← Book details Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 85

Sashe 27

Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Junaid gaba ɗaya ya gaji sauran masa kaɗan ya isa saman katangar, yana riƙe da ƙarfe wanda yake riƙe da katangar, yana sauƙe numfashi ya sunkuyar da kansa ƙasi yana kallon abunda ke faruwa ata ƙasa, zaro ido yayi waje cikin firgici ya furta "innalillahi wa inna ilaihi raju'un, oh my God..."
Ganin duk anyi fata-fata da sojojinsu iya mutum uku ne kawai suka saura, daga Angel ne sai maza biyu sune suketa faman faɗa, dan ma dabbobin duk suma sun ƙare corocodile ɗaya ne ya saura sai macijai dake sunfi sauran yawa amma suma an ƙarar da fin rabin su, sojoji maza biyun ne suketa aikin jefa musu bom a macijen nan, ita kuma Angel crocodile wanda ya rage ne yayo kanta da zafinsa, ga babu bom a hannunta sannan bindigarta ya faɗi babu halin ɗauka yana tsakiyar macijai,
Junaid kallonta yake domin shikam har ya fidda rai akan rayuwarta,
Crocodile ɗin ne yayi sama tukun ya faɗo mata a kanta ya danneta bakinsa a saitin wuyanta zai datsa mata wuya da haƙwaransa masu kaifin bala'i,
Haka zuciyar Junaid yake bugawa da ƙarfin gaske, jikinsa na rawa kamar zai faɗo ƙasa,. zuba wa crocodile ido yayi wanda ya rufe Angel gaba ɗaya ba'a hangota, ganin corocodile baya motsi abun ya ɗaure masa kai, sai can bayan wasu mintuna idon Junaid still yana kansu yaga crocodile yana motsi lokaci guda kuma saiyaga an ture shi gefe ga jini yanda yaketa tsiyaya daga wuyansa, Angel ce ta tureshi gefe ta tashi zaune tana jan numfashi ga duk jinin crocodile ya ɓata mata jiki,
Junaid daga nesa yake kallonta cikin mamaki yace "how comes?..."
ba tareda ta jiyoshi ba domin yayi nisa da ginin sosai..
Tunani ya shiga yi yanda abun ya kasance wato a lokacin da crocodile ya rufo kanta ta rigada ta cire wuƙar jikin takalminta ta cakawa crocodile a wuya, bataji ciwo ba sai kurzuwan da tayi...
Junaid murmushi yayi ya furta "gud jaruma ta..." da ƙarfin gwiwarsa ya cigaba da yin sama,

suma sauran sojojin da suka rage su biyun murna sukayi ganin Angel bata mutu ba, domin tana temaka musu sosai, babu wanda zai iya yin faÉ—an da tayi...
Angel hango bindigarta tayi a cikin macijen kamar wanda ake ƙara yawansu, ɗaya daga cikinsu ne ya kalli Angel a tsorace yace "Madam bom fa ya kusan ƙarewa sauran guda goma kuma naga macizen da sauransu,
Angel ta miƙe tsaye tareda faɗin "zanyi maganinsu kuwa yanzu zasu ƙare..."
ta karɓi sauran bom ɗin tace dasu "ku fara aiki da bindiga, Ni kuma zanji dasu da wannan bom..."
duk faɗan nan da takeyi da jaka a bayanta ta sauƙe jakar ta ciro takalmin mai taya, sannan ta cire takalmin ƙafarta ta sanya maitayar ta miƙe tsaye da jakar bom a hannunta ta rufu kan macijen nan da gudun gaske tana mummurƙuse su da takalmin tayanta tareda jejjefa musu bom, da zaran maciji ya kawo mata sara saita zamar da ƙafarta tana wasan gudun takalmin taya akansu...
maza biyun nan haka suka tsaya suna kallonta ga yanda take bada action Kamar a film, shima Junaid kallon ƙasa yayi yaga irin abunda Angel takeyi smile kawai yayi a daiden lokacin har ya isa sama ya zauna yana hutawa,

cikin ƙanƙanin lokaci Angel ta gama da macijen nan tas sai gawarwakinsu dake wajen kaca-kaca,
tana gamawa tazo ta cire takalmin tayan ta mayar cikin jakarta sannan ta maida asalin takalminta na soja,
suna tsaye suna jiran Junaid ya haura ya buÉ—e musu gate su fantama cikin masarautar domin ta ciki aka kulle,
Junaid igiya ya ciro shima daga cikin jakarsa ya ɗaure a jikin ƙarfen saman gini sannan ya kama igiyar nan ya fara sulalowa ƙasi ta cikin masarautar haka har yaje ƙarshe, yaji babu alamun motsin mutum ko ɗaya, hannu yasa ya buɗe gate ɗin da ƙarfin gaske yake tura gate ɗin zai buɗe, suma su Angel ɗin tafowa sukayi da gudu suka sa hannu kowa yasa ƙarfinsa aka buɗe gate ɗin gaba ɗaya,
Bayan sun shige cikin masarautar tsayawa sukayi suna tunanin ta yadda zasu fara kutsawa ciki,
Junaid yace "kowa ya riƙe makaminsa da gaske saboda wannan yanada hatsari sosai..."

ÆŠaya daga ciki yace "dan Allah kasa a turo mana wasu sojojin, mu kaÉ—ai bazamu iya da wannan ba, mu huÉ—u ne fa kawai muka rage..."
Junaid yace "taya za'a turo su bayan babu waya a hannun mu duk sun faÉ—i..."

