← Book details Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 85

Sashe 35

Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sumaiya tace "amma kuma ance yarinyar itama ta ƙone a cikin gidan?..."
Lailah ta kuma cewa "duk shiri ne, yanzu haka tana ɓoye a gidan mu, a tunanin mutane sun ɗauka ta mutu.."
Sumaiya ta kuma cewa "Amma Lailah fatan dai kinada hujjoji a hannunki saboda bama aiki sai mun tabbatar da gaskiyar lamarin..."
Lailah tace "ni ce kuwa mai tattare da hujjoji, domin har recording ɗin maganar ta cewa ita ta ƙone gidan inada shi, sannan inada photonta da video duk maganganun da takeyi, inaso ku buga jaridu akanta sannan ku bubbuɗe duk wata kafar television ku tallata ta da duk wasu maganganun da tayi, inaso hukuma tayi aiki akanta, abi hakkin Doctor Fateema..."

Sumaiya itama ta gamsu da bayanan Lailah tace "shikenam zan sanarwa Ogan mu kuma zaiyi farin ciki sosai dajin wannan batun domin ba ƙaramin kuɗi zamu samu a kafar mu ba, mungode sosai Lailah,
yanzu kizo ki bamu duk wasu bayanai, inba sa'a ba sai anyi zanga-zanga akan a hukunta yarinyar..."
Lailah murmushi tayi sannan tace "shikenam saikin ganni..."
daga nan sukayi sallama..

Daƙer Malam Lawan ya rarrashi Junaid suka tashi har saida Doctor Hasheem yasa hannu suka fita da Junaid, domin kasa tafiya yayi ƙafarsa ta riƙe, ga zazzaɓin da yake kawo masa hari...

Ayushert tana daga cikin ɗakin tana jin ihun da Junaid yake yi gaba ɗaya ji takeyi kamar ta kashe kanta, itama kukan take sosai, tana cikin kukan sai taji murɗa yana damunta da sauri tasa hannu ta toshe bakinta tana yunƙurin amai! tashi tayi da gudun gaske ta nufi toilet,
haka take kwarara amai kamar ranta zai fita, duk abunda taci saida ta amar dashi, har ta koma tana aman zallar ruwa...

haɗagowa tayi tana maida numfashi sama-sama, domin ba ƙaramin wahala take sha ba, lokaci guda ta fita hayyacinta...

Narasimha tin tinin yazo ya ɗauke Damusa sun ɓace tare.....

*TOFAH KAR DAI ACE YUSHERT CIKI GARETA🤔🤔🤔*
*TAFIYAR OGAH JUNAID DA DAWOWARSA ONE MONTH...*
*TAYI 3 MONTHS A GIDAN DOCTOR HASHEEM...*
*4MONTHS KENAM🙄🤔🤔 NIDAI NA FARA LISSAFI..*

𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️

𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔

the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅

𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️

𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871

*💫💫{{N W A}}💫💫*

Book two

C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 41 ➡️ 42

Bayan Malam Lawan sun isa gida daƙer ya rarrashi Junaid, duk da har yanzu jikin nashin ba ƙwari, Junaid yana jan ƙafa ya shige ɗakin da yake a gidan Malam Lawan, yana shiga ya tarar da Damusa baya nan ƙirjinsa ne yayi wani irin bugawa daiden lokacin shima Malam Lawan ya shugo, da sauri Junaid ya waiwayo yana faɗin "ina Sujjur?.."
Malam Lawan yayi murmushi yace "kwantar da hankalinka Sujjur ya tafi yana can cikin ƙoshin lafiya" Junaid cike da mamaki yake kallon Malam Lawan yace "bangane ba, shin ina ya tafi?.."
yace "Junaid kenam ai masu masarauta bazasu bar Sujjur ya zauna a gefe guda ba, an bi ta hanyar tsafi an É—auke shi..."
Junaid yace "toh amma waye yazo ya É—auke shi?.."
Malam Lawan yace "Narasimha babban matsafine a cikin masarautar shine mai basu kariya akoda yaushe..."
Jinjina kai Junaid yayi sannan yace "ok na sanshi..."
ya ƙarasa maganar tareda zama a bakin gado yana dafe da kansa, maganganun Ayush ne suka fara masa yawo a ƙwaƙwalwa, lokaci guda kuwa saiga hawaye yanda yake ta gangaro masa, cikin sassanyar murya yace "why! why!! meyasa Yushert zata mun haka, mahaifiyata ta ƙona da wuta, saboda wani ƙudirinta da ban, meyasa zatayi wa mommy haka bayan tayi mata halacci a rayuwa..."
ya É—ago yana kallon Malam Lawan wanda shima tagumin yayi yana jinjina maganganun Ayush,
Yace "tabbas ba ƙaramin kuskure ta aikata ba, ban taɓa tunanin zatayi haka ba.."
Junaid dafe goshinsa yayi yana zubda hawaye, ji yayi malam lawan ya dafa kafaɗarsa yana rarrashinsa tareda faɗin "kayi haƙuri Junaid, kar ka biyewa zuciyarka ka aikata wani mummunan abu, inaso ka jirani ina zuwa yanzu..." yana kaiwa nan ya miƙe ya fice...
Bayan minti goma sai gashi da ƙaton littafi a hannunsa da wani ɗan ƙaramin akwati, Junaid ɗagowa yayi yana kallon Malam Lawan, yace "wannan littafin da na kawo maka kwanaki ne ai.."
Malam Lawan yace "ehh yanzu zan karanta maka tarihin rayuwar iyayenka da kakanunka sannan saika É—auko mun É—ayan littafin da Narasimha ya baka, anan zaka gama fahimtar ko kai waye ne..."
Junaid shidai kawai kallon Malam Lawan yake da lufu-lufun idanuwansa waÉ—anda suka canza sukayi jawur...

Malam Lawan ne ya fara kora masa labari tin daga farkon haihuwar mahaifinsa har zuwansa Nigeria,
Malam Lawan kaf saida ya bayyana komai, da kuma silar kamuwa da ciwon Damusa har warkewarsa sannan ya bayyanar masa akan cewa Ayush ce tayi silar warkewarsa ta hanyar cire wannan zoben jikin cibiyarta...
Bayan Malam Lawan ya gama da littafi na É—aya haka yasa Junaid ya É—auko masa littafi na biyu nan ma ya fara bayyana masa labarai na tarihin rayuwarsa dana Ayushert,
Kamar yadda Narasimha ya bawa mommy labarin masarauta haka malam Lawan shima ya bada wa Junaid labarin kaf ba abunda ya bari,.
ya gama bashi labarin daiden lokacin anata ƙiraye-ƙirayen sallar mangarib,

