← Book details Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 85

Sashe 66

Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ayush fashewa tayi da matsanancin kuka jin yanda Uncle Artaff yake gaya mata maganganu, daman da farkon yana sassauta mata ne saboda baƙin fuskokin da suke wajen bayaso yayi magana awajensu da kuma yaransa tinda yanzu sun tashi sun tafi iya yasu-yasune hakan yasa ya buɗe mata wuta,
Sarki Raamud shima sam baiji daɗin maganganun da ya gayawa Ɓingel ba, kawai dai ya sharar ne,
jin tayi shuru sai faman kuka take tayi yasa Uncle Artaff ya darara mata tsawa tareda faɗin "magana nake miki Ayshert yakamata ki kawo karshen ƙudire-ƙudiren da kike yi akan wannan Ahali biyu da kika zamo musu ƙarfen ƙafa, banda mugunta babu abunda kika iya kenam? wani irin baƙar zuciya gareki ne? kodai muguntar da mahaifinki yayi a baya ne ya dawo kanki?...."
Sarki Raamud gaba ɗaya zuciyarsa tafasa take da jin kalaman Artaff, mommy ce ta dakatar dashi tana bashi haƙuri da cewa "kayi haƙuri Malam, mu saurara muji daga bakinta..."
ta dafa kafaɗar Ayush tace "kiyi haƙuri Daughter kinji yanzu gaya mana abunda yake zuciyarki..."
Ayush ta gagara dakatar da kukan da ya kuɓuto mata domin anyi mata bahagon fassara da mummunan zargi akan wai bata son Mommy..."
daƙer ta iya dakatar da kukan tace "Ni Allah yaga zuciyata mommy abun alfahari nane, koda wasa ban taɓa jin haushin mommy ko kaɗan ba acikin zuciyata, mommy tamun halacci a rayuwata wanda har ƙarshen numfashina bazan taɓa mantawa baaa..."
tana kuka gaba ɗaya ta fita hayyacinta, eyes ɗinta sun zama jajawur har dishi-dishi take gani tsabar kukan data sha, ta cigaba da cewa "nasan kuna jin haushi na amma kuyi haƙuri idan na mutu shikenam, ina roƙon Allah yasa wannan cikin dake jikina ya zamo ajali na da zaran na haifa muku Baby...".
ta ƙarasa maganar tana kallon Junaid wanda kansa yake kallon ƙasi tin lokacinda uncle Artaff ya soma magana...
lumshe idonta tayi ta matso hawayen da suka kwanta mata akan idonta tana jan numfashi tace "Indai haka halina yake nima nayi Allah wadar da kaina, bansan meye butulci ba saboda tinda mahaifiyata ta haifeni babu wanda ya taɓa temako na sai mommy, itace macen farko dana buɗe idona na ganta a gabana a matsayin bare kuma har ta temakeni ta mayar dani mutum,
Bansan meyake damuna ba, haka kawai sai in yanke hukunci cikin rashin tunani da hankali, idan akace nayi gabas ni kuma sai nayi yamma, wallahi bansan me yake damuna baaa, bansan meyasa banason Auren mommy da Abbah ba, haka kawai nake jin ƙunci a zuciyata..."

