← Book details Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 85

Sashe 20

Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mommy tace "duk ba abun tashin hankali bane yanzu zanje gidan Barrister Aminu babban abokin mahaifin Angon ne shi zai zamo maÉ—aurin Auren yaron,
Ita kuma yarinyar malam lawan ne zai karɓi Aurenta, don haka zan bada sadakin a Barrister Aminu, nidai malam dan Allah a tabbatar an tara shaidu..."
Yace "ba komai hajiya Allah ya sanya alkhairi.."
ta amsa da "Ameen.."
daga nan suka katse wayar..
Mommy da sauri ta yafa gyalenta ta É—auki key É—in mota ta fice a É—akin..

*****

Angel da Ayush suna tareda Malam lawan sun kora masa bayani kuma ya gamsu yayi gyaran murya sannan yace "insha Allahu zaki musulunta yanzu, zan faÉ—i kalmar da zaki musulunta wanda idan kika faÉ—i kalmar shikenam kin shiga cikin musulunci dake da wanda yayi shekara 100 a cikin Musulunci kun zama É—aya don haka duk abunda nace kema ki maimaita..."

Angel tace "toh Malam.."

Haka yake karanto mata kalmar shahada tana biyawa har suka zo ƙarshe...
Malam yace "yauwa Æ´ata Masha Allah yanzu kin zama musulma kema, yanzu abunda ya rage shine ki canzawa kanki suna daga Angela ki koma asalin sunan musulmai..."

Angel tana murmushi yanzu zuciyarta tayi wasar ta kalli Ayushert tace "meye asalin sunanki Ayush?.."
Ayush tace "kina son zama takwarata ne?.."
Angel tace "eh mana..."
Ayush tayi murmushi sannan tace "wow naji daÉ—i sosai toh ni sunana Ayshert.."
Angel ta turo baki cike da shagwaɓa tace "no no noo ba Aisha ba..."
Ayush tana dariya tace "wato sunana ba daÉ—i ko?"..
Angel tace "yess zan zaɓi suna ne mai daɗin gaske..."
Malam yace "toh muna jinki ki zaɓi sunan daya kwanta miki..."

Angel tajaa dogon numfashi sannan tace "Ni sunana Maryammm na zama takwarar mahaifiyar Annabi Isah..."
Sai malam ya ƙarasa mata da cewa "A.S.."
gaba ɗayansu sunyi farin ciki sosai dajin sunan da Angel ta zaɓawa kanta..
Malam yace "toh bari na ƙira matata kuje ta gwada miki yanda ake wankan shiga musulunci..."
Angel ta amsa da "toh malam.."

Malam yana shirin tashi kenam saiga ƙiran wayar Mommy ya ɗaga ƙiran yana faɗin "Assalamu alaikum Hajjajo ykk?.."
Mommy ta amsa masa cikin farin ciki sannan ta sanar masa cewa "zuwa ƙarfe 5 na yamma akwai ɗaurin Aure a masallacin data buɗe, ta sanar masa Auren waɗanda za'ayi sannan kuma shine maɗaurin Auren yarinyar..."
Malam yaji daɗin wannan batun sosai yayi hamdala sannan yace "ba damuwa Allah ya kaimu lokacin yanzu ma tashi zanyi nayi wankan shirin tafiya don yanzu haka ƙarfe huɗu ne kuma kinga sauran mana awa ɗaya, zan gayyaci mutane sosai..."

Mommy ta katse shi da cewa "a'ah malam bana buƙatar wasu mutane da yawa an rigada an tanadar da dattijai basu fi mutane goma zuwa ashirin ba saboda Auren sirri nake son yi wanda banaso ko su yaran su sani balle.."
Malam ya jinjina kai tareda faÉ—in "toh amma Hajiya meyasa? ko basa son junansu ne?.."
Mommy tace "a'ah kawai dai akwai abunda nake tsarawa ne, hatta shi yaron bai san da Auren ba balle ita yarinyar kuma banaso a sanar musu dan Allah malam.."
Mallam yace "toh shikenam Hajiya ba damuwa Allah ya sanya musu Albarka acikin Auren nan..."
Mommy ta amsa da Ameen sannan ta kuma cewa "yanzu haka ina gidan Barrister Aminu shima na sanar masa zaku haÉ—u a masallacin na bashi sadaki million É—aya da zoben gwal..."
Malam yayi hamdala tareda nuna farin cikinsa daga nan suka katse wayar..."