********

Sarki Raamud kuwa shida matarsa duk sun ruɗe jin tashin bomabomai da ƙarar bindiga,
Uma Bara'at kam sumar ta sau uku jin halinda ake ciki ga tsohon ciki,
tana kuka tareda faÉ—in "shikenam mun mutu an kawo mana farmaki, nasan bazamu bar nan a raye ba..."
Sarki Raamud yana rarrashinta yace "ki kwantar da hankalinki tabbas ni sukazo farmaka amma kuma akwai wanda zai tari faɗan, yanzu haka nasan yaƙin ya koma kan Munafurr..."
Daƙer ya rarrasheta tayi shuru, suna cikin wannan halin suka ji an buɗe ƙofa, ganin Munafurr ne yasa duk suka razana, kafin suce komai Munafurr ya riƙo wuyan sarki Raamud ya ɗagashi sama da hannu ɗaya sannan ya cabko wuyan Bara'at itama ya ɗagata sama tana lilo da sawayenta ga ciki ɗurumma a gaba ya girma sosai!
Haka yayi waje dasu a haka yana riƙe dasu da hannu ɗaɗɗaya, ita kuwa Bara'at har numfashinta ya soma ɗagewa,
ya fito a fusace domin ransa ba ƙaramin ɓaci yayi ba ganin duk an tarwatsa masa mayaƙan dabbobinsa, yana fitowa harabar masarautar yanda su Junaid suke a tsatstsaye, ganin Munafurr yasa duk suka razana,
haka ya wurga sarki Raamud da Bara'at gaban su Junaid, Bara'at ihu takeyi saboda cikinta ba ƙaramin buguwa yayi ba tana faɗin "wayyo cikinahhh, innalillahi wa inna ilaihi raju'un cikina zan mutu..."
Junaid kallon Bara'at yake yana tuna mahaifinsa da tayi sanadiyar mutuwarsa, sannan ya juyo yana kallon sarki Raamud wanda shine silar rashin lafiyarsa kuma shine wanda yake wahalar dashi, tsananin tsanarsu ne ya ƙara shiga masa zuciya,
Idonsa ya ɗaga yana kallon Munafurr ji yayi Angel ta ƙanƙame shi tana faɗin "wallahi Oga Junaid ba'a turomu mu yaƙi wannan basamuden dodon ba, mu rufawa kan mu asiri mu kama waɗanda ake nema...."
Junaid duk yana jin abunda Angel take faÉ—a amma bai bata amsa ba,
Sauran sojojin guda biyu kuma duk fitsari suka sau a jikinsu ganin halittar Munafurr a yayin da kuma ɗaya acikinsu ya makance tsabar irin kallon da yake yiwa Munafurr, sai ihunsa akaji yana murtsika idonsa tareda faɗin "wayyo ido na, wayyo idona bana gani wallahi, duhu nake gani..." yanata lalumen mutane, lokaci guda kuma yayi tsitt ya ƙafe a guri ɗaya sakamakon ƙarfen da Munafurrr ya wurgo masa ya soki maƙogaronsa ya faɗi ƙasi matacce,
Junaid zaro ido yayi waje yana kallon É—aya daga cikin sojojinsa wanda aka masa wannan É—anyen hukunci...
Ita kuwa Angel ƙara ƙanƙame Junaid tayi jikinta na kakkarwa tace "idan kuka haɗa ido dashi zaku makance, Munafurr ne mungun mutum ne wannan anban labarinsa....."
Munafurr wani ƙarfen kuma du ya wullowa Angel jin tana magana sauran kaɗan ƙarfen ya shige mata goshi Junaid yayi saurin cabkewa sannan ya wurgar gefe,
duk wanda yayi magana haka yake wannan hukuncin,
Bara'at kuwa tintinin sarki Raamud ya toshe mata baki....

Munafurr da ƙwayar idonsa ya rufe babban gate ya kulle yana wani irin dariya yana cewa "yau kun shugo masarautar sarki munafurr, nine mai wannan masarautar kuma anan zan bisine gawarwakinku...", yana mai ƙara tintsirewa da dariya,
ɗayan soja ne ya ɗago bindigarsa ya fara harbin Munafurr kafin bullet's su ƙarasa gurin Munafurr har ya juyar da bullet da ƙwayan idonsa sun koma kan sojan da yayi harbin, lokaci guda shima ya faɗi matacce,
Yanzu iya Junaid da Angel ne suka rage sojoji!
Ga Uma Bara'at kwance kan cinyar Sarki Raamud sai murƙususu take tayi cikinta ba ƙaramin ciwo yake mata ba, tana jin yanda twins ɗinta suke mata juyi a ciki......

*WAƊANDA AKAYI YAƘI DASU NACE BAAAA HOW MARKET🙌🙌*
*Naga iya Angel da Junaid ne suka tsira a yaƙin waje kodai kuma an sheshsheƙeku ne ko kuma kun bi Adity kun gudu🤔🤔*

Wai shin kunga laifin Aditi data gudu kuwa? Nidai banga laifinta ba yaciin🤣🤣🤣

Akwai waÉ—anda basa comments dalilin da yasa nake hutawa kenam wallahi,
Mutane kusan 50 amma bazaka samu mutum 10 waÉ—anda zasuyi maka sharhi ba haba dan Allah..
Duk temakon kai ne dai, zaku karanta abu amma ba liking bare comment
Kodan gadararku kun biya kuɗi ne🤔🤔
Amma ai nima idan akayi mun godiya zanji daÉ—in yin typing next
Dan Allah ku gyara wannan bayi bane, mu kyautatawa junan mu shine zaman tare....
🙏🙏🙏🙏🙏🙏

𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️

𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔

the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅

𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️

𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871

*💫💫{{N W A}}💫💫*

Book two

C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 33 ➡️ 34
Chapter 27 · 0% Book details