← Book details Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 85

Sashe 40

Matar Damisa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗaukar ta yayi sannan ya zaunar da ita a cikin farin bahon wanka ya kunna mata fanfo mai ruwan ɗumi saida ruwan yazo mata saitin ƙirjinta tukun ya kashe ruwan tareda ɗaukar sabulu mai ƙamshin gaske yana murza mata a jikinta cikin salo, haka yake bi yana mulmulka mata sabulun a duk ilahirin jikinta, lumshe ido tayi sannan ta ƙwantar da kanta a bakin bahon tana kallon sama,
shima cire singet jikinsa yayi da gajeren wandonsa ya shiga cikin bahon dake baho ne mai girman gaske domin zai iya ɗaukan mutane uku zuwa huɗu, ƙara kunna musu ruwan fanfo yayi mai zafi har saida ruwan yazo saitin wuyansu tukun ya kashe, hannu yasa yana wanke mata jikinta ta ko ina daga sama har ƙasa daiden lokacin da ya rufu kanta a cikin ruwan ya manna mata kiss akan goshinta, still idonta a lumshe ko buɗe su batayi ba, sai daga baya ta buɗe idonta a hankali tana kallon cikin ƙwayar idonsa, hancin su yana manne dana juna haka numfashinsu yake hargutsuwa dana juna, a haka yake wanke mata jikinta a hankali yana shafar jikinta kamar wanda yake shafar jikin kifi tsabar tsantsi da laushi hannunsa yakai saitin pant ɗin ta ba tareda yasa hannunsa ta cikin pant ɗin ba haka ya soma shafar saman pant ɗin cikin salo,
daiden lokacin ta sauƙe ajiyar zuciya tareda lumshe ido kamar mai yin bacci, haɗe musu lips yayi yana socking a hankali har ya zura harshensa cikin bakin ya kamo harshenta yana tsotsa kamar wanda ya samu lollipop, haka yake tafiya da hannunsa yana shafar tumbin cikinta har zuwa saman breast ɗinta, nan ma shafawa yake yana murzawa a hankali,
gaba É—aya ta gama fita hayyacinta haka itama take mayar da martani suna kissing junansu, ta zagayo da hannayenta biyu ta bayansa tana shafa shi itama a hankali,
gurin yayi shuru sai motsin ruwa ake ji yana bada sauti a hankali,
ƙara sauƙar da hannunsa yayi kan tumbin cikinta yana shafawa a hankali ji yayi kamar ba tumbin Ayush yake shafawa ba domin yasan kalar tumbinta ɗan ƙarami ne a shafe kamar babu komai a cikin cikinta, yanzu kuma yaji tumbinta ya sauya sosai cikin ya ɗan yi girma sannan yayi tauri, raba lips ɗinsu yayi sannan ya ɗago yana kallonta cikin wani irin yanayi a hankali ya ambaci sunanta "Yushert.."
Itama buÉ—e eyes É—inta tayi a hankali take binsa da kallo cikin sexy voice yace "you have a pregnant?..."
zaro Ido tayi sosai tana binsa da kallo, murya a sanyaye ya kuma cewa "Please ki gaya mun gaskiya my wife, cikin ki ya É—ago sosai..."
girgiza masa kai tayi babu bakin magana, zuciyarta ne yake wani irin bugawa, ta tsorita sosai jin abunda ya faÉ—a,
Junaid hannunsa yakai ƙasin marar ta yana shafawa a hankali yake motsi da lips ɗinsa yace "marar ki ya ɗago Yushert, kina ajiye da Baby na.."
ya ƙarasa maganar yana goga musu hancinsu guri ɗaya, ji yayi tace "tayaya hakan zata faru?..."
É—agowa yayi yana kallonta da murmushi a fuskarsa yace "our first night, kafin na tafi California shin kin tuna? kinsan lokacin ma an É—aura mana Aure..."
Ayush rufe idonta tayi sosai tana tariyo abunda ya faru a tsakaninsu, a cikin zuciyarta take maganar cewa "kenam daga yi sau É—aya sai ciki? Impossible I can't believe..."
a daiden lokacin Junaid ya manna mata kiss a saman lips É—inta...

