← Book details Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 85

Sashe 80

Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Bayan isar su ƙasar california a Babban Birnin Masarautar ƙasar suka sauƙa, Ayush gani tayi kamar ba masarautar ba duk an chancanza ko ina, suna daga cikin mota bayan sun sauƙa a airport daga cikin masarauta sarki Raamud ya tura driver akan yaje ya ɗauko su, gani sukayi an buɗe babban gate kai tsaye motar ta shige ciki, ga wasu manya-manyan Bodyguards a jere fuskokinsu kamar mutuwa ba alamar dariya, Areeph yana leƙensu ta window tareda cewa. "Daddy ina ganin waɗannan a Film, sune masu harbi da bindiga awajen yaƙi...."
Murmushi kawai Junaid yayi jin yanda yaran suketa mita akan Bodyguards, bayan sunyi gaba sosai suka ƙara tarar da wani gate kuma du, nan ma buɗe musu akayi kumadu wasu ɗirka-ɗirkan baƙaƙen Amurkawa aka ajiye a jere saboda tsaro ga wasu manya-manyan karnuka da suke yawo a compound ɗin gidan, daga nan ne sai babban ƙaton cikin fada yanda manya-manyan baƙi suke zama domin tattaunawa da mai martaba sarki Raamud wato fadar sarki kenam, anan kuma kujerarsa take na zinare, anan suka sauƙa part ɗin sarki Raamud kenam kafin su wuce part ɗinsu,
Karnukan nan har sun kewaye motar suna huci duk da sun san motar gidan ne amma so suke suga mutanen cikin, suna fitowa Ayush ta ƙanƙame Junaid da ƙarfi jikinta har kakkarwa yake ba ƙaramin tsoron kare take ba, ko a can Nigeria mah bata fitowa waje saboda karnuka har yaran suka saba, suma yaran fitowa sukayi duk da basa tsoron kare amma waɗannan karnukan sun razana su, saboda su kalarsu daban yake na turawa ga gashi tumuzu guda ajikinsu, suma karnukan ganin Ogah Junaid yasa duk suka kama gabansu saboda daman shine ya watsar dasu a cikin gidan, karnukansa ne,
Haka suka shiga cikin babban falon su Mommy, ƴan aiki kawai suka tarar sunata aikace-aikacen su, duk zama sukayi akan kujeru Ayush kam bazata iya zama ba haka tasa akayi mata kwatancen yanda ɗakin mommy yake, da gudu take taka matakala har ta isa part ɗin mommy tana zuwa tasa hannu ta buɗe ƙofar ɗakin da fara'a akan fuskarta, abunda ta tarar ne yasa tayi go slow awajen, ido a zazzare take kallon mommy tana bawa yaro nono ga kuma ɗaya a kwance saman gado,
Mommy kallon Ayush tayi tana dariya daman tasan dole abun zai bata mamaki, domin shima Uncle Artaff daya zo ya tarar da jarirai abun ba ƙaramin mamaki ya bashi ba,
Mommy tace. "shugo mana Ayusher...". cike da tambayoyi a bakinta ta ƙarasa shugowa tana faɗin mommy mezan gani haka daman kin haihu ne shine baki sanar mana ba haba Mommy ..."
Ayush tana ƙarasa maganar saiga Ogah Junaid shima ya shugo da sallama a bakinsa da Sarki Raamud yana riƙe da hannun Amrish da Angel, shima Junaid tsayawa yayi kamar wanda aka dakatar dashi, cikin rashin fahimta yace "Mom wadannan yaran waye? aina kika samo su, karfa ki cemun yaran wasu kika karɓa kina shayar dasu?..."
Mommy tace "toh idan ba yaran wasu ba shin yaran wa kakeso nace maka?..."
Gira a haÉ—e yace "yaran wasu mana, saboda ke dai nasan a yanzu bazaki haihu ba.."
Ayush tace "Yaya Junaid wallahi mommy haihuwa tayi gashi tana shayar dasu..."
Junaid hararar ta yayi sannan yace "kar ki gaya mun maganar shirme mana, nasan halin Mom yanzu haka É—aukosu tayi a gidan marayu..."
Ayush ta kuma cewa "toh tayaya ruwan Nono zai zo mata alhalin ba haihuwa tayi ba..."
A ƙaiƙaice ya daka mata tsawa da cewa "yimun shuru, haihuwar lafiya..."
Mommy dai kai a sunkuye ta kasa cewa komai ga yaro yanda yaketa shan breast,