Angel duban malam tayi cike da mamaki tace "malam kamar da Mommy kukayi wayar koh?..."
Malam yace "eh hakane Maryam.."
ta kuma cewa "toh amma naji kuna maganar Aure shin Auren wa za'ayi?..."

Ayush ce ta katseta da cewa "haramun ne shiga shirgin da ba naki ba Aunty Maryam..."
Ajiyar zuciya Angel tayi sannan tace "toh na daina ƙanwar Maryam.."
Duk sukayi dariya
Malam kam girgiza kai yayi yana murmushi sannan ya tashi ya nufi ciki ya sanar da matarsa Malama Zainab akan ta koyawa Angel yanda ake wankan shiga musulunci da duk wani abunda ya shafi Addinin Musulunci.."
Malama Zainab ta amsa masa cike da farin ciki itama....

🗣️🗣️🗣️🗣️ *SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!*
*DAN GIRMAN ALLAH KU DAINA COMMENTS A CIKIN WANNAN PAID GROUP, KU RINƘA ZUWA CAN OLD GROUP KUNA COMMENT ACAN SABODA KAR WANCAN GROUP ƊIN YA MUTU KUNGA BA TURA LITTAFI NAKEYI ACAN BA, AMMA YIN COMMENTS ƊINKU ACAN ZAI ƘARA ƘARFAFA GROUP ƊIN...*

*NI INA BUÆŠE GROUP ÆŠIN NAN NE SABODA ANA ÆŠANYIN HIRA IDAN AKWAI MASU BADA SHAWARWARI AKAN LITTAFIN SU BADA, AMMA BANDA SHARHI DAN ALLAH ACAN GROUP ZAKUNA YI*

*SANNAN WAÆŠANDA BASA MUN COMMENTS NI BAZANCE MUKU KOMAI BA SABODA KUÆŠI KUKA BIYA KUKA SHUGO AMMA ZAKU NA GANIN DELAY ÆŠINA WAJEN YIN NEW UPDATE, DALILIN DAYASA BANA MUKU UPDATE KENAM AKAN LOKACI SHINE RASHIN COMMENTS ÆŠIN WASU DAGA CIKIN KU...*

*WAÆŠANDA BASA CIKIN WANCAN GROUP ZAN TURO DA LINK KU SHIGA KUNA COMMENT ACAN ÆŠIN....*

𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️

𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔

the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅

𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️

𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871

*💫💫{{N W A}}💫💫*

Book two

C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 25 ➡️ 26

Junaid yana kwance ya rufe idonsa sosai har wani zaƙami yake yi tsabar ɓacin rai, abunda ya tsara daman a ransa shine idan ya tashi bazai bar Doctor Hasheem da ransa ba, domin babu abunda zai hana shi ya murɗe masa wuya!

Doctor Hasheem yayi dace sosai tinda har ya bar É—akin yayi tafiyarsa Junaid bai buÉ—e eyes É—insa ba,
Jikin Junaid ne ya fara kakkarwa, kansa yana juyawa inda ba'a kwance yake ba toh babu abunda zai hanashi faɗuwa, cije leɓɓensa yake da ƙarfin gaske...

Shi kuwa Doctor Hasheem sauri-sauri gudu-gudu haka yake tafiya har ya iso bakin gate ya buɗe da sauri ya shige motarsa yabar ƙofar gidan,

Ƙarfe 5:00 duk waɗanda aka buƙaci suzo gurin ɗaurin Aure duk sun zo kowa ya halarci gurin sai iya dattijai kawai ake gani dake su aka buƙaci suzo,
daga ƙarfe 5 zuwa 6 har an ɗaura Auren Junaid khan Maahmud da kuma Ayshert Máahmud akan sadaki million ɗaya da zoben gwal 🙏🙏
an kammala komai yanzu Junaid da Ayush sun zama ma'aurata a rashin saninsu,.
Mommy zuwa tayi ta buga cards na shaidar Auren su da date É—in da aka É—aura Auren da photunan ma'auratan a jikin katin,
waɗannan katinan ta bugosu ne badan ta rabasu ba sai dan ta ajiyesu ko wata matsala zata iya ɓullowa ga shaida nan,
Mommy tayi farin ciki sosai dajin an ɗaura Auren, tuƙin mota take amma bakinta a washe yake ta gagara rufesu tsabar farin ciki, da wannan farin ciki ta isa gida,
Horn tayi maigadi ya buɗe mata da sauri domin a lokacin ma ƙiraye-ƙirayen sallar mangarib ake yi, da gudu ta shige gidan kai tsaye wajen parking ta nufa ta ajiye motarta ta fito fuskar nan wasar!

