin tana nan a ƙasar Iran ko magana bata iya yi saboda damuwar dake ranta, tana dai cin abinci tana komai amma bata cewa komai sannan ba sosai take iya gane mutum ba sakamakon hawan jinin da take fama dashi amma tana raye har yanzu, wasu lokuta nakan je na dubota, tare muka cigaba da zama da mahaifiyata a ƙasar Iran bamu sake komawa ƙasar california ba cikin masarauta, a Iran na cigaba da karatuna har nayi boko da Arabic, amma nafi zurfafa karatuna akan musulunci har Allah yasa na zamo babban malami a ƙasar Iran, amma duk hankalina yana kan binciken yanda zanyi na samo ɗan uwana Máahmud, har Allah ya bani sa'a na samo shi, ya kuma ɓoyeni a gurin matarsa wato Doctor Fateema ya nuna mata cewa ni Abokinsa ne, muka zauna a haka amma bansan dalilinsa nayin haka ba, har Allah ya kawo Bara'atu cikin rayuwarsa ina ganinta nasan akwai ƙullaliyar al'amari domin Ni Allah ya bani wani irin baiwa na saurin gano mutum, ni ba matsafi bane amma ina iya gano komai akan mutum kuma duk wasu bayanai na Raamud ina sanin su domin shima bazan iya fita daga cikin rayuwarsa ba, duk wasu ƙalubalen da yake faruwa da Raamud na sani, domin shi ya shiga jikin Bara'at ta hanyar tsafi ya Aureta ya kuma shiga jikin Máahmud har yayi sanadiyar mutuwarsa ta dalilin cikin Raamud dake cikin Bara'at, wanda a lokacin mun shirya ni da Mahmud akan cewar zamu sanar da matarsa gaskiyar lamari akan Máahmud da kuma ni kaina sai dai Allah bai yadda ba... A lokacin da Bara'at ta koma jeji da zama nabita naje na zauna dasu saboda nasan ba laifinta bane na koyar dasu abubuwanda basu saniba, nayi hakane saboda bazan taɓa barin Ahalina su tagayyara ba, koba komai Bara'at da ɗiyarta sun zamo jinin mu bazan gujesu ba, kuma shi kansa Raamud bazan taɓa ƙinsa ba duk da ƙiyayyar da yake nuna mun a baya, naji daɗi yanzu da aka sanar mun cewa Masarautar mu ta gyaru, insha Allahu masarautar mu bazai taɓa barin hannun mu ba saidai idan mun ƙare gaba ɗayan mu....." Daga nan yaja ajiyar zuciya a yayin da hawaye suka wanke masa fuska...
Chapter 55 · 0% Book details