← Book details Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 85

Sashe 82

Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan wata guda da tafiyar Ayushert aikin Hajj, Ogah Junaid yana zaune a Babban office ɗin shi sai faman danne danne yake a cikin computer sai ji yayi wayarsa tana ring-ging, bai tsaya duba wayar ba sai ya cigaba da aikin gabansa domin ya saba irin haka sai a ƙirashi sau nawa amma bai ɗaga ba kuma yana kusa da wayar, bayan ƙiran ya katse sai kuma aka turo da message, anan ne yakai hannunsa kan wayar domin duba saƙon da aka turo masa, lokaci guda ya miƙe tsaye a razane yana faɗin "what .."
Ƙirjinsa ne ya hau bugun uku uku ido a zazzare, daƙer ya iya haɗiyar yawu wanda ya tokare masa maƙogaro, ganin text ɗin ba karamin razana shi yayi ba,
{Sorry your wife....}
abunda aka rubuta kenam, ya gagara gane mai hakan yake nufi, dasauri yabi number da akaita ƙira amma abun mamaki lokaci guda akayi switch up, jiki ba ƙwari ya fice daga office ɗin, yana fita a gaggauce ya shige motarsa kai tsaye gida ya miƙa domin tabbatar da abunda ke faruwa da matarsa, ko zasu iya sanin komai...

Mommy tana dinning tana shirya kayan abinci a sarki Raamud, wannan aikin ba na masu aiki bane aikinta ne, saida ta gama tsab zata haura upstairs ta nufi ɗakinsa kwatsam taji ana ƙwallah mata ƙira tin kafin a shugo falon, mommy ba ƙaramin tsorita tayi ba tace "innalillahi wa inna ilaihi raju'un, Allah yasa dai lafiya ..". dasauri ta sauƙo falo daiden lokacin da Junaid ya shugo hankali a tashe ya nufeta tareda faɗin "meya faru da Yushert?..."
saida gabanta ya yanke a tsorace tace "wani abu ya faru da ita ne?..." Nuna mata message da aka turo masa yayi mommy ta karɓa tana dubawa lokaci guda ta sauƙe ajiyar zuciya tana hararar sa tareda cewa. "wallahi saika kashe mai rai, haba wannan wani irin tayar da hankali ne haka, Ni nayi tunanin wani abu ya faru ne ashe abunda aka rubuta kenam..."
Junaid yana kallon mommy yace "sorry your wife?...! Abunda aka rubuta kenam toh amma me hakan yake nufi? shin meya faru da ita? kuma ba ita ta turo wannan message ba still nabi number but switch up...."
sai a yanzu itama mommy ta shiga yin nazari tace " wait bari na ƙira number Sameeha naji meke faruwa ne saboda Ayushert a wajenta ta sauƙa..."
tana shirin ƙira saiga ƙiran Uncle Artaff mommy tace "yawwa ga Uncle ɗinku ma ya ƙira.."
ta ɗauki ƙiran tareda sallama, mommy tace "yadai naji muryarka sanyi² meke faruwa?..."
Junaid eyes É—insa akan mommy kansa har wani juyawa yake, saiji yayi mommy tana faÉ—in "Alhamdulillah Masha Allah mai aka samu?.."
daga ɓangarensa ya bata amsa da cewa "Namiji...". Mommy tace "toh amma ita Ayush tana lafiya koh?.." Uncle Artaff bai bata amsa ba ya katse wayar..
cike da mamaki tace "ha'a lafiya kuwa"..