Mommy tana shiga ta fara ƙiran sunan Angel! Angel!! Angel!!! "Ha'a kar dai ace yarannan basu dawo ba? kuma dare yayi ai zasu kamo hanya su dawo gida ko?..."
tana kaiwa nan ta haura upstairs tana faÉ—in "bari na dubo yarona ko shima ya fitan ne.."
tana zuwa ta fara knocking a hankali har saida ta jera kusan sau biyar tana buga ƙofar ba'a buɗe ba daga baya ta tura ɗakin,
ganin Junaid a zaune a bakin gado ya haÉ—e kansa da gwiwarsa yana rungume da kansa yasa ta cewa "wato kana jina inata faman knocking shine ko ka kulani koh my son..."

Junaid yana jinta bai ɗago ba, still ta ƙara cewa "kodai fushi ake da Mommy?..."
nan ma ko motsi baiyi ba, hannu mommy tasa tana ƙoƙarin ɗagoshi, ɗagowa yayi da wasu rinannun eyes ɗinsa waɗanda suka shashshanye juyowa yayi yana kallon Mommy ido kamar zai rufe kansa,
Mommy cikin nuna damuwa tace "lafiya kuwa Junaid? meya faru dakai haka, dubi yanda ka koma fa..."
Murya ciki-ciki yace "Please Mom my Headache..."
Mommy tace "subhanallahi ciwon kai kuma my son, meya jawo hakan? bari naje na É—auko maka magani ko..."
tashi mommy tayi da sauri ta fice a É—akin kai tsaye É—akin magani ta nufa, ta jido maganunnuwa har kala uku aciki har da wanda zai sakashi bacci domin har da rashin baccin ma,
cikin ƙanƙanin lokaci mommy ta dawo hannunta ɗaya yana ɗauke da bottle na ruwa, ta sameshi a yanda yake a zaune itama zaman tayi tana ƙoƙarin ɓare masa maganin,

zuciyarsa ne yaketa harbawa da ƙarfin gaske, yana tariyo maganganun Doctor Hasheem, alokacin ne ya gaskaka maganganunsa na cewar bashida ƴanci tinda har ya rasa dangin mahaifinsa, akwai tambayoyin da yakeson yiwa mommy..."
yana wannan tunanin Mommy ta bashi maganin data ɓare, karɓa yayi ya watsa su a bakinsa sannan ya karɓi bottle ya korasu da ruwa, sauƙe ruwan yayi yana mai jan dogon numfashi..."

Mommy tace "sannu koh my son, Allah ya yaye maka..."
Jinjina kai yayi yana kallon ƙasa,
Mommy ta kuma cewa "Junaid shin akwai abunda kake ji a ranka akan Ayushert?..."
ÆŠagowa yayi yana kallonta cike da mamaki yace "bangane ba"
Momy tace "ina nufin kana jin sonta a zuciyarka? dan Allah kar ka ɓoye mun ka faɗamun gaskiya..."
Junaid ɗan bubbuga goshinsa yayi ido a lumshe yace "kinsan fah a wancan lokacin ma saboda ke ne yasa na amince da baikon nan kuma tazo ta watsa miki ƙasa a ido" yaja dogon numfashi sannan ya kuma cewa "Mom kinsan duk abunda kike so ina ƙoƙarin ganin nayi miki shi, inason ganin abunda zai faranta miki rai..."

Mommy tana murmushi tace "Alhamdulillah naji daÉ—in wannan batu naka, toh amma shin kana jin sonta a zuciyarka? idan nace ka Aureta zaka Aure ta?..."

Junaid juyowa yayi yana kallon mommy fuska ba Annuri yana yamutsa fuska yace "wai kam Mom shin ita kaÉ—ai ce mace aduk faÉ—in duniyan nan? kin nace a wannan yarinyar shin dole ne saina Aureta..."
Mommy ta ɗaga kafaɗarta alamar bata damu ba ta kuma cewa "Hmmm Junaid kenam nasan dai kana son Ayush, toh meyasa kake ɓoye mun?..."

Junaid yace "toh idan inasonta ita ɗin shin tana sona ne?..." ya ƙarasa maganar ba tareda ya juyo ya kalleta ba...
Chapter 20 · 0% Book details