tashi yayi Junaid daga kanta yana faÉ—in "rufe idonki kar ki sake suma mun irin na wancan lokacin farkon zuwanki gidan mu..."
Ayush ganin yana shirin miƙewa a tsirararsa yasa ta rufe idonta ta sauri, har saida ya fita daga cikin bahon ya ɗauki 3quater sa ya zura, jikinsa duk damshin ruwa yasa hannu yayi wa Ayush ɗaukar luɗa ya fita da ita cikin room ɗin da yake a asibiti, ƙwantar da ita yayi sannan yasa hannu ya cire mata jiƙaƙƙen pant ɗinta ya jawo mata mayafi ya rufe mata jikinta gaba ɗaya, har yayi wannan ɗawainiya idonta a rufe yake,
komawa cikin toilet yayi yaje ya wanke mata kayan sakawarta daya ɓaci da amai har pant ɗinta da breziya duk saida ya wanke su tas sannan ya shanyasu,
ɗaukar singlet ɗinsa yayi ya sanya shi a jikinsa sannan ya koma cikin ɗakin, saida yasa key a ɗakin tukun yazo shima ya ƙwanta tareda rungumo Ayush jikinsa ya rufa musu mayafi kafin a ƙirga mintuna har bacci yayi awun gaba dasu....

Asussuban farko Ayush ta tashi daga bacci tana mutsil-mutsil jin yanda Junaid ya ƙanƙameta ne yasa ta ɗanyi shuru saboda kar ta tashe shi, a hankali take zamar da hannunsa daga rungumar da yayi mata, da haka har tayi nasarar tashi ba tareda ya farka ba, duban kanta tayi taga ashe tsirara take ƙwance, da hanzarinta ta nufi toilet taje ta saka kayanta sannan ta fito tazo gaban Junaid ta durƙusa tana hawaye a hankali take faɗin "kayi haƙuri Yayana nima na sani ina ɗauke da cikinka na tsawon wata huɗu, amma sai dai a wannan lokacin bazaka kasance tareda mu ba, dani da jaririna zamuyi nesa dakai saboda bamuyi maka halacci ba, munci amanarka, jaririna a jikina yake dole zai kasance dani a koda yaushe, Yaya Junaid daga yau bazaka ƙara ganin mu ba, ina fatan Allah ya baka wata matar da ta fini komai, kuma Allah ya baka ƴaƴa masu albarka waɗanda suka fi jaririna, ina sonka mijina...."
tana kaiwa ƙarshe ta miƙe tareda kai masa sumbata akan goshinsa daga nan ta nufi bakin ƙofa a hankali ta murza key ta buɗe tayi ficewarta,
tana fita daga cikin asibitin ta fara gudu ko tsaya É—aukar akwatinta batayi ba, haka ta wuce security tayi ficewarta,
Garin shuru ba kowa sai hasken nepa ta ko ina, wani wajen kuma duhu ne ba haske da haka take tafiya ƙafarta ko takalmi babu,
wani mai mashin ne ya tsaya a gefenta yana faɗin "Hajia lafiya kuwa na ganki a cikin daren nan ko asuba ba'a ƙira ba.."
juyowa tayi tace "lafiya ƙalau wani warai mai ɗan nisa nake son zuwa.."
yace "toh idan babu matsala hau na kai ki yanda zaki sauƙa, Allah yasa dai ba aljana zan ɗauka ba..."
Ayush kuka take jin abunda ya faÉ—a ne yasa ta yin dariya ta hau mashin suka tafi,
tafiya suke ba ƙaƙƙautawa har sun fara fita daga cikin gari babu wasu gidaje sai jeji,
Mai mashin ne ya tsayar da mashin yana faɗin "dan Allah baiwar Allah wallahi da niyar temako na ɗauko ki naga kina cikin matsala, nima asibiti zanje dubowa mahaifiyata dan Allah karki cutar dani, yanzu na gane cewa ke ba mutum bace amma ki rufa mun asiri ki barni na koma cikin garin mu lafiya, wallahi daga nan bazan ƙara yin gaba ba, wallahi ni ko fuskarki bana iya gani tsabar duhu sai iya hasken mashin ɗinane kawai..."