Junaid jin ance Namiji ne har yaji sanyi a ransa, ya ɗaga hannu sama yana godewa Allah cike da farin ciki, ya kalli mommy yace "amma wanda ya turo saƙonnan ba ƙaramin tsorata Ni yayi ba, me makon yasa congrats amma wai sorry, Sorry for what?..."
Mommy tace "toh yanzun ya za'ayi?..."
Junaid yace "me kuwa za'ayi illa a É—auko mun matata da jariri a dawo mun dasu gida..." Mommy tace "haka ya kamata ayi, kawai zance wa Uncle Artaff su dawo gida kawai ko kuma Ni naje na dawo da ita..."
Junaid yace "gaskiya Mom gobe da sassafe jirgin Makka zai tashi yakamata kije da kanki, yaranki kuma tinda sun fara wayo kuma ga masu aikin ki kawai ki barsu...."
tace "ehh daman barinsu zanyi, yanzu dai bari naje na samu Abbanku na sanar masa..."
Junaid ya amsa tareda ficewa daga part É—in gaba É—aya, kai tsaye part É—insu ya nufa...

Bayan shigar Mommy room É—in Sarki Raamud tarar dashi tayi akan sallaya bayan ya idar da Sallah ya kifa kansa akan gwiwowinsa, itama zama tayi akan sallayar dab dashi ta ambaci sunansa cool voice. "My King.."
ÆŠagowa yayi da rinanan idanuwansa waÉ—anda suka kaÉ—a sukayi jaa tsabar kukan da yasha, mommy a tsorace taja baya cikin tashin hankali take faÉ—in "Subhanallahi Mai martaba mai zan gani haka, kuka fah kake yi? Na juma ban ganka acikin wannan halin ba dan ALLAH ka sanar mun..."
Jinjina kai yayi sannan yace "yanzu na gama yin waya da Artaff..."
Mommy cike da mamaki tace "nima nayi waya dashi yake sanar mun cewa Ayushert ta haifi É—a Namiji..."
Girgiza kai sarki Raamud ya shiga yi yace "Ɓingel ta haifi Jaririnta kuma yana nan cikin ƙoshin lafiya amma sai dai ita ta rasa tata Rayuwar...". wani irin razana mommy tayi tareda ja da baya tana faɗin "innalillahi wa inna ilaihi raju'un⁴..." haka ta rinƙa nanatawa lokaci guda ta kifa kanta aƙasin carpet ta fashe da matsanancin kuka jiki na kakkarwa,
Sarki Raamud jiki ba ƙwari haka yake rarrashinta shima yana zubda ƙwallah, daƙer yake furta "kiyi haƙuri kulli nafsin za'ikatul maut, duk mai rai mamaci ne...". Mommy kuka take ba bakin magana, a wannan ranar haka ta wuni tana wannan kukan...