Uncle Artaff kallon sarki Raamud yayi sannan yace "akwai wani abu wanda yake tattare da É—iyarka kuma abun daga sashinka ya fito..."
sarki Raamud kallon Artaff yayi cikin rashin fahimta yace "nidai nasan Ɓingel batada Aljanu..."
Uncle Artaff yace "kai wannan kawai ka sani amma bakasan abunda suka ajiye maka ba..."
girgiza kai sarki Raamud yayi kwata-kwata bai fahimci abunda Artaf yake nufi ba,
Uncle Artaff ne ya kalli matarsa Zainab yace mata "a cikin jakar hannunki akwai wani abu a leda ki miƙo mun...". kamar yanda yace haka kuwa tayi sannan ya ce wa Ayush tazo gabansa ta zauna...
itama hakan tayi jiki a sanyaye ba ƙwari, durƙusawa tayi a gabansa tana hawaye, wani ɗan ƙaramin ƙwalba ya ciro ya buɗe murfin sannan ya tsiyayi wani farin Ruwa yace mata "buɗe bakin ki..."
ta buÉ—e bakinta cikin fargaba da tsoro haka ya bata wannan ruwan sannan ya mulmulka mata akan goshinta, yace "buÉ—e cikin ki.."
haka ta É—age rigarta ya shafa mata wannan ruwan..
Ita dai ta gagara ganewa duk wannan na menene,
lokaci guda ta fara jin wani irin zafi da raɗaɗi ajikinta, kayinta ne ya soma juyawa kamar wacce tayi maye! hankalinta ne ya fara barin jikinta, ƙoƙarin tashi ta soma yi Uncle Artaff yayi saurin riƙota ya zaunar da ita,
cikinta ne ya soma juyawa nan take ta ƙwanta aƙasin carpet tana shure-shure tareda ƙwalla uban ihu, launin kalarta duk ya sauya zuwa yellow tarr, ga wani irin ihun da takeyi tana birgima a tsakiyan falon,
Mommy ganin yanda Ayush ta koma yasa ta ƙanƙame Abbah tsabar tsoro, shi kuwa Junaid hankalinsa ba ƙaramin tashi yayi ganin Ayush a cikin wannan halin, har ya motsa zai zo yanda take Uncle Artaff yayi saurin dakatar dashi ta hanyar ɗaga masa hannu kuma idonsa a rufe,
jin ihun da ake yi ne yasa su Hafzat da Judan suka yo falon da saurin su, ganin Ayush ta koma yellow yasa Hafzat rungumar judan jikinta na kakkarwa,
a hankali Uncle Artaff yazo ya ɗage mata rigarta sama yana tofa mata addu'o'i cikin ƙanƙanin lokaci saiga wani ɗan ƙaramin maciji ya fito ta cikin cibiyarta, a lokacin ne Ayush ta dakatar da yin shure-shure ta rufe idonta gaba ɗaya ko motsi bata ƙara yi ba,
Ganin haka yasa mommy tsorita sosai kawai addu'a take ta faman zubawa, Junaid gaba ɗaya jikinsa ne yahau ɓari ganin wannan masifar,
Duk waran babu wanda bai firgita ba,
suna cikin wannan halin saiga wani irin baƙin hayaƙi ya bayyano wani gabjejen mutum ne ya tsaya a cikin hayaƙin, tsayinsa ya kere fankar falon gashi baƙi ƙirin dashi sai ƙaho guda biyu akansa kamar rago, idanuwansa jajawur yana sanye da baƙar riga har ƙasi,
Mommy ganin wannan Aljanin yasa ta sumewa akan Sarki Raamud, itama Hafzat suma tayi ganin abunda yafi ƙarfin ƙwaƙwalwarta, Judan bai san lokacin da ya riƙota ba sauran kaɗan ta faɗi ƙasi dake a tsaye suke,
Aunty Zainab matar malam ma suma tayi akan kujera Allah yaso yaran basa nan da ƙwaƙwalwarsu ce zata zauce,
Judan rungumar Hafzat yayi ya ɓuya a bayan kujeru da ita,
Shima Junaid da gudu yazo gefen Uncle Artaff ya tsaya kayuwansu a sama suna kallon baƙin Aljani,