Junaid ba ƙaramin jijjiga yayi ba a wannan labarin gaba ɗaya ya shiga taitayinsa, fuskar nan ta koɗe har wani yellow+² yayi tsabar firgicin da ya shiga da tashin hankali, idonsa kamar wanda yayi shaye-shaye daƙer yake lumshe su ga fatar lips ɗinsa duk ya bushe, kana ganin Junaid kasan ba ƙaramin jiki yake sha ba, duk ya fice a kamannunsa ya rarrame lokaci guda,
wani irin ƙaunar Ayush ne yaji ta shige masa zuciya domin ba ko wace mace bace zata ita sadaukar da rayuwarta akan wani ba, kuma ta dajirce sosai akan Junaid, ta ɗauki duk wani wahalarsa, ta kuma jure duk wulaƙancin da yayi mata...
Jinjina kai yayi a hankali ya furta "tabbas soyayyar gaskiya bazata taɓa gushewa ba, bazan taɓa rabuwa da Yushert ba domin bazan samu mace kamarta ba, Mommy tamkar mahaifiya take a gurin Yushert don haka nabarwa komai a hannun Allah, shine mai yanda yaso nidai burina Yushert ta dawo gareni, inaso na biyata da nawa dubun alkhairin data aikata mun a baya, zan sa a raina cewar mu marayu ne daga ni har ita wanda ya rage mana mutum ɗaya ne shine mahaifinta kuma mahaifina wato sarki Raamud..."
Junaid ya ƙarasa maganganunsa tareda miƙewa tsaye...
Malam Lawan yace "toh daka miƙe tsaye ina zakaje?.."
Junaid kallon Malam Lawan yayi sannan yace "zan koma gurin Yushert, zanje na tafo da ita domin ita É—in rayuwata ce kuma jinin jikina..."
Malam Lawan yace "idan kaje Ayshert bazata taɓa sauraronka ba a halin yanzu, zata walaƙantaka ne.."
Junaid yace "zan iya juran duk wani wulaƙancin ta Malam, nidai burina ta kasance dani..."
Malam Lawan ne ya riƙo hannunsa yace "shikenam! Shikenam!! yanzu dai zauna inaso na baka wani albishir ɗin labari wanda yau zakayi ƙwanan farin ciki"
Junaid jin wannan batun yasa ya zauna cikin gaggawa yana facing ɗin Malam, gaba ɗaya yana ɗaukin malam ya sanar masa, gani yayi malam yasa hannu ya ɗauki wani ɗan ƙaramin akwati wanda yayi baƙi ƙirin daka ganshi kasan acikin wuta aka ciro shi,
Junaid yana kallon akwatin yace "wannan kamar boxes É—in mommy.."
Malam Lawan yana jinjina kai yace "shin kasan meye a cikinsa?.."
Junaid ya jijjiga kai alamar a'ah, malam Lawan yana murmushi yace "wannan ɗan ƙaramin akwatin a cikin shirgin mommy na ganshi, komai ya ƙone amma banda shi sakamakon jikinsa na ƙarfe ne..."
yasa hannu ya buɗe cikinsa ya ɗauki card guda ɗaya ya miƙawa Junaid, da sauri ya karɓa yana dubawa, ƙirjin Junaid ne yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske ganin a jikin katin an manna photonsa dana Ayush kuma ga sunansu a jiki..
Junaid miƙewa yayi da sauri yana faɗin "Malam wannan kamar katin Aure koh?.."
Malam yana murmushi yace "ba alamar tambaya Junaid! hakane ka duba date ɗin da aka ɗaura muku Aure kai da Ayushert, a washe garin zaka tafi yaƙi aka ɗaura Auren, kuma a ranar da Angela ta musulunta a ranar aka ɗaura Auren ba tareda kun saniba, ban san dalilin da yasa mahaifiyarka ta ɓoye muku ba, amma mune shaidun Aurenku domin nine maɗaurin Auren Ayshert kai kuma Barrister Aminu ne abokin mahaifinka..."

Junaid kamar zai sume a gurin tsabar farin ciki haka ya ɗora katin a saitin zuciyarsa yana fitar da numfashi a hankali ga wani irin murmushi a saman fuskarsa har saida dimple ɗinsa suka lotse yace "Allah na gode maka, Allah Ubangiji ya sakawa mahaifiyata da gidan Aljanna, ina Alfahari dake mahaifiyata, taga zuciyata ina ƙaunar Yushert sosai..."
Malam Lawan yace "Ma sha Allah, yanzu dai taho muje muyi sallah saika ci abinci cikin nutsuwa tinda farin ciki ya wanzu maka..."
Junaid yace "Malam idan nayi sallah zanje na É—auko matata.."
Malam yace "a'ah ka bari sai gobe da safe sai kaje ka fahimtar da ita, idan ta yadda kun tafo shikenam, idan kuma bata yadda ba saika barta dani ni zanje na É—auko maka ita cikin fahimtar juna..."
Junaid jinjina kai yayi da smile a kan fuskarsa yace "shikenam malam Allah ya kaimu goben.."
Amma ba haka yaso ba, lokaci guda kuma sai yake jin wani irin ƙololuwar baƙin ciki sakamakon zamanta a gidan Doctor Hasheem kuma tana mazannin matar Aure, sai kuma ya fara jin kishi a ransa...

******

Lailah tana tare da Sumaiya ƴar jarida duk ta gama basu wasu bayanai da hujjojin da zasu bayyana Ayush a matsayin mai laifi, Sumaiya ce ta kalli Lailah tace "gaskiya kinyi ƙoƙari mutumiyata, kin bamu duk wasu bayanai da ake buƙata insha Allahu zuwa nan da kwana uku zaki fara ganin photunan Ayushert da video maganganun ta a gidan television, toh amma saidai Yayanki Hasheem shima zai fito a cikin jaridar mu saboda shine ya ɓoyeta kuma zamuje har ƙofar gidanku tareda tarin ƴan jaridu da masu ɗaukan rahotanni, kuma nasan tabbas dole ƴan sanda da sojoji zasu je domin kamota because mahaifiyar Captain Junaid ta kashe..."
Lailah murmushi tayi tace "saina jiyo ku Æ´ar uwa..." tana kaiwa nan tayi tafiyarta...
Chapter 35 · 0% Book details