Girgiza kai Ayush tayi tace "shikenam ba damuwa hakan ma nagode sosai, ka juya kawai ni zan ƙarisa gurin da zanje..."
tana kaiwa nan tayi gaba abunta ko tsoro da fargaba babu niyarta shine ta koma jejin da suka zauna da mahaifiyarta...
Shi kuwa mai mashin da gudu ya juya ya koma baya..

Bayan sallar asuba gari yaɗan fara wayewa Junaid yana ƙwance bai tashi ba har yanzu domin wani irin nannauyar bacci ne ya ɗauke shi,
yana cikin bacci yaji an turo ƙofa da ƙarfi Malam Lawan ne ya shugo da hanzarinsa yana ƙiran sunan Junaid,
"Junaid! Junaid!! Kai Junaid ka tashi mana"
Mutsil-mutsil Junaid yake yana shirin buÉ—e idonsa, malam Lawan ne yasa hannu ya finciko shi zaune yana faÉ—in "ko sallah bakayi ba, shin kasan maiyake faruwa ne yanzun?.."
Junaid waige-waige ya somayi yana faÉ—in "ina Yushert take?.."
malam yace "Ayshert kuma tazo ne?.."
cikin rashin fahimta malam yake kallon Junaid,
Junaid ganin kar malam yayi tunanin wani abu yasa ya kawai da maganar Ayush yace "lafiya kuwa malam?.."
Malam yace "mafarki kayi koh?.."
sunkuyar da kai ƙasi Junaid yayi yace "Hmmm!.."
Malam yace "yanzun tashi kayi sallah tukun kaji wani zance.."
sauƙa daga kan gadon Junaid yayi yana tunanin abubuwa da dama a ransa ya nufi toilet ya ɗauro Alwala, yana maganar zuci "shin ina Yushert taje? yaushe ta tafi? daman ba zuwa tayi ta zauna dani ba?..." haka yake wannan tunanin har ya komo ɗakin ya ɗauki jallabiyarsa yasa sannan ya daidaita nutsuwarsa ya fara sallah, bayan ya idar ya fuskanci malam Lawan yaga kamar yana cikin matsala yace "wai malam meyake faruwa ne kam?..."
Malam ne ya miƙe tsaye yaje ya ɗauki remote ya kunna plasman dake manne a jikin bangon ɗakin yace "Junaid kalli abunda yake faruwa..".
Tashar labarai ne ta ko ina ana maganar Ayush cewar ita tasa wuta a gidan Doctor Fateema, ita tayi sanadiyar mutuwar Doctor Fateema, ga photunan Ayush yanda yaketa yawo ana nunota ga kuma photon marigayiya Doctor Fateema, ga photon gidan yanda yayi ƙurmus, an bayyanar cewar Ayush tana nan a gidan Doctor Hasheem a ɓoye..
Sai kuma aka nuno video gidan Doctor Hasheem yanda mutane suka taru a ƙofar gidansa kowa yana riƙe da makamai ga ƴan jaridu ga sojoji da ƴan sanda dasu human rights duk a ƙofar gidan, a cikin television ganan maigadin gidan yanda aka cire masa kayan jikinsa a barshi daga shi sai gajeren wando ana tilasta masa akan ya faɗi yanda Doctor Hasheem ya ɓoye Ayush....
Kawar da wannan video akayi suka kunna recording maganar Ayush yanda ta amsa da cewa ita ta ƙona Doctor Fateema a lokacinda take magana da Doctor Hasheem duk a cikin television yanzu ta tabbata cewar ita ta kashe Doctor Fateema ta hanyar dasa gobara a gidanta....

Junaid yana zaune baisan lokacin da ya miƙe tsaye ba kamar zai haɗiyi ransa, a fusace yace "waye ya sanar da ƴan jarida wannan maganar? Waye yayi wannan aika-aika? bazan zauna ba dole zan nemo Yushert bazan bari a raunanata ba, tana da juna biyu a jikinta..."
a tsawace yake wannan maganar ya fice daga cikin É—akin a ruÉ—e,
Shima Malam tashi yayi yabi bayansa da sauri, suna zuwa Malam ya buÉ—ewa Junaid motar shima ya shiga suka tafi, kai tsaye gidan Doctor Hasheem suka nufa yanda Æ´an jaridu da sojoji suke...
Chapter 40 · 0% Book details