Sarki Raamud ne ya dafa kafaɗarsa yana cewa "Junaidd look at me, seriously Mom ɗinka ta haifi twins, kamata yayi kayi murna duk da nasan rashin sanar muku ne yasa ka shiga konkonto abun zaiyi matuƙar baka mamaki...."
Kafin sarki Raamud ya rufe baki Junaid ya katse shi da cewa "Da kuma bani haushi ba, haba tayaya zanyi murna tsofe-tsofe daku kuna haihuwa, ku dubi ƙananun jarirai fah wai ku kuka haifesu wallahi abun yaban kunya, ina laifin Ni na haifesu,
yanzu idan naje gurin Aiki mezance wa Abokai na da sauran yarana sojoji ina matsayin General nace Mamana ta haihu kenam? Impossible ku cigaba da ɓoye kuliyoyinku har su girma don nima babu a wanda zan gayawa, ai dole ku ƙi sanar mana kunya ce ta isheku, tayaya zaku ƙira kuce kun haihu daman ga jikokin ku...."
yana kaiwa nan ya juya zai fita kawai kunnuwansa suka soma jin kukan É—ayan jaririya dake kwance akan gado alamar ta tashi daga bacci ne,
Ayush tace "Mommy kawo wannan na hannunki na riƙe shi saiki shayar da wancan .." haka kuwa akayi mommy ta ɗauki ta kan gadon itama tasa mata Nono a baki,
Junaid juyowa yayi yana kallonta da jariran jinjina kai yayi yace "Hmmm!!!..."
ba tareda ya kuma cewa komai ba haka ya buÉ—e É—akin ya fice,
Sarki Raamud girgiza kai yayi yana murmushi domin sai yanzu ya tabbatar da cewa har yanzu akwai sauran ƙuruciya ajikin Junaid...
Ayush ta kalli sarki Raamud tace "Abba Gaskiya banji daÉ—in rashin sanar mana da kuka yi..."
Yace "sorry Ɓingel bazata mukaso muku daman, sai kunzo ku tarar da ƙannenku..."
Mommy tasa baki da cewa "ƙannenku kuma kuliyoyinku...". Ayush kwashewa tayi da dariya sai yanzu ma abun yake bata dariya da maganganun Junaid,
Shima sarki Raamud dariya yayi yana faÉ—in "Allah ya shiryi Junaid..."
ya ƙarasa maganar tareda ficewa shima,
Ayush ta kalli mommy tace "mommy kiyi haƙuri da maganganun Yaya Junaid..."
Mommy tace "cabb haba Daughter kema dai kinsan nafi kowa sanin halin Junaid, wallahi ko kaɗan banji ciwon abunda ya faɗa ba, daman ai ya saba irin haka akan mai zan damu kuma, banda iya shege irinsa inda ace nayi Aure da wuri ai da yanzu ƙannensa sun girma, amma yana nan shi kaɗai kamar shaiɗan ba ƙanne ba yayu, ki rabu dashi kawai..."
Ayush tace "gaskiya kam, ai Mommy naga baki tsufa ba, babu wanda zai ce ke kika haifi Yaya Junaid saidai wanda ya sani...."
Mommy tace "daman ai shi ya tsufar dani, haba shekarunsa ma duka-duka 35 ne dai, ke kuma 25 yanzu daman ya baki shekara goma, tinda lokacin da Mamanki tabar gidan mu kina jaririya lokacin shekaransa goma, Babansa kuma yabar duniya..."
Ayush tace "Ahhh mommy 35 ai ya girma shima ya kusan tsufa..."
Mommy tace. "haba Ayusher lokacin danasa aka É—aura Aurenku shekaransa 30 dai, yanzu kuma shekaranku biyar dayin Aure..."
. jinjina kai Ayush tayi da murmushi a fuskarta, ta kalli jaririn hannunta tace "Mommy ya sunansu?.."
Mommy tana riƙe da macen tace "wannan macece anyiwa Mamanki mai suna amma inkiya sunanta Ummul khair,
Shi kuma na hannunki mai sunan Uncle Artaff ne yaci inkiya Abul-Ameen...."
Ayush tinda mommy ta ambaci cewa anyiwa Umanta mai suna bakinta yake washe tsabar farin ciki, tace "wow Mommy naji daɗi sosai, Amma ni Ummy zan rinƙa cewa saboda Ummulkhair sunan yamun tsayi bazan iya faɗi ba..."
Mommy dariya tayi tana cewa "kaii Daughter saikace ba Æ´ar gari ba har ki gagara faÉ—in sunan Ummulkhairy?..."
gaba ɗaya dariya suke suna hirarsu abun burgewa kowa yana riƙe da jariri ɗaya.....

Su kuma Amriish da Angel suna part É—in sarki Raamud sai wasa yake tayi dasu, Areeph kuma yabi Daddynsa sunyi can part É—insu...
Chapter 80 · 0% Book details