Washe gari mommy da Sarki Raamud sun shirya akan zasu je makkah, amma sun kasa sanar wa Junaid halin da ake ciki, shi a tunaninsa zasu je ne su taho da ita da Jaririnta...
Bayan kwana biyu da tafiyarsu, Ogah Junaid yana zaune a babban falonsa yana kallon tv ga Amrish kwance saman cinyarsa ta damu sosai da rashin ganin mommyn ta, kullum saita tambayi yaushe zata dawo, kullum tana cikin kuka wai ita akaita gurin mommynta daƙer Junaid yake rarrashinta domin Amrish tanada rarraunar zuciya kamar Ayush, abu kaɗan take saka abu aranta, ita kuwa little Angel tana can tanata wasanta bata damu ba, tayi kewar mahaifiyarta amma akoda yaushe tanasa ran zata dawo, shi kuma Areeph koda yaushe yana cikin dube duben littafinsa na school, ko kuma yaita danne² computer sam bai damu da tafiyar Mommynsa ba saboda yasan zata dawo...
Ogah Junaid yana zaune yasan yau ne su Mommy zasu dawo, saboda hakane yasa tinda suka tafi bai fita yaje gurin aiki ba saboda yaran,
Ji yayi an buɗe gate mota ta shugo, yana jin parking mota yasan su ne suka dawo da murmushi akan fuskarsa ya ɗago da Amrish yana faɗin "Mamana tashi maza ga mommynki ta dawo..". a ruɗe ta tashi tana cewa "Mommy ta dawo ina take? kafin su nufi bakin ƙofa saiga su Mommy sun shugo da sallama a bakinsu tana ɗauke da Jariri a hannunta, sai sarki Raamud yana biye da ita da kuma Uncle Artaff su uku, Junaid kallonsu yake ganin ba Annuri a fuskokinsu, idon mommy a kumbure yanda tasha kuka, haka suka shugo gaba ɗayansu suka zazzauna akan kujera shima Junaid zama yayi ya kasa cewa komai, ita kuwa Amrish da gudu taje ƙiran sauran ƴan uwanta cewa Mommynsu ta dawo,
Ogah Junaid murya na kakkarwa yace "ina take?..." Mommy sunkuyar da kai tayi ƙasi tana sharar hawaye, Uncle Artaff ne yayi ƙarfin halin cewa "Junaid kayi haƙuri akan abunda zamu ce maka, inaso ka kwantar da hankalinka kayi imani da ƙaddara mai kyau ko akasin haka, mu sani cewa duk rintsi duk wuya wata rana zamu bar duniya ko yau ko gobe kai ko yanzu ma idan Allah yaso zai karɓi rayukan mu..."
Cikin rashin fahimta Junaid yake bin Uncle Artaff da kallo yace "Please uncle duk nasan da wannan nidai buƙatata a sanar mun a inda Yushert ta tsaya, na ƙosa dana ganta kuma ƴaƴanta suma sun damu sosai..."
Mommy ce ta taso daga yanda take zaune ta zo gurinsa tareda miƙa masa Jariri tace "ganan yaronta nan ita bata samu damar zuwa ba..."
yatsina fuska yayi tareda faɗin "ban gane bazata samu damar zuwa ba, shin meya faru da Yushert ne kuke ƙoƙarin ɓoye mun?..."
Sarki Raamud kam babu bakin magana sai hawaye domin yayi babban rashi a rayuwarsa, Ɓingel Abar ƙaunarsa kuma farin cikinsa....
Uncle Artaff yayi ajiyar zuciya sannan yace "kayi haƙuri Ayshert Allah yayi mata rasuwa..."
Junaid jin kansa yake kamar a sama yake ga wani irin hajijiyan da yake ɗibansa Lokaci guda, a ruɗe yace "whattt...". yana riƙe da Jariri a hannu badan a zaune yake ba babu abunda zai hana hajijiya ya ɗebe shi, lips ɗinsa ne yake kokarin motsa shi amma ya kasa furta komai, lokaci guda idanuwansa suka rine sai hawayen dake gangaro masa, a hankali yakai idonsa kan yaron yana ƙareshi da kallo, girgiza kai ya soma yi tareda faɗin "i can't believe, Yushert bazata mutu ta barni ba, inaji ajikina Ni zan rigata mutuwa, zanje na ɗauko matata tinda kun kasa tafo mun da ita..."
a gigice ya miƙawa mommy yaron dake hannunsa yana sambatu ya tashi zai nufi waje, Sarki Raamud yayi saurin riƙo shi yana faɗin "kayi haƙuri mana Junaid, ka sani fah kowa ma zai mutu kuma lokacinta ne yayi, ka godewa Allah ta hanyar Haihuwa ta mutu, tana buƙatar addu'ar mu dan Allah ka kwantar da hankalinka...."
Junaid idonsa akan sarki Raamud daƙer yake motsi da bakinsa yace "Abbah da gaske Yushert ta mutu?..."
Jinjina masa kai kawai yayi yana zubda ƙwallah, cikin ƙanƙanin lokaci numfashinsa ya ɗage luuuu yayi baya zai faɗi sarki Raamud yayi saurin taro shi yana faɗin "innalillahi wa inna ilaihi raju'un Junaid! Junaid!! Junaid!!!..." haka ya kiɗime yana ƙiran sunansa amma ko motsi Junaid babu,
Mommy tana zaune kawai ta fashe da kuka, Uncle Artaff ne shima ya miƙe suka ɗago shi kai tsaye upstairs suka haura dashi yanda zai kai su room ɗinsa...
Chapter 82 · 0% Book details