Cikin dirarren murya baƙin Aljani yace "meyasa ka ƙirawo ni ARTAFF?..."
Uncle Artaff yace "na ƙira ka ne saboda ka cire hannunka akan wannan yarinyar ɗiyar sarki Raamud..."
wani irin Dariya baƙin Aljani yayi sannan ya haɗe rai yace "indai akan wannan ne kayi kuskuren ƙira na domin sarki Raamud shi da kanshi ya sadaukar mana da ita..."
Sarki Raamud a tsorace yace "Ni kuma? yaushe mukayi haka dakai?.."
Baƙin Aljani yace "RAAMUD bayan kaje mana da buƙatun mu baka ko wani irin tsafi shin ya mukayi dakai? munce muna buƙatar jinin yaronka, kace bakada matar Aure balle yaro anan ka sanar mana cewa saidai jinin yaron ɗan ɗan-uwanka! Nace maka jinin yaron zamuyi amfani waran tayar da damisan ku!!!
ta hanyar Damisa kuma zaka samu ko wani irin tsafi, mu muka sanya maka hannu akan ko wani irin tsafe-tsafe da kakeyi, amma da sharaɗin duk lokacin da ka karya mana tsafin da muka baka to kuwa zamu bibiyi ɗaya daga cikin ahalinka ko ɗanka ko ɗiyarka amma baza muyi amfani da yaron daka kawo mana jininsa ba saboda shi ya gama mana amfani, bazamu ƙara shiga rayuwarsa ba saidai mu shafi wani daga cikin jininka kuma ta hanyar nan zan gama da ahalinka gaba ɗaya,
Bayan tsafinka ya karye mun bibiyi É—iyarka wato jininka ba tareda saninka ba, kayi nasarar toshe kafar da zamu turo mata Aljanu amma saidai mun ajiye mata macijin huda a cikinta bayan ta cire zoben dish daga cibiyarta, daga lokacin ta zamo namu kuma muka tusa mata rashin imani a lokacin da muke so tayi mana wani aiki, mu mukayi control É—inta ta sanya gobara agidan da take ta hanyar amfani da maciji tinda shi ba Aljani bane, saidai munyi rashin nasara matar da muke so ta mutu an ceceta,
Kuma bazamu taɓa barinka kayi Aure ba shiyasa muke control ɗiyarka akan karta bari ayi Auren,
kuma matarka mu muka sanyata ta mutu ta hanyar Munafurr, munyi rashin nasara akan Junaiduu, wannan macijin da muka sanyawa ɗiyarka da zaran ta haihu zamu sheƙeta sannan mu ɗauke Jaririn, kuma munyi alkawarin kaima sai mun janye jinin jikinka...."

wani irin haÉ—iyar yawu sarki Raamud yayi duk ya haÉ—a gumi,
Artaff yace "Baƙin Aljani muna neman Alfarma daka bar alhalin nan tinda basuyi maka komai ba, sarki Raamud shine mai laifi kuma shima muna neman yafiyarka akan ka barshi haka..."

Baƙin Aljani yace "Artaff duk da nasan kaima acikin ahalin kake amma banyi garajen shiga rayuwarka ba sakamakon kayi karatu ne agurin babban malamin Aljanu kuma muna matuƙar jin maganarsa don haka kaima zamu saurari maganarka albarkacin babban malami..."

Artaff yace "Nagode Baƙin Aljani amma ka barshi yayi Aurensa sannan yarinyar nan ka barta haka, tanada zuciyar imani kar ka sanyata ta zamo munguwa,
Ata sanadiyarka ta zauna agidan kurkuku kuma karka taɓa mata yaran da zata haifa, na roƙeƙa idan har nima zakaji maganata to kabar mun Ahalina..."

Baƙin Aljani yace "shikenam! Shikenam zamu tafi mubar maka ahalinka amma kada a sake neman mu..."
Artaff yace "babu wanda zai sake hulɗa daku acikin Ahalina nayi maka alƙawari..."
Ayush tana kwance bata san awani duniya take ba Baƙin Aljani ya ɗagota sama da hannu ɗaya sannan ya ɓace da ita ɓatt!!!

Junaid a zabure yayo gurin da Baƙin Aljani ya tsaya sai ƙwalla ƙiran Ayush yake yana faɗin "Ina Yushert take, ina ya kaimun ita, Yushertttt! Yushertttt!! Yushertttt!!! ya tafi mun da ita, Uncle! Uncle!! kayi wani abu dan Allah kasa ya dawo mun da ita please 🙏 please 🙏...."
Uncle Artaff yazo gurin da Junaid yake ta surutai kamar wani taɓaɓɓe ya dafa kafaɗarsa yace "ka kwantar da hankalinka Junaid bawai ya tafi da ita bane, kaje ɗakinku zaka sameta cikin ƙoshin lafiya..."
Junaid yana jin haka ya ruga da gudun gaske ya haura Upstairs, yana zuwa yasa hannu da ƙarfi ya bankaɗa ƙofar kwatsam saiya tarar da Ayush kwance akan katafaren gadonsu sai sharar bacci take ga kuma cikinta shima yana nan lafiya, da sauri ya ƙarasa wajen gadon ya ɗale tareda rungumota jikinsa da ƙarfi kamar wanda za'a ɗauketa, yayi shuru yana rungume da ita ....
Chapter 66 · 0% Book details